Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Infiraji

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙar Infiraji

 1. Ya ilahil Arshi ba ni,

 Hankali da yawan bayani,

 ‘Yan’uwa suka tambaye ni,

 In ma waƙa tamu sani,

 Gyara ba zai kamar kashi ba.

 2. Gargaɗi mai bada tsaro,

 Nai nufi da hani da horo,

 Duk maso rahama ya taro,

 Hankali babba da yaro,

 Sai wanda ba za shi lahira ba.

 3. Sa idon natsuwa ka duba,

 Duniya ba mu zo zama ba,

 Duba Hairul halƙi in ba

 Wauta da rashin natso ba,

 Ka tuna ba za mu dawwama ba.

 4.’Yan ‘uwa ku mu bar sakewa,

 Kun ga girman Annabawa,

 An kira su zuwa kushewa,

 Wanda wai shi don daɗewa

 Ya zata ba za shi lahira ba.

 5. Yai ma kaimugun hasara,

 Ya bi mummunar dabara,

 Ya ɓace da rashin basira,

 Sai shi zo da dubun lalura,

 Shi faɗi ba za ta karɓuwa ba.

 6. Mai tuƙe masa hanzarinsa,

 Tawwafan tsararrakinsa,

 Jinjiri a cikin uwarsa,

 An kira, tilas ya amsa,

 Ta bare, ba zai zauna duniya ba.

 7. Wasu ko da ƙurciyarsu,

 Wasu ko a kira uwarsu,

 Tun suna tsumma ta bar su,

 Wasu nuƙuda ta kar su,

 ‘Ya’yan ba su leƙa duniya ba.

 8. Ga ka mai wa’adi daɗaɗɗe,

 Mai ya sa wawa ka ruɗe?

 Ko zama wundi ka harɗe?

 Shekarunka da sun ka shuɗe,

 Ka tuna ba za su komuwa ba.

 9. Tun kana yaro a tsumma

 Ke faɗin mutuwa, ka girma,

 An mace a gabanka, har ma,

 Kai rashin tsoffinka, amma

 Ba ka shaida taka na zuwa ba.

 10. Tattalinka adon zubuni,

 Ko dara ka hawar da huni,

 Wai a ce maka mai sukuni,

 Zuciya ko ba yaƙini,

 Ba ta shaida za ka lahira ba.

 11. Me ya sa ka yawaita homa?

 Ko tuwo da fura da nama?

 Ko ado da asho da laima?

 Bar ta sallah ko iƙama,

 Ba ka ma iya ida Fatiha ba.

 12. Sai ka sha ka ci kai nishaɗi,

 Kasuwa ta zo da buɗi,

 Cuce-cuce ba a taɗi,

 Wanda yasshiga wanga ruɗi,

 Ba zai daraja a lahira ba.

 13. Tun da sauran hankalinka,

 Yaƙi birnin zuciyarka,

 Nemi tauhidi kaza ka,

 San su alwala da wanka,

 Tun ba a aiko ma Mala’ika ba.

 14. Ka sani rai ba shi wanzo,

 Tsai da sallah kai ta ƙwazo,

 Kai hajji ka ziyarci Manzo,

 Ran da duk mutuwarka ta zo,

 Ba ka je a cikin rashin shiri ba.

 15. Yanzu ‘yan bori da boka,

 Sun kusaci su hallaka ka,

 Zabiya ta ƙarashe ka,

 Tun da ta ce ba kamar ka,

 Baka ƙara barin takabbura ba.

 16. Da maniyyi farkonka,

 Kumfa mussai ƙarashenka,

 Najasa ke tsattsakinka,

 Me ya ƙarfafa taƙamarka,

 In ba ruɓushi da hallaka ba.

 17. Ga shi ka tozarta kanka,

 Son kuɗi ya sa ka shirka,

 Da dubun miliyan gare ka,

 Ran da ka mutu sai a kai ka,

 Da tufan da ba zai yi fam bakwai ba.

