Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Gonar Bakura, Gonar Sardauna Ta Biyu

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙar  Gonar Bakura, Gonar Sardauna Ta Biyu

 

G/Waƙa: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

Jagora: Sardauna Amadu,

  ‘Y/ Amshi: Allah ya ƙara imanin giwa,

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

  Jagora: Sardauna yai gona,

: Ku maida himmakku ga annaya,

 ‘Y/ Amshi: Batun aikin gona.

 

 Jagora: Wanda ad duniya duk,

: Shina da albarkag gonax2

 ‘Y/ Amshi: Yana da albarkag gona.x2

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza[1].

 

Jagora: Saboda an kashe bara da jema,

: Sa jema lauɗi,

: Mai kashe kyamro.

: Ƙarangiya da badi da zara,

: Yal yaɗi Daudu sabara da irin ginshi,

: Zamarƙe da jema dagallaɓa,

: Tare da kyauro

: Shanun Sardauna gashi,

  ‘Y/ Amshi: Sun tattake shi,

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

  Jagora: Sardauna ya aje shanu ƙula-ƙula[2],

: Manya masu,

 ‘Y/ Amshi: Masu ƙoƙarin aikin gona,

: Ga gonas Sardauna,

 

  Jagora: Inda duk kam motsa suna,

  ‘Y/ Amshi: Suna batun aikin gona,

 

  Jagora: Sardauna Amadu,

  ‘Y/ Amshi:Allah ya ƙara imanin giwa[3],

 

Jagora: Kai!

: Shahwa guda-guda,

: Ba rigima nikai ba,

: Dahwa mai turu,

: Ai shin bari kora ta,

: Sassauta man kalangu,

: Don waƙag gona,

: Na Amadu Sardauna,

: Ni na Illo Kalgo,

: Mai waƙag gona,

: Na Amadu Sardauna,

: Komi nika so na Ali,

: Sai in yi Bakura,

: Inda albarkan noma,

: Hwaɗa ma mutane,

: Su kama imanin noma,

  ‘Y/ Amshi: In gero kab biɗa,

: Yi gonas Sardauna,

: In maiwa kab biɗa,

: Yi gonas Sardauna,

: In dawa kab biɗa,

: Yi gonas Sardauna.

 

  Jagora: Ai ni dai na gode,

: Amadu Sardauna,

: Zaman shi yas sa,

:Wani irin kudaku[4]

: Da ban ga kowa da irinai ba,

: Kudakun ga na Sardauna,

:Ya hwashe,

: Zaƙi ag gare shi,

:Ban ga iyaka ba.

: Ashe kudaku na,

: Gonas Sardauna,

: An bay yunwa ƙasag ga,

: Ga saye ya girma,

: Kudakun ga na Sardauna,

: In an gino saye guda,

: An yayyanke shi,

: Anka sa maka talle,

: A samo manja a barbaɗa mai,

: Ga kalwa,

: A kawo gishiri a sa,

: Ga kudaku mai taushi,

: Sannan a yi kwance-kwance,

: Ko a zubo mai,

: Dus shi bi shi shina milka,

: A samo gumi[5] mai hwari,

: Karo a dahe ma shi,

: Sai ya yi lugunɓutu luɓus,

: A laƙaƙe shi,

: A kwalho mara guda,

: A sa kwano sabo,

: A kawo maka kai,

: Zanne hankali ya kwanta,

: Ka jere damanka[6],

: Ka yanko loma,

: Ka kaɗa baki,

: Ka sa leɓo,

: Ka ruhekke ta.

: Ka tabbata kunnuwaka,

: Su ka hwaɗin,

 ‘Y/ Amshi: Ni a kai ni gonas Sardauna,

 

 Jagora: Kunnuwa ka hwaɗin,

 ‘Y/Amshi: Ni a kai ni gonas Sardauna,.

 

  Jagora: In ga,

 ‘Y/Amshi: Albarkag gona.

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

Jagora: In Gabas kat taso,

 ‘Y/ Amshi: Ka shiɗa[7] gonas Sardauna,

 

  Jagora: In Yamma kat taso,

‘Y/ Amshi: Ka jiɗa gonas Sardauna.

 

  Jagora: In Kudu kat taso,

‘Y/ Amshi: Ka jiɗa gonas Sardauna.

 

  Jagora: In Arewa kad darkako,

 ‘Y/ Amshi: ka jiɗa gonas Sardauna.

