Ticker

6/recent/ticker-posts

Sanya Yatsa A Farji

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, ance mace in tana sa yatsa agabanta yana da illa to ya matsayin yake in mijinta ne yake sa mata. Kuma ance idan mace ta biyawa kanta bukata yana jawo mata fitan tsutsotsi, in ya kasance mijinta ne yake biyamata ta hanyar wasa da ita har ta fitar da maniyyi ba tare daya sadu da ita ba, shin zata iya kamuwa da matsalar itama?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalamu warahmatullah.

Biyawa kai bukata (istimna'i) haramun ne bisa nassin Alƙur'ani mai girma. Allah Maɗaukakin Sarki yana fadar siffofin bayinsa muminai mutanen kirki, sai ya ce:

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ

Bayin Allah nagari Sune waɗanda dangane da farjinsu suke kiyayeshi. (Suratul Mũminun 5)

إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ

Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka (kuyanginsu) to lalle sũ bã waɗanda ake zargi ba ne. (Suratul Mũminun 6)

فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ

Sabõda haka Duk wanda yanemi wata hanya ta biyan bukatar sha'awarsa saɓanin matarsa ko baiwarsa, toh shi yana cikin masu ketare iyakokin Ubangiji. (Suratul Mũminun 7)

Sannan kuma biyawa kai bukata (Istimna'i) yana iya janyo miki matsaloli ta fuskar lafiyarki. Kamar daskarewar maniyyi, ciwon mara mai tsanani, rikicewar tunani, ciwon makanta, rikicewar jinin haila, fitar tsutsotsi daga gabanki da sauransu.

Amma mijinki zai iya yi miki Ma'ana ya sanya hannunsa yayi miki wannan wasa da farjin naki kodai atsakiyar lokacin da kuke cikin jima'i ko kafin ku fara da kuma bayan kun gama, Kema kuma ya halatta kiyi masa wasa da al'aurarsa. Malamai sunyi cikakken bayani akan ilmin jima'i da yadda ake yinsa. Don karin bayani aduba IT HAFUS SADATIL MUTTAƘEEN na lmam alzabidy IHYA U ULUMID DEEN na lmamul gazaly acikin kitabu adabin Nikahi.

Saboda haka idan mijinta ne yake mata hakan, yana motsa mata babbar sha'awarta, ta yadda dukkan wata ni'ima da take tare da ita zatayi waje, kuma ba mamaki daga bayan wannan wasannin zai nemeta (saduwa).

Amma idan ita ce da kanta take gamsar da kanta haka, ba yadda zaiyiwu wannan maniyyin da sauran duk wata ni'imarta ta fita waje, dole ne sai wata ta tsaye mata a gabanta, ta yadda wannan sauran da ya tsaye mata, shi ne zai zame mata damuwa, mararta tana ciwo, kanta yana ciwo, tsutsotsomi suna fita daga gabanta da dai sauransu.

Sannnan yana daga cikin irin hikimar mazan da basa iya gamsar da matayensu, kafin kwanciyar Aure, suna amfani da wannan mathod ɗin ta yadda mace zata sami gamsuwa, sannan kuma sai ya nemeta ɗin in Shã Allahu.

Amma namiji baya wuce mijti 5 akan mace, shima zai iya haddasa mata irin wannan damuwar.

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments