Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Noma Ta Alhaji Sani Aliyu Dandawo

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo

Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo

Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo

An ƙiyasta cewa an haifi alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a wajajen shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da arba’in da uku (1943) a garin Argungu ta jihar kebbi, amma dai mahaifinsa ɗan asalin jihar Sakkwato ne a garin Shuni. Alhaji Sani ya yi karatun boko amma bai yi nisa a cikinsa ba don iyakacinsa firamare, amma ya yi karatun muhammadiyya inda ya karanci alkur’ani da littatafai da dama. A shekarar 1959 ne suka tashi daga Argungu suka koma garin Yawuri da zama.

A shekarar 1964 ne ya fara waƙa kuma ya fi bada ƙarfi wajen waƙoƙin fada, amma daga baya ya riƙa yin waƙoƙi irin na siyasa da na sauran jama’a masu hannu da shuni[1] da kuma wasu fitattun mutane. Saboda kasancewarsa makaɗin fada, Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo ya yi wa sarakuna da dama waƙa, kuma bai da wata waƙa da ke zaman ba kandamiyarsa.

Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo yana da matan aure biyu da ‘ya’ya fiye da ashirin maza da mata. Allah ya karɓi rayuwarsa watan Afirilu na shekarar dubu biyu da goma sha shida (2016).



[1]  Masu arzikin dukiya.

Post a Comment

0 Comments