Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Rabon Gado: Ta Malam Ibrahim Halilu Marinar Tsamiya

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙar Rabon Gado: Ta Malam Ibrahim Halilu Marinar Tsamiya

1. Mu gode Jalla wanda yaw wadata,

 Ga al’amurrar duka bai buƙata.

2. Mu sallama ma Musɗafa Manzommu,

 Da Alu har Sahbu su agaje mu.

3. Zani ƙasida ta rabon Mirasi,

 Ga ɗakuna shidda bisa ga nassi.

4. Ka san gidajen da ka ɗaukat gado,

 Kowane ɗaki suke ka ji ƙasida.

5. Lazimci Larbi na cikin Risala,

 Tsaya ka gane shi ka bar kasala.

 6. Haba da baz bi shi ka san ashabu,

 Ka san waɗanda za ka ba nisabu.

7. Lura ka gane ma’abuta nisfi,

 Guda biyat na ka riƙa da ƙarfi.

8. Ka sa miji ka sa ɗiya da sulɓi,

 Ka sa ɗiyat ɗa ita ag ga larbi.

9. Da ‘yar’uwa Shaƙiƙiya kawo ta,

 Ko ita nisfi taka son a ba ta.

10. Da ‘yar’uwa jahat uba ka falka,

 Ka ji biyat sun cika babu shakka.

11. Sa ma’abuta rubu’i su biyu na,

 Miji da mata da yawa na sunna.

12. Sa ma’abuta sumuni zaujatu,

 Su at guda ɗai ga ƙidan siƙatu

13. Su ma’abota sulusani su ko,

 Su duka na lura da su ka sakko

14. Ɗiyan tsatso sai bi da bintani,

 Ɗa biyu jahat da ka biɗo ukhtani

 15. Shaƙiƙatani babu duk khilafa,

 Sulusani at na su riƙe ka ƙarfafa

 16. Da ‘yan uwa biyu ga jahat uba suke

 Ukhtani ke nan ka tsare ka warke

 17. Su huɗu ke nan ga ƙida ka gane

 Yi ijtihadi ka iya su kowane

 18. Sa ma’abota sulusi su biyu na,

 Uwa da isnaini li’ummi ka tuna

 19. Sun cika daidai sulusi at,

 Lura da su ba ka da mai kaushe su

 20. Sa ma’abuta sudusi guda bakwai,

 Kar fa ka sake su riƙe su daidai

 21. Zana kasa uwa rabonsa,

 Duk sudusi anka fitas ka ba su

 22. Ka ba ɗiyat ɗa uwat uba duka,

 Uwat uwa sa ta ga ka duka cika.

 23. Da ‘yar uwa jahat uba da ɗan’uwa

 Shi ko li’ummi bari raunanawa

 24. Sun cika daidai bisa wanga larbi,

 Kway yi shi ya tsira ga masu albi

 25. Allah shi haushe mu bisa sawaba,

 Da godaben Annabi mai muhibba

 26. Na cika waƙa ta batun mirasi,

 Allah ka tara mu cikin firdausi

 27. Mai tambayal Naziru Ibrahimu,

 Yay yi ta sattaru rufe laifinmu

 28. Mu yo salati inda ɗan Amina,

 Da Alu har sahabu da tabi’ai.

Post a Comment

0 Comments