 18. Ka ci ka sha ka yi taiɓa,

 Ka mace ƙabari ya karɓa,

 Ka ruɓe tsutsa ta sharɓa,

 Yanzu me ya fi kyau ka zaɓa,

 In ba farali da nafila ba.

 19. In tuna maka in ka mance,

 Tun kana ciki kun yi zance,

 Kai da Rabbul Arshi, ka ce,

 Za ka bi shi ka ko amince,

 Da ibadatai, ba kai musu ba.

 20. Ka riƙo wa’adi ga Allah,

 Za ka yin azumi da sallah,

 Hajji, zakka, ga kasala,

 Ta tsare ka cikin jahala,

 Ba ka nemi sani ga maluma ba.

 21. Wanda bai biɗi malamai ba,

 Ba shi aiki mai sawaba,

 Wanda bai yi gamon katar ba,

 -------------------------------

 Tun da dai ba zai yi tambaya ba.

 22. Ka ga yai wa kansa ƙeta,

 Ƙoƙarinsa shikan raba ta,

 Ukku: ci, tufuwa da mata,

 Tun da issha in ya kwanta,

 Rana kan huda bai sani ba.

 23. Ran da yai azumi masiba,

 Ta haɗam masa ba kaɗan ba,

 Sai ya tara hali da dabba,

 Ba halin dabbar ƙwarai ba,

 Ba kamar mussa da karnuka ba.

 24. Shi kinin jaki da doki,

 Ne, zuwa gwanki da kanki,

 Ƙoƙarinsa shikan fi auki,

 Ne a ƙare dare da taki,

 Bai damu da wanke jannaba ba.

 25. Bar zaton tsarkin ibada,

 Gun mutum mai wanga ada,

 Ya ɓace har zuci tun da,

 Ba sanin kalmar shahada,

 Shi ko ba zai yi tambaya ba.

 26. Shi fa jahilci ya sarbu,

 Ne na kafirci ga aibu,

 Wanga zan ce ya zamo bu-

 Ɗin batun Malam Habibu,

 Da shikan mana ba abin musu ba.

 27. Shi ya ce mana ai jahala,

 Shi da kafirci ga illa,

 ‘yan ‘uwa na, la muhala,

 ‘yan kwanika ma la’alla

 Girman ba zai wata bakwai ba.

 28. Shi batu nasa gaskiya ne,

 Don hadisin Musɗafa ne,

 Sayyadil wara in ka gane,

 Ka ga shaiɗanun mutane,

 Ibilis bai fi su kangara ba.

 29. Jahilai kau yai ma zance,

 Don hadisin na rubuce,

 Na ji Alƙali shina ce,

 Zuciya in ta makance,

 Fa ganin ido bai yi fa’ida ba.

 30. Fassaran ga na Alkarimu,

 Shi ya fari batun ga namu,

 Anguwar Juma na samu,

 Nan ga Alƙalin ga namu,

 Tun watan Ramalana bai raba ba.

 31. Yai batunga da ni da malam,

 Yakubun kusfa muna zam-

 Ne yai shi tamasuli kam,

 Tun riƙon sarkinmu malam,

 Kawa Ja’afaru bai yi shekara ba.

 32. Jahilai kau sun fi son jin

 Shafe ilmi, wai su bar jin,

 Gargaɗi, tilas su kau ji,

 Ba da son kura a daji,

 Yunwa kan ci shi har ƙwado ba.

 33. Kar ka ba mutuwa aminci,

 Don wada ko don talauci,

 Don yawa ko don kaɗaici,

 Ta haɗam ma waɗansu gun ci,

 Ba su tauna abin da sun haɗe ba.

 34. Ta taho ta ɗauki sarki,

 Mai hawa da dubun dawaki,

 Ga dubun matsara a ɗaki,

 Inda ma ta fi ƙara auki,

 Bata bar fanko maras kwabo ba.

