Na Ƙare Da Lauwali

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Na Ƙare Da Lauwali

     1. Ya Allahu na kiraika ina ƙuzami,

     Ba ilimi garan ba bani da ƙwazon komi,

     Amma na sani nufinka ka sa ai komi,

     Bismillahi Rabbana kai kay yo komi,

     Kai kay yo mu Jalla kai ka nufin ai komi.

     2. Mai ƙamnar Rasulu na murnar hirata,

     Su’ul mar’i ya fi son ya ji motsin Shata,

     Rabbul khalƙi na kira ka ina garkata,

     Arrahmani mai gamammar kyauta,

     Wanda ya san bayanin na unguwa da na babban birni.

     3. In banci ka Jalla bani sanin sunana,

     Ballanta sanin gida ko in san gona,

     Balle in yi kwance in huta ko kwana,

     Sarki wanda yai dare kana yai rana,

     Kuma shi yai yi damana kana yai rani.

     4. Mun gode ma Jalla ba da sanin kowa ba,

     Haka zahirinmu ba kalimar wargi ba,

     Jama’a ko waninmu kar ya sake don woba,

     Duk mai godiya ga Haliƙu ba ni ɗai ba,

     Sarkina guda da ya isa ba ƙarya ba.

     5. In ko don kana cikin daji ƙunƙurmi,

     Koko don zaman ka ɗan yaƙi zunzurmi,

     Kai bari mantuwa sanin Allah ak komi,

     In ya baka babu wanda ka cewa komi,

     In kuma ya hana ina wani mai ɗibar ma.

     6. Kowa ya sani akwai Allah sai Jaki,

     In ko ɗan talakka na koko ɗan sarki,

     Koƙ ƙi batun ga nawa ran tashi sai kulki,

     Ya man la ya mutu kai ab babban sarki,

     Allah wanda ya kirai ka kanai mai sauƙi.

     7. Jama’a ‘yan’uwa mu sake shiri mui tuba,

     Mu bi Allah Ubangiji tun bai aiko ba,

     Tafiya lahira mukai ko bamu shiryo ba,

     Kwaƙ ƙi batun Ubangiji in bai luro ba,

     Da zuwa lahira jahannama na mai zoba.

     8. In kwananka sun cika ba mai ƙaro ma,

     Duk uzurin da ka faɗi ba mai karɓar ma,

     Kuma laifin da kai gidan duniya ya girma,

     Kai tuna Ubangiji don manzon girma,

     Allah agazan ni ba don ƙwazona ba.

     9. In an tsince ran mutum ya ko zama gawa,

     Ba shi batun ɗiya da mata balle bawa,

     An kai shi can cikin ƙabri sai kewa,

     Ka san tattalin gidan duniya sai wawa,

     Har ranar da anka kammai bai shiryo ba.

     10. Kowa adda rai shi san mutuwa ab baya,

     In ka sami lahiya ciwo ab baya,

     Bari saɓo tutut ana ƙara ma kaya,

     Sheɗan na ga zuciyarka shinai ma ƙarya,

     Tuba ga Jalla ba da takhirin komi ba.

     11. Tsarci Ubangiji ka san Allah ya aiko,

     Musulunci garemu tauhidi af farko,

     Sallah ko ga lokaci mu tsare tun farko,

     Har azumi abinda kaɓ ɓata sai ranko,

     Kwaƙ ƙi batun ga ya yi kafirci sai tuba.

     12. In ka sami dukiya ka yi zakka daidai,

     Har nomanka lissafa ka hukumta daidai,

     Ga na biyat cikin su in lisafta daidai,

     In layyak ka ta yi banda sakewa kai dai,

     Tafi hajji ka yo shi ba yawon banza ba.

     13. Kai bar tattali ka ima yawan aibobi,

     Sai ka ci ɗai ka sha ka ɗora yawan rubobi,

     Kenkendi da riguna wasu kau jabbobi,

     Ko tarin buhuhuwa ka aje tsabobi,

     Har mutuwa ta sauka ba da shirin komi ba.

     14. Shi wawa yana zaton khairi na yay yo,

     Bai shirya da Lahira ba sai duniya yas shiryo,

     Nashi nufi shi adana komi yay yayo,

     Alfasha da munkari su na ɗai yayo,

     Ya bar tuna yau da gobe ba ta barin kowa ba.

     15. Ka san dunig ga bata zamowa kullum ,

     Lura da ‘yan’uwa suna ta wucew kullum,

     Kwanukkan ka kau suna ta ragewa kullum,

     Sai haukak ka ɗai ka ƙara turewa kullun,

     Ka mance kamar Tabaraka bai aiko ba.

     16 Ku koma ga godabe bin shiriya shi ya fi,

     Tsarci Ubangiji ka zanka kiran ya khafi,

     Ko sheɗan da kag ga na ƙara ma ƙarfi,

     Nashi gida da taffi wutaitai zafi,

     Nan shika tabbata cikinta ba a fissai ba.

     

     17. Kwab bi ta duniyag ga ya lalace banza,

     In don tattalin ka tcarma rashi ya haza,

     Kad dasa albasa walau taba ko gwaza,

     Komi gare ka ya tafi bakin banza,

     Kul an turbuɗe ka ba da shirin komi ba.

