Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Zinariyar Jibo Jikan Mamman
G/ Waƙa: Ai zinariyar
jibo jikan Mamman,
: Gun marafa ban renama ba.
Jagora : Zinariyar jibo jikan mamman,
: Gun marafa ban renama ba,
: Ina iri game gona maƙi gudu malam
tela,
: Sannu a gaisheka Ɗan
galadima malam,
: Ai kayi kyau da bada kyauta sai tanko,
: Don Allah bada girma ga manya,
: Tanko rabagga mai sabon gayya,
: Ai tun daga zuru har riva hat ƙiri,
: Ai tankole duk da ayyubin na sa.
Jagora:
Ni kulu na ɗa mai kamarka kai
malam Tanko,
: Ai kyau da bada kyauta sai Tanko,
: Sannan da bada girma gungun manya,
: Tanko ɗa banga mai kama mai ba,
: Ai duk yag gane ni sai ya ba ni,
: Kuma tambayar ya kai mid dameni,
: Ke kuluwa hauwa me ciki mis same ki,
: Kulu duk a ƙare kina huskar Ladi,
: Ke kulu ko ko hatsin daka ne babu,
: Ai na ne a kwai hatsin malam tanko,
: Ke kulu ko ko tuwon ciki ne na katse,
: Ai na ce akwai tuwon malam Tanko,
: To kulu ko ko kuɗin kashi ne babu,
: Na ce akwai kuɗin malam Tanko.
Jagora : Ai
Hauwa Kulu ko lafiya jikin nan na katsa?
: Kulu ina lafiyar jikin nan na katsa,
: Ke Kulu na so a tai gida ayi allura,
: Tun dai nan zaman mutum bawan Allah,
: Ai ya nuna tunbin giwa,
: Ina biri jikan aisha,
: Ai da kai da dila,
: Ai gardamar ku,
: Da jemage batun hawa bisa[1],
: Sai kai ƙanen diringi mai gora,
: Ha da ɗan ɗoruwa da takalman waso,
: In dai ta liƙe niya don
galmingo,
: Kai daɗi na nana banɗi bai san tsoroba,
: Mugu niyaɗi doruwa ta yaɓe ni,
: Duk da bako ka biri don wankame.
Jagora : Ai
Hauwa ko da ban Hillanci,
: Amma dai wari ja’o
ita na gane,
: Ni Hauwa ba
ni son waƙar jauru,
: Daɗe wala- na ce wala,
: Niɗɗi wala cedi wala,
: Kutu kaɗi woɗi tubarkallah,
: Na zan jiran machata na ba ni,
: Ba ni gidan da ba ni ƙamna in
gode,
: Ina iri game maƙi gudu gan
mai zobe,
: Aiirin Jibo ɗan Mamman.
0 Comments
Post your comment or ask a question.