 

  Jagora: In Gabas kat taso,

: Ka shiɗa,

‘Y/ Amshi: Gonas Sardauna.

 

  Jagora: Sardauna Amadu,

: Ba abin,

 ‘Y/ Amshi: Walakanci na ba.

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

 

  Jagora: Sardauna Amadu.

 ‘Y/Amshi: Allah ya ƙara imanin giwa.

  Jagora: Ai darajjan noma,

: Ba gareku ta,

: Ɗai hwarau[8] ba,x2

: Ɗanhodiyo Shehu,

: Yay yi roƙo,

: Yay yi gewayen,

: Duniya daidai,

: Yar roƙi addini daidai,

: Addini yat tsaya,

: Da albarkag gona,

: Ɗanhodiyo yar roƙi,

: Kuma darajja,

: Ai tat tsaya,

: Da albarkag gona,

: Shehu kuma,

: Yak koma roƙon,

: Salati da sallah,

: Tat tsaya sosai,

: Kuma ya gama,

: Da albarkag gona,

: Sannan Usumanu,

: Ɗanhodiyo kuma,

: Yak koma roƙon darajja,

: Kuma yag gama,

 ‘Y/ Amshi: Da albarkag gona,

 

Jagora: To ashe gara mu kantare,

‘Y/ Amshi: Ga albarkag gona.

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

 Jagora: Shehu daddahwa,

:  Zabuwa da ta iske gero,

: Jibge[9] gonas Sardauna,

: Dud da doro taka yi,

‘Y/ Amshi: In sami albarkag gona.

 

  Jagora: Kaza ka hwaɗin in tona tsaba,

: In walƙata[10] ina ta rawata,

‘Y/ Amshi: Saboda albarkag gona.

 

  Jagora: Shanu suna ta kuka,

: Sai godiya ga,

‘Y/ Amshi: Ga albarkag gona.

 

Jagora: Talo-talo ka ta rawa,

: Shina ta rawa,

: Shina ta bugun,

: Bindigassa,

 ‘Y/ Amshi: Albarkag gona.

 

  Jagora: Awaki na barbara,

: Suna kekkewa,

: Saboda,

 ‘Y/ Amshi: Albarkag gona.

 

  Jagora: Ga jakkai na rawa,

:Suna ta tumami[11],

 ‘Y/Amshi: Saboda albarkag gona.

 

 Jagora: Raƙumin dud da tuma[12] shikai,

: Shina garali[13] nai.

 ‘Y/ Amshi: Saboda albarkag gona,

 

  Jagora: Ai doki na haninyatai,

: Rainai kwal[14].

: Bai gunekke ba,

: Ya ci,

 ‘Y/ Amshi: Albarkag gona,

 

 Jagora: Ku gangara gonab Bakura,

 ‘Y/ Amshi: Gonas Sardauna,

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

 Jagora; Ni ba ni zama,

: ina ta wa wahalab banza,

: Ina ta kiɗI,

: Wanda ba na manoma ba,

: Ni manoma nika wa kiɗi su tai,

‘Y/ Amshi: Su tai aikin gona,

 

 Jagora: Manoma nika wa kiɗi,

‘Y/ Amshi: Su tai aikin gona,

 

 Jagora: Sardauna Allah,

‘Y/ Amshi: Shi ƙara imanin giwa.

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

 

 Jagora: Babu gamba[15],

:Shanun Amadu,

: Sun tattake ta,

 ‘Y/ Amshi: Sun tattake ta,

 

Jagora: Babu jema,

: Shanun Amadu,

: Sun kalkatce[16] ta,

‘Y/ Amshi: Sun kalkatce ta.

 

  Jagora: Harƙiya ta mace,

: Ban ga burgu ko ɗai sosai ba,

: Ƙarangiya kake kyamro,

: Da kai da yalyaɗi da ginshi,

: A’ a lalle zamarƙe bai,

: Yo toho ba,

: Ina gahi yay yo?

; Gashi ya kwanta ya bi,

; Gonas Sardauna,

; Sa Amadu Bello,

: Ya wata’ala,

‘Y/ Amshi: Ya ƙara imanin giwa.