    18. Ya ahalil uƙuli kada mu sake don ƙarya,

     kwab bi ta duniya shina komawa baya,

     Tsufa na zuwa kana ta faɗa don gaya,

     Sheɗan ya tsare ka ba gaba balle baya,

     Har ka kwanta dama ba da shirin komi ba.

    19. In ilimi gareka shi ka hana ma tuba,

     Lura da malaminka ya tafi bai dawo ba,

     In kau dukiya gare ka kana wata ƙaba,

     Tajirran garinku sun tafi basu komo ba,

     Wawa ya ɓace ga banza bai luro ba.

    20. In iko gare ka shi ka hana ma tuba ,

     Ka ga uban gidanka ya tafi bai komo ba,

     Zancen gaskiya nikai ma ba ƙarya ba,

     Tsare haƙƙin Ubangiji ni ba don ni ba,

     Ko laifin da ag garan ma ban gyaro ba.

    21. Tsarci Ubangiji ka san Allah as sarki,

     Dubi sama’u ta tsaya da nufi nai sarki,

     Ga rana kaza wata ƙudura tai sarki,

     Wa’ iya abinga sai shi babban sarki,

     Kun fa yakunu ba da tasirin komi ba.

     22. Kuma ya shimfiɗe ƙasa da wurare bamban,

     Da tudu nai da rafuka da duwatsu bamban,

     Dubi tsirin hakukuwa da itace bamban,

     Duk Rabbul ibadi masu kamannu bamban,

     Shi yay yo mu ba da ko wahalar komi ba.

     23. Ga aljanna can gidan ni’ima ta yay yi,

     Hurul aini na ciki nata balle baya,

     Babu zufa walau ka ce iska ko sanyi,

     Shinfiɗu iri-iri da gidaje an yi,

    Kowa ac ciki ba zai yi rashin komi ba.

     24. Ya yo ta gida bakwai da nufi nai sarki,

     Ya ko sa maruruwa ciki ga sarƙoƙi,

     Can aka ɗaure kafiri a aza mai kulki,

     Hargowa ciki nata tamkar jaki,

     Har abada shina ciki nata ba a fissai ba.

     25. Mutuwa zamu yi mu bar aikin ganganci,

     In yaji gare ka ba shi barin ka shanci,

     In ƙarfi gare ka ba ta barin kai santsi,

     Ni dai zulluminta shi ka hana man barci,

     Ban san ran da za a aiko manzona ba.

    26. Ko ga zaton da kay yi ranka ana barma shi,

     Sheɗan ya shige cikinka yana lallashi,

     Duk aibin da kag gani shi nay yo ma shi,

     Zamakin ya fi son ka zo a nasa garwashi,

     Kai ka ɓad da kanka ba don laifi nai ba.

    27. An haife ka tun kana yaro ka girma,

     Jinƙai wanda duk a kai Alla ya yo ma,

     Ayoyin Ubangiji kuma na safko ma,

     Ga wa’azi gare ka ka zama tamkar kurma,

     Ga nasihad da anka yo ma baka hango ba.

     28. In Allah ya yi ma shiriya ka falko,

     Dubi mutanen da sunka wuce tun farko,

     Mutuwa ba ta rangwame in kaw ta safko,

     In tauri gare ka dubi su ƙumba kasko,

     Mutuwa ta wuce da shi tun bai shiryo ba.

     29. In raunin jiki gareka daɗa kai wawa,

     Ko kabrin jiki kamar babanen Adawa,

     Dubi Hasan na Mutti ya zamna Badarawa,

     Malakul mauti ya riƙai ya ko zama gawa,

     Daɗa sai tuntuni da ya tafi bai dawo ba.

     30. Daga bisa Adamunmu har kawowa Musa,

     Har ga Ahma har bisa sabkar Isah ,

     Duk tafiya sukai bale mu nan ‘yan kusa,

     Kai duba akhi kasan tafiya tai nisa,

     Sai mu yi tattalinta tun dai bata sabkoba.

     31. Mai zancan fululi ya bari kozon banza,

     Zanka salati ka da kazo ka ɓakalce banza,

     Koki batun nabiyu ya lalace banza,

     Duk kwazon da yayyi ya tafi bakin banza,

     Zamakin babu maganin zunubi sai tuba.

     32. Tammat wa’azu mun cika Allah bai lada,

     Daga nan ‘yan uwa kuzanka har abada,

     Ba fakhari nikai ba don dai kamnar lada,

     Mai kamnar rasulu duk shi rika don lada,

     Don shiriya a kan bi ba aikin banza ba.

    33. In sun tambayeka mai waken kaji,

     Ce liman Alu na Isa daɗa shi ya yi,

     Dori tana hululiya sakewa yayyi,

     Don kamnar rasulu shi dai bege yayyi,

     Da yabon jalla ba fululiyar banza ba.

     (Liman Isa: Na ƙare Lauwali)

    Wannan wata shahararriyar waƙa ce da mabarata ke amfani da ita wajen bara a yankin ƙasar Hausa. Waƙar limamin Isa ne ya wallafa ta saboda yabo da begen Annabin rahama, amma kuma ta kasance mashahuriya ga amfani da ita wajen bara. Kusan kowane lungu, mabarata na amfani da wannan waƙar. Wasu sun hardace ta duka wasu kuma sun hardace wasu ‘yan baitoci masu wadatar da su ga yin bara.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.