Ticker

6/recent/ticker-posts

Roƙon Allah Kan Neman Sauƙin Cutar Zafi: Ta Malam Mu’allah-Yiɗi Salame.

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Roƙon Allah Kan Neman Sauƙin Cutar Zafi: Ta Malam Mu’allah-Yiɗi Salame.

1.   Ya Khaliƙal nami mai iyawa,

Bisa ga komi Jalla mai rabawa,

Ni ban shikai tutut ina yabawa,

Na gode mai baiwa shi na daɗawa,

Mai baya kowa ba shi ko hanawa.

2.   Na sallama ga Ɗaha shugabanmu,

Yasina ka ji wasiɗimmu,

Komit taɓa mu shi ka agajinmu,

Na yi salati ga maƙamnacinmu,

Muhammadu ka ji madogaranmu.

3.   Yi ijtihadi ka riƙe ahzabu,

Na auliya’ullahi su akaɗabu,

Zan ka kiran sayyidina awwabu,

Kaza da allai nai da ko sahabu,

Da mai biyar su duk bisa sawabu.

4.   Ya wanda yaɗ ɗaukaka yas san komi,

Yaz zama shi ka sarrafawat komi,

Ga ni gareka ya makomat komi,

Ya Rabbu kai kay yi ni kay yi komi,

Kai ad da iko da sani da komi.

5.   Kai ad da mu mun haƙƙaƙe ba shakka,

Muna kira ka bamu jin ƙayin ka,

Ya mau’ill-uffati na kirai ka,

Bawanka ɗan bawanka ɗan boyak ka,

Ga shi da gaskiya shi na kiran ka.

6.   Sa’adatud daraini nib biɗe ka,

Na daɗa shukuri kuma na yabe ka,

Nawa raj’i Jalla na gare ka,

Ba ni da ƙamna duk sai gare ka,

Komit taɓa ni Rabbu zan gare ka .

7.   Daɗai waninka Rabbu ban kira shi,

Da baɗini da zahiri ka san shi,

Don mazu-mazu abɗahal ƙuraishi,

Ya Hayyu ya Ƙayyum ya Zal’arshi,

Agaji bawanka har shi yo talauci.

8.   Ya arhamur Rahama’u mai sakowa,

Kyauta tutut gare mu na zubowa,

Bata da fashi tana tafowa,

Ya Rabbu don sunan da yaz zam kowa,

 Ya san shi don ya wuce a yi mai wawa.

9.   Ya zal-ula ban da malazi sai kai,

Ba ni da magani ga kai na ko ɗai,

Ya Rahimi ka san dawa’ina kai,

Duban ni ya Allahu dubin jinƙai,

Don wanda kaz zaɓa cikin talikkai.

10.  Don Arfa da wanda ke tsayawa,

Ranar wurin Hajji da girmamawa,

Da wanda ajami ka yi da larabawa,

Domin mala’ikku da annabawa,

Kaza waliyyai haka ƙadirawa.

11.  Don sulaha’u Rabbana don ahayar,

Don nujaba don nuƙaba don aƙarar,

Ya Rabbi don waɗanda kab ba asarar,

Shaihunmu Shehu Usmanu da sayyidi Mukhtar,

Da Shehu Abdulƙadiri Abrar.

12.  Sa mini albarka ga arzikina,

Isan ni kafi bisa hasidina,

Kai ad da yi kumyata makirina,

Ka bani lafiya cikin jikina,

Da al’amurrana da ko ganina.

13.  Ya Rabbu don bayin ka salihina,

Don anbiya’u su da abidina,

Sa ni cikin bayinka muminina,

Ubangiji inganta zahiri na,

Da baɗinina shi zamo yaƙina.

14.  Ral lahira ya Rabbi tsarshe ni wuta,

Da ni da muminnan da kayi ma bauta,

Da duniya da lahira ka kyauta,

Ka tabbata min sutura da kyauta,

Da kay yi ya ilahuna daɗa ta.

15.  Tsaran ni tsarshe ni ga yin nadama,

Dan nana har cana tsayin ƙiyama,

Don girman ƙur’anu in yi zama,

In zamni duniya cikin salama,

Ka bani cana lahira karama.

16.  Don mujtaba don Murtala Mumajjidu,

Wanda ka ceton mu ga gobe Sayyidu,

Ya Rabbi don Khairul-wara Mu’ayyidu,

Don Musɗafa maƙannacinmu Ahmadu,

Babban fiyayye Musɗafa Muhammadu.

17.  Dawwama jinƙai bisa mai muƙami,

Haƙiƙatal-aƙawali shi imami,

Awwal anbiya’i, mai khitami,

Duk mu yi salati ka hakaza salami,

A dawwama ma sayyidul anami.

Tammat bi hamdillahi.

Kowane rukuni na mabarata yana amfani da rubutattun waƙoƙi gwargwadon hali, sai dai makafi sun fi amfani da su. Kusan kowane makaho ya riƙe wani ɗan yanki na wata rubutattar waƙa ta wa’azi ko madahu ko wani fanni na addini. Wasu suna hardace dukan waƙa wasu kuma wani sashe cikinta suke hardacewa.

 


Post a Comment

0 Comments