Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Ilmi: Ta Malam, Adamu Jingau Furfuri

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙar Ilmi: Ta Malam, Adamu Jingau Furfuri

 1. Na roƙi Jallah abin nema na,

Don wanda kai cikakken suna,

Ka kai ni Makka abin fatana,

 In zama Alhaji can wata rana.

 2. Mun gode Jallah Ta’ala Sarki,

Sa mu ga Annabi ko a mafarki,

Duk wanda bai iya wankan tsarki,

 Ƙarshensa ai masa suna jaki.

 3. Ina gaya maku ‘yan makaranta,

Da ku samari da ku ‘yan mata,

In an gaya mana a ba ca ta,

 Sai mu riƙe su mu zam ‘yan gata.

 4. Rashin sani ga mutum ƙauyanci,

Nemi sanin ilmi binnanci,

Kai ƙoƙari ka yi komai ɗaci

 Ko a Kano kake ko kuma Bauchi.

 5. Almajiri nake ba ni da komi,

Mai shan fura nake ko tai tsami,

Gun Jallah zan biɗi sauƙin komi,

 Ba gum mutum ba da ba shi da komi.

 6. Yau da ɗan Taroro da Kure da Manu,

Sun zo cikin Fagge sun naɗe hannu,

Wai su nufinsu su naushi idanu,

 Sun mai da kansu kamar wasu shanu.

 7. Batun da zan yi a kan manufata,

Da doke hanci da giwa na mata,

Ku daina dambe ku zo makaranta,

 In kun ƙi gobe akwai mahukunta.

 8. Zan gargaɗi ku ji matan aure,

Don Allah kar ku fito ku yi kare,

Ku bar mazanku da kallon ƙyaure,

 Ku zo anai muku gyaran aure.

 9. Matar da ba ta fita ta yi gulma,

‘Ya’yanta ba su fita su yi su ma,

Matar da ke ta fita don gulma,

 Wannan miji nata ya sha fama.

 10. Bar haɗa kanku da matan banza,

Waɗanda ba izini sai murza,

Kullum sunai muku ƙaryar banza,

 Wai an saya musu kwalba da kaza.

 11. Zan zagi karuwa matar wawa,

Ba mai riga ta ga kokon maiwa,

Kullum da safe ta zo nasarawa,

 Tana karairaya wai ita giwa.

 12. Ke babu alkawari sai ƙarya,

 Mai zub da goro ta tsinto ƙwarya,

 Jikinta babu na koko da gaya,

 Kullum da safe ta je ta mashaya.

 13. Mai son ki zai wuni noma rana,

 Dominki zai rasa kurɗin zanna,

 In mai rini kake ka hau marina,

Can za ta bi ka kamar wata ɓauna.

Post a Comment

0 Comments