Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Danguzuri

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Shehu Ajilo Ɗanguzuri

An haifi Alhaji Shehu Ajilo a garin Ɗanguzuri ta ƙaramar hukumar Maƙarfi a jihar Kaduna, babu takamammar shekarar da kwanan watan da aka haifi Shehu ajilo, saboda a cewarsa ba a rubuta ba, kuma duk waɗanda ya kamata ya tambaya sun riga mu gidan gaskiya. A wata hira da na yi da shi a ranar Laraba goma ga watan goma sha ɗaya shekarar dubu biyu da ashirin da ɗaya (10/11/2021) ya ƙiyasta mani shekarunsa cewa saba’in zuwa tamanin ne a halin yanzu. Ajilo ya yi sana’o’i da dama daga ciki har da koyarwa da tuƙin mota da yankan farce da ɗaukar hoto wadda ita ce sanadiyar sunan Ajilo da sauransu.

Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

Alhaji Shehu Ajilo ɗanbaiwa ne, domin duk waɗannan sana’o’in da ya yi babu wadda aka koya masa sai dai kawai ya yi, ko ma waƙa da ya fara bai yi zama yaron kowa ba sai kawai ya fara abarsa.

Asalin iyayensa daga Kano suke a wani ƙauye da ake kira Rikadawa ta ƙaramar hukumar Madubi, kakansu ya zo ne tare da mahaifinsa domin yawon nema irin na Kanawa, sai ya auri Bazazzagiya a nan, kuma aka haife shi a nan tare da sauran danginsa.

An ba shi auren ‘yar Shata wadda ake kira Hajjaju a sakamakon wani kiɗa da ya yi  a lokacin bukin yayarta Sadiya wadda ta yi aure a Kano. Mata ne suka gayyace shi ya yi wasa a can a lokacin Shata ba ya gida ya je Maiduguri yana yi wa Abdulmuminu Aminu waƙa. To da ya fara waƙar nan daga cikin matan Shatan sai wata ta ce ta bashi fuloti[1], wata ta ce ta ba shi bulo, wata ta ce ta ba shi siminti, ɗaya kuma ta ce ai sai a ba shi mace. Sai kuwa Hajjaju ta ce tana sonsa, sai kuwa aka buga masa waya cewa ai an ba Shehu Ajilo Hajjaju, sai kawai ya ce wannan masoyina? To tana sonsa?  Aka ce eh, shi yana son ta aka ce eh, shi kenan sai aka yi auren. Allah ya yi mata rasuwa da kimanin shekara goma sha biyu da auren, ta riga mahaifin nata rasuwa da sati biyu, domin ta rasu bayan sati aka zo addu’ar bakwai, sai sati mai zuwa Shata ya rasu. Allah ya gafarta masu bakiɗaya.

Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

Alhaji Shehu ajilo ya fara yin suna ne a kiɗan gangar noma, wadda ya ƙware sosai a kansa har ake kiransa aljanin kiɗa ƙanen Ɗanbinta.

Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

Musamman a lokacin siyasar NEPU da PRP a lokacin su Sardauna ya yi kiɗa ‘yammata na rawa suna amshi. A halin yanzu dai yana da mata biyu bayan waɗanda suka rasu da waɗanda suka rabu da shi.



[1]  Wato filin da ake gina gida a kansa.

Post a Comment

0 Comments