Ticker

6/recent/ticker-posts

Ƙirarin Amada Ta Asma’u ‘Yar Shehu.

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Ƙirarin Amada Ta Asma’u ‘Yar Shehu.

 1. A mu gode Sarki mai sarauta sarmada,

 Subhana sarki wanda yay yi Muhammada.

2. A mu zan salati tutut muna yin sallama,

 Bisa Annabin mu yaf fi kowa Ahmada.

3. A ku karɓa waƙa don kirari da za ni yi,

 Jama’a ku karɓa mui kirarin Ahmada.

4. Allahu yah hore mu ga yabo nasa,

 A mu sami annuri da hasken zucciya.

5. A mu sami annuri da hasken zuciya,

 A mu tsarkaka ga yabon Fiyayye Ahmada.

6. Mu roƙi tuba jalla mai kyauta kusa,

 A shi ba mu shi domin darajjar Ahmada.

7. Mun roƙi gafara ko shi gafarta mana,

 Sarki karimun don Fiyayye Ahmada.

7.  Fikon fiyayye ya fi kwanne gwargwado,

 Ga faɗin Ta’ala yaf fi ɗaukaka Ahmada.

8.  Sama ta fa ɗaukaka kun sani ba ta kai kamar,

 Nisan kwatancin ɗaukaka ta Muhammada.

9.  Al’arshi ya komo tharahu ga ɗauka,

 Dan ɗauka tai Annabinmu Muhammada.

10.  Haskensa ya fi wata na arba’ata ash ara,

 Don babu annuri Kaman na Muhammada.

11.  Hakana ga zarumci zama duka zarumi,

 Bai kai ga zarumcin Fiyayye Ahmada.

12.  Almiski har kafur ku san duka ba su kai,

 Ƙamshi na al’udin jiki na Muhammada.

13.  Hakanan ga kyawo ko ga zati ba wa shi,

 Don babu ko dukka Kaman na Muhammada.

14.  Ba a yo ga tahalikai kama tai nan dai ɗai,

 Ba za a yi abadan kama tasa, Ahmada.

15.  Hakana ga halki masu sha’wa ba wa shi,

 Fara’a da kyawon murmushi na Muhammada.

16.  Ai shi fa ba shi hushi ku san shi fa gaskiya,

 Saɓo kaɗai shi kawa hushi fa Muhammad.

17.  In yai hushi kau babu duk mai I masa,

 Ga bida shi hanƙuri sai da tuba Ahmada.

18.  Hakana da tarin hanƙuri ga mutum duka,

 Wa girgije malka kyauta na Muhammada.

19.  Allahu ko ya bashi mu’jiza mai yawa,

 Ƙur’anu ko ya isa al’jabi ga Muhammada.

20.  Mutuwar (r) wuta fa ta Farisa kau ya isa,

 Gulbi na Sawata ya ƙafe don Ahmada.

21.  Gina da ƙista ta tuɗe hal mobizai,

 Da ya yi mafarki sun ji tsoron Ahmada.

22.  Haka sha uku ga wata da yar rabu hal biyu,

 Da Buhari Tirmizi sun faɗa ga Muhammada.

23.  Ƙur’an ku san ko ya faɗi ya bayyana,

 Don mu’jiza tai shi Fiyayye, Ahmada.

24.  Rana na bisa ta faɗi ta zama la’asari,

 Domin Aliyu da yab biɗe ga Muhammada.

25.  Shi anka hauda Buraƙa can tafiya sama,

 Ba wanda yah hau sai Fiyayye Ahmada.

 26.Ya shafe akwaiya Ummi Ma’badi nan da nan,

 Bisa Mu’jiza tai ta yi nono, Ahmada.

27.Shi girgije ya wo fa inuwa taguwa,

 Ta kai shakawa can ga Annabi Ahmada.

28.Dokin Surakatu yai ƙafo don Mu’ujiza,

 Bisa kan fako don martaba tai Ahmada.

29. Zancen damo Wallahi ya isa mu’ujiza

 Hakanan barewa don Fiyayye, Ahmada.

30.Ƙurciya tai kwai ya faɗi ya bayyana

 Don mu’ujizatai, Annabimmu, Muhammada.

31.Ya ba ukashatu cana ice ya zamo,

 Yuƙa ga fama, Annabinmu Muhammada.

32.Gaba da mallaiku fa sun shaida ku san,

 Don mu’ujiza tai shi, Fiyayye, Ahmada.

33.Sauran ruwa fa kaɗan na alwalla tasa,

 Sun ƙwadda babba dud da yaƙin Ahmada.

34.Kuka da nishi su da babban ƙututture,

 Bisa mu’jiza rabuwa da Annabi Ahmada.

35.Ku sani yawa fa gare su basu ƙidayuwa,

 Da yawa Halimatu tag ga mu’jiza.

36. Allahu ɗai ya san su, Wahidi mai sani,

 Sarki da yaf fifita Annabi Ahmada.

37. Ya Rabbi mun roƙe ka tsiran Duniya,

 Domin darajja tai, Fiyayye Ahmada.

38. Ya Rabbi sauƙi ko na mutuwa hakaza,

 Dom martaba tai Annabinmu Muhammada.

39. Hakanan jawabin ko Nakiri da Munkari,

 Domin Fiyayye Al-Rusulu, Muhammada.

40. Ya Rabbi mun roƙe ka ni’ma Barzaha,

 Domin Fiyayye, Annabinmu Muhammada.

41. Ya Rabbi mun roƙe ka tsira lahira,

 Ran alƙiyama don Fiyayye Ahmada.

42. Ga awo na mizan ayyuka ko su fi,

 Nan masu kyawo don Fiyayye, Ahmada.

43. Ansar takardu Jalla Sarki Rabbana,

 Ana bamu hannun dama domin Ahmada.

44. Ya Rabbi sa mu shiga ceton Annabi,

 Ana bamu hannun dama domin Ahmada.

45. Ya Rabbi sa mu shiga ga ceton Annabi,

 Domin darajja tai Fiyayye, Ahmada.

46. Ya Rabbana shashe mu ko Alkausara,

 Tabkin Fiyayye, Annabinmu Ahmada.

47. Ya Rabbana tsarshe mu gobe wuta ka kai

 Mu gidan raha, Aljanna domin Ahmada.

48. Ya Rabbana mu ga gobe huska (r) Annabi,

 Domin darajja tai, Fiyayye Ahmada.

49. Ya Rabbana mu ga haka zatin nan na sar-

 Ki gobe domin Annabinmu Muhammada.

50. Tarshe mu ko Sarki da shehohimmu duk,

 Hakana uwaye don Fiyayye, Ahmada.

51. Tarshe mu tare da Shehu Abdulƙadiri,

 Mai kai mu gobe ga Annabimmu Muhammada.

52. Mun gode Allah nan fa waƙa ta cika,

 Allah shi karɓa don Fiyayye Ahmada.

53. Allah shi dawwama assalatu da sallama,

 Bisa Al-Rasulu da yaf fi kowa, Ahmada.

54. Na sallama Alai haka duk,

 Har Tabi’ina da Tabi’ina Muhammada.

55. Ramzi na Hijira tai Fiyayye rushdana,

 Allah shi ba mu shiri ga sunna (r) Ahmada.

Post a Comment

0 Comments