Wakar Noma Ta Abdullahi Danburji (Mai zanbunan Morai)

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Waƙar Noma Ta Abdullahi Ɗanɓurji (Mai zanbunan Morai)

    Taƙaitaccen Tarihin Abdullahi Ɗanɓurji

    An haifi Abdullahi Ɗanɓurji (Mai zambunan Morai) a ranar ɗaya ga watan bakwai shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da uku (1/7/1963) a garin Morai ta ƙaramar hukumar Talatar Mafara. Ya gaji kiɗansa ne tun daga kakansa mai suna Magaji Musa, wanda aka fi sani da suna Magajin Zambo Morai. Ya fara kiɗansa ne daga bisani bayan ya ɗan tasa, kayan kiɗansa su ne ake kira zambuna yana kiɗin sarauta ne da na noma. Yana da yara masu yi masa amshi guda shida kamar haka:

    1.                  Abdullahi Kyalla

    2.                  Janaidu

    3.                  Lawali Tubali

    4.                  Muhammadu Ɗanbuki

    5.                  Abdulmaliki Na’unwala

    6.                  Sanusi mai Iye.

    Waɗannan su ne ‘yan amshinsa waɗanda yake yawon kiɗansa da su wato su suke riƙa masa aikin waƙoƙinsa.

    Abdullahi Mai zambuna yana da matar aure ɗaya mai suna Aishatu, kuma yana da ‘ya’ya shida, huɗu daga cikinsu maza, sauran biyun mata. Mazan sun haɗa da Attahiru da Musa da Sambo da kuma Muhammadu Bello. ‘Yanmatan kuwa sune Suwaiba da Maryam.

     

    Makaɗa Abdullahi Morai ya yi waƙar noma ta manoman shinkafa ne, waɗanda ya kira da suna masu kadada. Abin kiɗansa sunansu zambuna kamar yadda ake kiransu a Morai da kewaye, wannan ne ma ya sa ake kiran sunansa mai zambunan Morai.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.