Noma Tushen Arziki

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Noma Tushen Arziki

    G/Waƙa: Noma tushen arziki

    : A yi noma yaƙin cigaba

    Jagora: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.

     

    ‘Y/Amshi : Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Yara da mun waÆ™a in mun gama

    : Mu tai arewa mu ja jiki

    : Mu kama noma tushen arziki

    : Gar kuga waƙa ta aure mu tsaf

    : Yara duk waƙar da nake muku

    : Ban kamar Shata ba uban Hajo

    : Ya riƙe noma tushen arziki

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

    Jagora: Gaisheku

     ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.

     

      Jagora: Kai kunga malam Garba Abubakar

    : ÆŠan Ammani Garba na Huntuwa

    : Ya riƙe noma tushen arziki

    Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: A lokacin da aka isko ni a a zariya,

    : Baba dan Adaraka Uban Ali Tunda,

    : Ka rike noman zamani to ni,

    : Mai kiɗanka da ɓotata riƙe.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Kai na fada maku noma zamuyi,

    : Wanda bai noma duniya don ko,

    : Riƙon aure zai mai wuya.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Masu kiÉ—a na Shehu ina kira,

    : Ku gyara hannu daidai da ku,

    : Ku shirya hannu daidai da ku,

    : Don kiÉ—an noma ne za a yi,

    : A kama noma tushen arziki.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Masu kiÉ—ana ku sake kiÉ—a,

    : Wannan ganga ta babba ce,

    : Wadda ya yi ma Audu Gwamnan Kano,

    : Ya zama turabi[1] ya tafi,

    : Ya Rabbana gafartan ya Haliƙu.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Kai ku tuna da farko da Najeriya,

    : Da tana noman gida mun taba,

    : Noman auduga mun yi noman koko,

    : Duniya kwana ake tashi ake kullum,

    : Sai ga man fetur ya fito,

    : To mun rikiÉ—e mun yad da su,

    : Sai ga man fetur ya tafi.

     

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Tunda man fetur bana yai Æ™asa,

    : Mu É—auki noma kowa yai waje.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Yara dare ya fara ya raba,

    : Ina kiÉ—anku na noman zamani.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Kai kaji waÆ™a ta tai sama,

    : KiÉ—an na noma tushen arziki.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Kai ku tuna da Shata Baba Uban Hajo,

    : Gonatai tai eka dubu,

    : In ya yi waƙar gona zai tafi.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin[2] cigaba.x2

     

      Jagora: Yara waÆ™ar noman zamani,

    : In mun yi noma yau duniya,

    : Mun samu kuÉ—inmu mu adana,

    : Ku zo gida mu kasa ukku,

    : Kashe É—aya mu fachanchana,

    : Kashi É—aya banki zamu kai,

    : Kashi gudan mu yi noman zamani.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Yara kun ga kuÉ—i in sun zo,

    : Mu riƙe kar mu sanya ido,

    : Mu riƙe duka wata rana ba wata,

    : Rana ba ce yau bare kuma,

    : Wasan damuna in aka labta[3],

    : Ruwa mi zamu ci.

    ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

    : A yi noma yaƙin cigaba.x2

     

      Jagora: Yara ku Æ™ara kiÉ—a daidai dani,

    : Saboda waƙar noman zamani,



    [1]  Mutuwa yake nufi.

    [2]  Wata tanyar da ake bi don samun cigaba.

    [3]  Yin ruwan sama mai nauyi/yawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.