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

  Jagora: Na gode Bakura kun ce daɗi,

: Gonas Sardauna,

: Nan ni ishe wani,

: Lamgaɗam lamki,

: Lamgaɗi lamɗam[17],

: Irin huran nono,

: Wadda tay yi tafshi damamma,

: An sa ta an tacekke ma,

: A zuba cikin tukunya wankakka,

: Ta kwana ta yi sanyi bakiɗai,

: Kai ko ga ka ka biyo rana,

: Ka taho cikin inuwag gona,

: A kwalho huran nan,

: Da kwacciya wata wankakka.

: A kawo ta a ba ka,

: Sai ka sa hannun dama,

: Ka riƙe shawa zalla,

: Bakinka ka yin,

: Ƙwatan ƙwatan,

: Ƙwantal manƙwal,

: Wuyanka ka ƙara,

: Ƙurmushe da gwadin daɗi,

: Ya Allah ka ƙara,

 ‘Y/ Amshi: Albarkag gona.

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

Jagora: Akwai wani rogo,

: Shina ga,

 ‘Y/ Amshi: Gonas Sardauna.

 

Jagora: Ba sai ka sa wuta ba,

: In ka sa rana,

: Ai yana,

 ‘Y/ Amshi: Ɗwaɗɗwaɗekke[18] ma.

 

Jagora: Ku shafa man sannu-sannu,

 ‘Y/ Amshi: Don waƙag gona.

  Jagora: Ni na Illo na Kalgo,

 ‘Y/Amshi: Mai waƙag gona.

 

 Jagora: Wane gonas Sardauna,

 ‘Y/ Amshi: Amman a gonas Sardauna,

,

Jagora: Ni na Auta na Kalgo mai,

‘Y/ Amshi: Waƙag gona,

 

  Jagora: Daudu gonas Sardauna,

 ‘Y/ Amshi: Gonas Sardauna,

 

  Jagora; Babban gonab Bakura,x2

 ‘Y/ Amshi: Gonas Sardauna,x2

 

 Jagora: Bani koma zuwa Gwanja,

: Allah ya hutassan,

: Ku tsaya mani,

; In zani na biɗat goron gwanja,

: Hwarhwaru[19] koko dai ja,

: Sai in gangara,

: Bakura ƙanen Sanda,

: Ga shi gonas Sardauna,

: Sardauna ya kahwa goro yai ɗiya,

: Nan aka ɗibassa a yona,

: Ko dubu bakwai,

: A rage saura,

: Gobe a tswage[20] dubu bakwai,

: Sai Sardauna,

: Sabadda albarkag gona.

 ‘Y/ Amshi: Saboda albarkag  gona,

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son,

: Ana kwanci banza.

 

  Jagora: Sardauna Amadu,x3

‘Y/ Amshi: Allah ya ƙara imanin giwa.x3

 

 Jagora: Shehu Ɗanhodiyo ya,

: Biya Makka ya roƙa ,

: To darajja mai dama,

: Sardauna Allah shi ma,

: Da arziki na Shehu,

 ‘Y/ Amshi: Da magana ta yi,

 

  Jagora: Yai roƙo yadda Allah,

: Yada yai ma Shehu,

:Sandar alhwarma[21],

: Rabbu Allah ya yi ma Amadu,

‘Y/ Amshi: In kwan jin daɗi.

 

  Jagora: Na gode ma albarkacin Sardauna, ,

: Na ji daɗi,

: Komi nike biɗa haka ya ban,

: Saboda,

 ‘Y/ Amshi: Sabadda albarkag gona,

: In rogo kab biɗa,

: Yi gonas Sardauna,

: In dawa kab biɗa,

: Yi gonas Sardauna. 

 

Jagora: Hausa[22] ga ni da mota,

: Sabadda albarkag gona,x2

‘Y/ Amshi: Sabadda albarkag gona..

 

  Jagora: Banda bashin waƙa,

: Zuwa ga gonas Sardauna,

: Komi nika so Sardauna

‘Y/ Amshi: Sardauna na miƙa min shi.

: Gonab Bakura,

: Gonas Sardauna,

 

  Jagora: Ɗai-ɗai-ɗai-ɗai,

 ‘Y/ Amshi: Aiki ba ya son,

:Ana kwanci banza.

