Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutane Ku Kama Sana’o’i

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mutane Ku Kama Sana’o’i

 

  G/Waƙa: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma.

 

  Jagora: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma.

 ‘Y/ Amshi: A maida hankali wajjen noma,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma.

 

  Jagora: Yanke talauci[1] kun san sai noma x2.

  ‘Y/ Amshi: Mutum ya kama noma ag girma,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma x2.

 

 Jagora: Wanda bai noman bai kyauta ba x2.

 ‘Y/ Amshi: Duk wanda ba ya noma an tsarmai,

 : Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma x2.

 

Jagora: Komai kuɗin shi bai yi dubara ba x2.

‘Y/ Amshi: Yau wanda ba ya noma an tsarmai,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma x2.

Jagora: Sha hura ka ɗau galma[2] Malam,

: Ka kama huɗa hili has sashe.

‘Y/ Amshi: Ka shuka auduga tai ma haske,

: Da ta nina ka anso nairori,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma.

 

Jagora: Najeriya ƙasa mai albarka,

: Kuma ga yawan jama’a malam x2.

‘Y/ Amshi: Ƙassad da Rabbana yay yilwanta,

: Mun tcarma ko’ina wajjen girma,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma x2.

 

Jagora: Da Najeriya mun dogara ne,

: Gyaɗa da auduga wajjen noma x2.

 ‘Y/ Amshi: Muna ciniki da ƙasashen waje,

: Arzikinmu bai lalace ba,

: Kuɗinmu ko’ina sun kai ƙarhi,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma x2.

 

  Jagora: Daga nan sai hada-hadam mai taɓ ɓullo,

: Sai munka daina noma sai kwangila x2.

  ‘Y/ Amshi: Mu ka ban noman gyaɗa da auduga,

: Kuɗinmu sunka zan ganyen banza,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma x2.

 

  Jagora: Sadda muna noman gyaɗa da auduga,

: Sannan Kano birnin Dabo

: Idan ka hangi dala kamat tsauni x2.

‘Y/ Amshi: Ga na’urag gurje auduga,

: Akwai su ko Gusau in ka je can,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma

: Mutane a kama sana’o’i x2.

 

 Jagora: Yanke talauci ka san sai noma.

 ‘Y/ Amshi: Mutum ya kama noma ag girma

: Mutane a kama sana’o’i.

 

 Jagora: Sadda[3] muna noman gyaɗa da auduga,

: Sannan Kano birnin Dabo

: Idan ka hangi dala kamar tsauni.

‘Y/ Amshi: Ga na’ura gurje auduga,

: Akwai su ko Gusau in ka je can,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma

: Mutane a kama sana’o’i.

 

  Jagora: Samun fetur gare mu babbas sa’a ce,

: Amma kan mu dogara wajjen shi,

: Saboda kasuwa tai ta hwaɗi x2.

‘Y/ Amshi: Kowa ya buɗa hili yai gona,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma,

: Mutane a kama sana’o’i x2.

 

  Jagora: Yanzu kasuwam mai ta hwaɗi,

: Gwamnati ba za ta samu kuɗin,

: Ɗaukaj jama’a ba kamad dauri,

: Da kyautata jin daɗin jama’a,

: Mi ad dubara ku jama’a?

  ‘Y/ Amshi: Mu shuka auduga da gyaɗa masara,

: Mu yi[4] shinkahwa mu sa dawa,

: Sannan mu shuka gero haw wake,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma.

 

Jagora: A noma dankali da rogo had doya,

: A maida hankali wajjen koko[5],

: Mu iya ci da kanmu Najeriya,

: Ham mu kai saura a ƙasashen waje x2.

 ‘Y/ Amshi: Kuma a gyara hanyoyin daji,

: Don motocin da ka ɗaukowa,

: Su kai gari-gari in sun ɗauko,

: Mutane a kama sana’o’i, 

: A maida hankali wajjen noma x2.

 

  Jagora: Abin dud da kan noma malam,

: Ka je ka saisuwa[6] kai amfani.

 ‘Y/ Amshi: Ba za a tauye kayan kowa ba,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma.

 

  Jagora: Abin dud da kan noma yai kyau,

: Ka je ka saisuwa kai amfani.

  ‘Y/ Amshi: Ba za a tauye kayan kowa ba,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma.

 

  Jagora: ‘Yan birni ku kama noma sosai x2.

 ‘Y/ Amshi: Da an wadata in kowa ya yi,

: In babu wanda yay yi zaman banza x2.

 

  Jagora: Idan kunka kama noma sosai,

: Da arzikinmu ya dawo sabo x2.

