Ticker

6/recent/ticker-posts

Masu Kadada

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

 Masu Kadada

 

  G/Waƙa: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

 Jagora: Allah mai sama Sarki,

: Taimaki dogo mai buga turu.

 

‘Y/ Amshi: In ci gumi tun ban yi gumi ba.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

 Jagora: Gyara Allah Mai sama sarki,

: Ar rahamani Jalla gwanina,

: Taimaki Dogo mai buga turu.

 

  ‘Y/ Amshi: In ci gumi tun ban yi gumi ba.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

 Jagora: Ka agaji Dogo mai buga turu.

  ‘Y/ Amshi: In ci gumi tun ban yi gumi ba.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

 Jagora: Jallah ka agaji Dogo mai buga turu. 

  ‘Y/ Amshi: In ci gumi[1] tun ban yi gumi[2] ba.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

Jagora: Farin cikina in ga kadada,

  ‘Y/ Amshi: In ga ana aiki bisa laka,

: Na san alheri aka nema.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

Jagora: Gwari da tat tiƙa masu kashi,

: Dub bana sun koma ga kadada,

: An ci ƙaya kuma an kashe gumbi.x2

  ‘Y/ Amshi: An hana sangale tai niya toho.

 

 Jagora: Daɗa an ci ƙaya kuma an kashe gumbi,

‘Y/ Amshi: An hana sangale tai niya toho,

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

Jagora: Ban iya ram maku masu kadada.

  ‘Y/ Amshi: Tunda abinci na kuka nema,

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

  Jagora: Amma ku sani ku masu kadada,

: Kowa nat tai zashi kadada,

: To ya sani sai ya yi da kuɗɗi,

: Ƙarhi zalla ba shi kadada,

‘Y/ Amshi: Yanzu kadada na halaka ka.

 

Jagora: Ƙarhi zalla ba shi kadada,

 ‘Y/ Amshi: Yanzu kadada na halaka ka.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

Jagora: Amma ku sani ku masu kadada,

: Kwas shiga daji zashi kadada,

: Ya zanka yin ta da kuɗɗi,

: Karhi zalla bashi kadada.

  ‘Y/ Amshi: Yanzu kadada na halaka shi,

 

Jagora: Ƙarhi zalla ba shi kadada,

 ‘Y/ Amshi: Yanzu kadada na halaka ka.

 

Jagora: Ga wani yaj je ya yi kadada,

: Ta dwage[3] mai baya da kuɗɗi.x2

 ‘Y/ Amshi: Yay yi zurun sai ya aza kuka,

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.x2

 

Jagora: To kai kas san ba ka da kuɗɗi,

: ba ka da kowa ba ka da komi,

: Don Allah mik kai ka kadada.

  ‘Y/ Amshi: Ko wata alhwarma[4] kaka nema.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

  Jagora: Sarkin noma faɗa mini komi.

‘Y/ Amshi: Inji batun aikin ga da yay yi,

 

  Jagora: Yac ce man bari Auduwa dogo,

: Shi sabon aikin ga da yaz zo,

‘Y/ Amshi: Ya kashe wa kuma ya kashe ƙanne.

: Ba ya barin manyanmu da kuɗɗi.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

.

 Jagora: Shi sabon aikin ga da yaz zo,

: Ya kashe wa kuma ya kashe ƙanne.

‘Y/ Amshi: Ba ya barin manyanmu da kuɗɗi,

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

 Jagora: Sarkin noma da yay yi kadada,

: Bakin hanya yay yi kadada,

: Ya shiga wawa ya yi kadada.

 ‘Y/ Amshi: Ya zama wawa ya gaza gyara,

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

  Jagora: Hanyak Kaura ya yi kadada,

: Uban ƙasa ya sa mashi hannu.

: In bancin an sa mashi hannu,

 ‘Y/ Amshi: Da bana ya ɓata mana suna.

 

  Jagora: In bancin an sa mashi hannu.

 ‘Y/ Amshi: Da bana ya ɓata mana suna.

 

Jagora: Ana ta kiran ba noma gabaɗai.

 ‘Y/ Amshi: Ka yi kadada ka gaza gyara,

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

Jagora: Duh hwadama[5] duka an yi kadada,

: Rwahin gulbi shi ka kadada,

: Rwahin tafki shi ka kadada.

: Na san temi bashi kadada,

: Sannan ƙozo bashi kadada.

 ‘Y/ Amshi: Ƙozon Ɗanruwa na halaka ka.

: Masu kadada masu kadada.

: Shinkahwar rani suka noma.

 

 



[1]  Shinkafa wadda aka cashe aka fitar da ƙwayarta.

[2]  Zufa/Jiɓi, wani ruwa da ke fitowa daga jikin mutum a sakamakon yanayi mai zafi.

[3]  Rikicewa/kwaɓewa, mutum ya rasa wurin kamawa.

[4]  Neman wata biyan buƙata.

[5]  Fadama, gonaki masu jigawar ƙasa, wato laka mai ajiye ruwa, an fi shuka shinkafa a irin wannan wurin. 

Post a Comment

0 Comments