 

Jagora: Shehu mi kaka rigima?,

: Ga mu gonas Sardauna,

: Ka ja man guda-guda,

: Bagudu kai dai,

: Ƙara kiɗin kalangu,

: Bai zan ɓanna ba,

: Amma na gonas Sardauna,

: Yadda nir riƙe waƙan gona,

: Zama ko komi nike biɗa,

: Ya ba Illo,

: Amadu na yi murna,

: Nai hwara’ah,

:  Nai ba’a na ƙara,

: Ina godiyar Allah,

: Zuwa ga albarkag gona.

‘Y/ Amshi: Zuwa ga albarkag gona..

 

  Jagora: A gaishe ku dai na gode,

‘Y/ Amshi: Gonab Bakura,

:Gonas Sardauna,

 

 Jagora: A gaishe ku dai na gode.

‘Y/ Amshi: Aiki ba ya son,

:Ana kwanci banza.

 

  Jagora: Hura na gona,,

‘Y/ Amshi: Ku zo ga albarkag gona..

 

Jagora: Tuwo na gona,

‘Y/ Amshi: A tai ga albarkag gona.

 

 Jagora: Kuɗi na gona,

 ‘Y/ Amshi: Saboda albarkag gona.

 

 Jagora: Ga gona.

‘Y/ Amshi: Sabadda albarkag gona.

 

 Jagora: Sutura na gona,

‘Y/ Amshi: Sabadda albarkag gona,

 

 Jagora: Karatu gona.

‘Y/ Amshi: Sabadda albarkag gona.

 

Jagora: Ba ni biɗar ayaba,

: In saye da kuɗɗina,

‘Y/ Amshi: Don akwai ta gonas Sardauna.

 

Jagora: Ba ni biɗam mangwaro,

: In saye da kuɗɗina,

‘Y/ Amshi: Don akwai shi gonas Sardauna..

 

 Jagora: Ni b ni biɗar alkama,

: Da kuɗɗina,

 ‘Y/ Amshi: Don akwai ta gonas Sardauna.

 

  Jagora: Ba ni biɗam masara.

: Da kuɗɗina

‘Y/ Amshi: Don akwai ta gonas Sardauna.

 

  Jagora: Ban biɗad dawa hwara,

‘Y/ Amshi: Da kuɗɗina,

: Don akwai ta gonas Sardauna.

 

  Jagora: Ban sayen samba Maikiɗi.

‘Y/ Amshi: Da kuɗɗina,

: Don akwai ta gonas Sardauna.

 

 Jagora: Ban sayen acca Maikiɗi.

‘Y/ Amshi: Da kuɗɗina,

: Don akwai ta gonas Sardauna.

 

 Jagora: Ban sayen mangwaro ɗan Kano,

‘Y/ Amshi: Da kuɗɗina,

: Don akwai shi gonas Sardauna.

 

 Jagora: Ban sayen gwaiba Maikiɗi.

‘Y/ Amshi: Da kuɗɗina,

: Don akwai ta gonas Sardauna.

 

 Jagora: Ga wake.

: Ga maiwa,

: Ga gujiya,

: Ga yalo,

: Ga kudaku,

: An kahwa shi,

: Gonas Sardauna,

: Ga rogo,

: An aje shi,

:Gonas Sardauna,

: Ga masara,

: An kahwa ta,

: Gonas Sardauna.

: Ga ayaba,

: An zuba ta,

: Gonas Sardauna,

‘Y/ Amshi: Had dabinon Agadas,

: Akwai shi,

: Gonas Sardauna.[1]  Zaman banza babu aikin yi.

[2]  Manya-manya, waɗanda suka ƙoshi ƙwarai.

[3]  Ya yi amfani da salon dabbantarwa a nan inda ya kira Sardauna da giwa.

[4]  Dankali.

[5]  Shinkafa wadda aka gyara aka cire kwalfarta sai dafuwa.

[6]  Yatsun hannun dama.

[7]  Sauka/zuwa.

[8]  Wanda ya fara yin wani abu.

[9]  Tari mai yawa.

[10]  Yin birgima.

[11]  Tsalle-tsalle.

[12]  Tsallen murna.

[13]  Jin daɗi.

[14]  Farin ciki wato cikin daɗin rai.

[15]  Wata ciyawa ce mai tsawo.

[16]  Tsuttsunke.

[17]  Daɗin abu mai ɗanɗano.

[18]  Farfashewa .

[19]  Farare.

[20]  A cika buhu ana dannawa sosai har ya cika tim.

[21]  Girmamawa.

[22]  Ƙasar Sakkwato.

Post a Comment

0 Comments