  ‘Y/ Amshi: Gwamnati ta samu kuɗin aiki,

: Ta ba mu magani da ruwan sha,

: Sannan ta ƙara sabbin hanyoyi x2.

 

  Jagora: Mu haɗa kanmu sannan mui ƙoƙari,

: Gwamnati ba za ta iyawa ba,

: Sai in mun ba ta goyon bayanmu,

: Mun taimaka gabaɗai dum mu yi x2.

‘Y/ Amshi: Arzikin ƙasammu ya bunƙasa

: Darajjak kuɗinmu ta dawo,

: Sannan mu cimma sauran Turawa x2.

 

  Jagora: Najeriya ƙasanmu ta kanmu

: Ba mu da wata ƙasa bayan ita,

: Tilas mu tashi mui aiki tuƙuru x2.

‘Y/ Amshi: Kamay yadda sauran ƙasashe

: Sun kai mu taimaka muma ya hi.

 

 Jagora: Wanda yab bar abin shi yal lalace,

: Bai taimaka ba ka san yai ƙeta x2.

 ‘Y/ Amshi: Taimako a gyara ƙasan nan,

: Ham manya-manya su ma sai sun yi x2.

 

 Jagora: Dole mu tashi mui aiki tuƙuru,

: Mu ci da kanmu mu ci da waje,

: Kuma mui ciniki da ƙasashen waje.x2

 ‘Y/ Amshi: Najeriya ƙasa mai albarka,

: Allah ya taimaki Najeriya,

: Garemu hag ga ‘ya’ya jikoki x2.

 

Jagora: ‘Yan birni ku kama noma sosai x2.

‘Y/ Amshi: Da an wadata in kowa ya yi,

 

Jagora: Talakawa ku kama noma sosai x2.

 ‘Y/ Amshi: Da an wadata in kowa ya yi,

: In babu wanda yay yi zaman banza x2.

 

  Jagora: Idan kun ka kama noma sosai,

: Da arzikinmu ya dawo sabo.

 ‘Y/ Amshi: Gwamnati ta samu kuɗin aiki,

: Ta ba mu magani da ruwan sha,

: Sannan ta ƙara sabbin hanyoyi.

 

  Jagora: Yanke talauci kun san sai noma.

  ‘Y/ Amshi: Mutum ya kama noma ag girma,

 

Jagora: Wanda bai noman bai kyauta ba x2.

  ‘Y/ Amshi: Yau wanda ba ya noma an tcarmai,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma

 

  Jagora: Da[7] Najeriya mun dogara ne

: Gyaɗa da auduga wajjen noma x2.

 ‘Y/ Amshi: Muna ciniki da ƙasashen waje,

: Arzikinmu bai lalace ba,

: Kuɗinmu ko’ina sun kai ƙarhi,

 

  Jagora: Daga nan sai hada-hadam mai tah hwaɗo,

: Sai munka daina noma sai kwangila x2.

 ‘Y/ Amshi: Mu ka ban noman gyaɗa da auduga,

: Kuɗinmu sunka zan ganyen banza,

 

  Jagora: An kakkahwa jam’iyyun haɗa kai,

: Don kowa shi sami aikin yix2,

  ‘Y/ Amshi: An ƙarhwahwa ma ‘yanmakaranta,

: Su ma su taimaka wajjen noma.x2

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma

 

  Jagora: ‘Yan birni ku kama noma sosai.

‘Y/ Amshi: Da an wadata in kowa ya yi,

 

  Jagora: Talakawa ku kama noma sosai.

‘Y/ Amshi: Da an wadata in kowa ya yi,

 

  Jagora: ‘Yan ƙauye ku kama noma sosai.

‘Y/ Amshi: Da an wadata in kowa ya yi,

: In babu wanda yay yi zaman banza,

: Mutane a kama sana’o’i,

: A maida hankali wajjen noma

 

 Jagora: Idan munka kama noma sosai.

: Da arzikinmu ya dawo sabo,

‘Y/ Amshi: Gwamnati ta samu kuɗin aiki,

: Ta bamu magani da ruwan sha,

: Sannan ta ƙara sabbin hanyoyi.



[1]  Abin da ke sa talauci ya gushe kuma bai dawowa har abada.

[2]  Yana nufin dai ka riƙi wani abin yi ta fuskar noma don kar ka yi zaman banza.

[3]  Lokacin da wani abu ya faru.

[4]  Noma.

[5]  Cocoa.

[6]  Sayar.

[7]  Tun farko-farkon kafuwar ƙasar Nijeriya har zuwa lokacin da aka karɓi ‘yancin kai har kawowa shekarun mulkin Shagari 1979 zuwa 1085.

Post a Comment

0 Comments