 35. In ta zo ba tsaitsayawa,

 Ko da ƙoshi ko da yunwa,

 Ta fi komai tsoratarwa,

 Ɗalibi har mai sanarwa,

 Ba a san ɗaya wanda ta rage ba.

 36. Mai kuɗi ko mai sarauta,

 Kowane ya ji tambarinta,

 Sai shi firgita don amonta,

 Don saboda sanin halinta,

 Ita ba tararta lafiya ba.

 37. Tambarinta gare mu kuka,

 In da rani in da kaka,

 San da duk ta bi sai a doka,

 In da dai mutuwa ta sauka,

 Ai ba ka rasa jin kururuwa ba.

 38. Tare dai ku ke ko ina ne,

 Ko kana tafe ko a zaune,

 Ba ta kunyar ko su wane,

 Da tana da makangari ne,

 Ai da Namaruzu bai mace ba.

 39. Dubi dai Fir’auna wai shi,

 Ne ɗagawa ba kamar shi,

 Har cikin ruwa ne ta bi shi,

 Bai haye ba ta maƙare shi,

 Bai kai ga abin da yai nufi ba.

 40. Ba ta sasanta ma kowa,

 In ta zo bata ragawa,

 Saurayi ko ko budurwa,

 Ɗai shi kan bar ɗai da kewa,

 Ba ta zo masa san da ya sani ba.

 41. Shin kira nata wa ya keɓe,

 Kibiya tata wa ta zaɓe,

 Ta bi ƙarfafa ta sharɓe,

 Da akwai maguda a raɓe,

 Su kumama da ba a mace ba.

 42. Ta cira sama ta saɗaɗo,

 Ta buge shaho ya faɗo,

 Ya mace barshe fa kwaɗo,

 Ƙarƙashin ƙasa in ta kurɗo,

 Ba ta ƙyale kuɗau da kurkudu ba.

 43. Ƙin biɗa ko tare tare,

 In ta zo ɗaya ba shi kare,

 Ma zuwanta cikin darare,

 Ko da rana cikin sarare,

 Ita ba tarar takai shiri ba.

 44. Zahiri a zaton ta yaƙi,

 Ko wuta ko ko ga biƙi,

 Ta taras da mutum masaƙi,

 Ya zage ya ƙare miƙi,

 Ya mace bai jefa ƙoshiya ba.

 45. Sanadi ga waɗansu doki,

 Wasu ko sanadinsu zaki,

 Wasu ko su mace a tafki,

 Wasu ko sanadinsu ɗaki,

 Shi zubo masu ba cikin shiri ba.

 46. Dubi dai manyan mazaje,

 Masu shan kotso da jauje,

 Sun wuce, manyan gwaraje,

 Soba mai baya da ƙauje,

 Ka cane ba za ka Lahira ba.

 47. Dubi dai ga sarakunanmu,

 Wanda sunka riƙe ƙasarmu,

 Masu ko darja gare mu,

 Dubi Shaihu Mujadadinmu,

 Ka tuna ba za mu dawwama ba.

 48. Yau ina Sarkin Musulmi,

 Bello, ko Abdul’karimi,

 Musa ko Abdussalami,

 Sun wuce, wannan muƙami,

 Ba a san ɗaya wanda zai rage ba.

 49. Ummarun Dallaji Korau,

 Ya mace, yaro ɗansa Kwasau,

 Basu Ɗalhatu yau a Zazzau,

 Su Abashe ina Aliyu Babba?

 50. Sun wuce sai ambaton su,

 Sai tunanin arzikinsu,

 Kyan adonsu da kyan hawansu,

 Ba ka ƙara ganin ɗayansu,

 In ba zuriyar da sun bari ba.

 51. Rabbi mun roƙe ka Allah,

 Don isar azumi da sallah,

 Don yawan falalar Risalah,

 Kar ka bar mu cikin jahala,

 Da abin da ba zai yi fa’ida ba.

 52. Ko da dai laifi tudu ne,

 Naka wanda ka tattara ne,

 Ke hawa ka gano na Wane,

 Ga mutum mai gargaɗi,

 Bai bar saɓon Ubangiji ba.

 53. ‘Yan ‘uwa in tambaye ku,

 Na ga zurfin wawutanku,

 Don ɓacewar hankalinku,

 Bibiyar son zuciyarku,

 Ba ta barku kuwaiga lahira ba.

 54. Soya tantabaru da kaji,

 Ko miyar taushe da goji,

 Ko hawan rali da roji,

 Ke daɗin tura ku daji,

 Ba ku san mutuwa tana zuwa ba?

 55. Ko yawan sanyin sumunti,

 Ke hana maku son salati,

 Zabiya mai tada sauti,

 Ke hana ku tunin wafati,

 Ba juyayinku lahira ba?

 56. Sai burodi da kyat da masa,

 Sai zuma a cikin gurasa,

 Sai da jin wa’azi ku nisa,

 Kui zugum, bai sa ku fasa,

 Aikin saɓon Ubangijiba.

 57. Mai kiran mata kawali,

 Nan da nan kuka ba shi jali.

 Kun ƙi ba da haƙin iyali,

 Wanda ma yab ba ku mali,

 Ba ku daina abin da yai hani ba.

 58. Kafiri ko ko shƙiyyi,

 Masu sambaru a layi,

 Masu mai da giya da shayi,

 Dai da su jama’a ka koyi,

 Ba su kwaikwayi masu hailala ba.

 59. Dubi ‘yan yara samari,

 Wanda su ya kamata dauri,

 Sui ta ilmi tun da fari,

 Gaskiya ta rigayi sharri,

 Yau ba shiriya suke nufi ba.

 60. Sai hululu da shan sigari,

 Ba su son istingifari,

 Sun fi jin maganar sharari,

 Mai faɗa masu zasu ƙabari,

 Daga baya garai su ba shi gaba.

 61. Sun tuɗas ma da kan su girma,

 Tun da ba su shirin makoma,

 Sai gurin ajo da silma,

 Hankalinsu shikan fi himma,

 Wai ba hidimarsu jumma’a ba.

 62. Yauhe mai wannan ɗabi’a,

 Ke tsare haƙƙin shari’a?

 Shi da dattijai mira’a,

 Ga mafi munin sana’a,

 Ba’a ci shi baƙi a gardama ba.

 63. Mun kuma roƙi sarki,

 Zuljalali, ka ba mu tsalki,

 Zuciya da jiki da aiki,

 Har ka sa a cikin mafarki,

 Mu ga Annabi ba da firgita ba,

 64. In na ratsa kufai zubabbe,

 Sa na kan tuna yau da gobe,

 Da mutane tai wa zobe,

 Yau wuƙar sarki da babe,

 Ya cika ta da ƙonsanal maharba.

 65. Ba a nesa ba ga Maƙera,

 Babu kowa fa sai fa kura,

 Sai karen buki shi ka ƙara,

 Sai fa jan ɓelbel da tsara,

 Tamkar ba su tara ‘yan Adam ba.

 66. Da garin sai masu iko,

 Yanzu ba ku masu tarko,

 Sai fa rimaye da ɓakko

 Soba mai son nuna fiko,

 Ba ka samu ya su a mallaka ba.

 67. Dandalinsu na cin abinci,

 Babu kowa sai kumurci,

 Ɗakunansu dila ka barci,

 Da tana da riƙon aminci,

 Da jangwarzo ba zai mace ba.

 68. Ya mace har ɗansa Yunfa,

 Tun da dai mamaya halifa,

 Larabawa masu iffa,

 Sun wuce, wake da ƙofa,

 Cewa ba za shi lahira ba?

 69. Ɗan ‘uwa, riƙa yi da lura,

 Ba a ci mata kau da bara,

 Sa kururuwa ɓata hira,

 Ko gidan gafiya da ɓera,

 Baka tsar mata in kaje gudu ba.

 70. In tazo dai na yawo,

 Ɗan fa shi ko ko ɓarawo,

 Babu shingin kai da kawo,

 Ba ta tarar sai da ciwo,

 Ita ba tarar ta lafiya ba.

 71. Tun da dai muka san akwai ta,

 Ba mu shakkar afkuwarta,

 Sai mu dai na faɗin halinta,

 ‘Yan uwa mui tattalinta,

 Tun rai bai kai ga tawwafa ba.

 72. Tattalin ta kiyaye haddi,

 Zuciya tai ijitihadi,

 Fai da ɓoye a bar fasadi,

 Har a kai ga biyan muradi,

 Ba sai an sance lafiya ba.

 73. Rabbana ka tsare mu kunya,

 Ko ɓata ko ratse hanya,

 Zuljalali ka ba mu shiriya,

 Zuciyar mu ta kama hanya

 Ba kau mai faɗa halaka ba.

 74. Ni da shitawa na saba.

 Tun gaban ban hankali ba,

 Sun riƙe ni, riƙo da kau ba,

 Ɗa dukansa akai mashi ba,

 In ba gatansa tai yawa ba.

 75. Shaihuna Abdura’ufi,

 Tun ina yaro la’ifi,

 Ya riƙe ni riƙo na zifi,

 Har ya zam na fara ƙarfi

 Bai bar ni cikin hakukuwa ba.

 76. Sai shi ce mini, “kai karatu,

 Ko da ba ka ganin rubutu,

 In ka gane ka wadatu,

 Da ya bi tahmisiri Tufuttu,

 Sai ban ji rabo kamar sani ba.

 77. Shi sani tamkar uwa ne,

 Gun marayu ko uba ne,

 Shi sani ma garkuwa ne,

 Kau ga mai tsoro gari ne,

 Ma shiginsa ba zai rawar ƙafa ba.

 78. Shi sani kan mai da bawa,

 Ɗa mafificin muruwwa,

 Arziki ne mai isarwa,

 In ka sama sa ko gaban wa,

 Ai ba ka zauna da firgita ba.

 79. In ka sami sani riƙe shi,

 Kam da ƙarfi kar ka bar shi,

 In ya kufce lalubo shi,

 Wanga zace ba shi ta shi,

 Kai ba ka rasa yin muwafuƙa ba.

 80. Maganin samun sa himma,

 Ce, ka dawwama in ka soma,

 Ko mai wahala ƙazama,

 Run gume ilmi a dama,

 Raggo ba za ya sha zuma ba.

 81. Kar ka yarda da mai kasala,

 Gun abuta don jahala,

 Shi kasa himma talala-

 Ce, mutum mai son kamala

 Ba zai bi maƙi muwazaba ba.

 82. In ka san ilmi kiyaye,

 Lokacin, sallah fiyayen,

 Arziki ga mutum na raye,

 Tsai da sunna fai da ɓoye,

 Ba ku tsa duhun kaba’ira ba.

 (Aliyu Namangi: Imfiraji ta biyu)

Wannan waƙa ta Imfiraji ita ma mashahuriya ce ƙwarai a bakunan mabarata musamman makafi. Ita ma ba domin bara marigayi Malam Aliyu Namangi ya wallafa ta ba, ya wallafa ta ne domin wa’azi da bege, amma mabarata suka mayar da ita abin yin bara. Haka kuma waƙoƙin imfiraji suna da yawa tun daga ta Ɗaya har zuwa ta tara, kuma kowace ɗaya daga cikinsu mabarata na amfani da ita wajen bara.

Akwai kuma wasu waƙoƙin waɗanda mabaratan ke amfani da su wajen bara waɗanda wasu mutanen suka rubuta su domin wani dalilin kamar wa’azi ko madahu da sauran irinsu:

Post a Comment

0 Comments