Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙar Furojet
Ita ma wannan waƙar mawaƙin ya yi wa ma’aikatar gona ne, ba wani mutum guda ba. Don
haka a cikin waƙar yake sheƙe ayarsa a kan fa’idojin wannan
ma’aikatar ga al’umma. Ga waƙar
kamar haka:
G/Waƙa: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
‘Y/ Amshi: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Waldiban ki kama mana.
‘Y/ Amshi: Kin gani shekara ta barkace.
Jagora: Uwam marar uwa.
‘Y/ Amshi: Mun gode furojet mutanen arziki.
Jagora: Su ka raya manoma.x2
‘Y/ Amshi: Su miƙe ƙahwahu ko’ina.x2
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Allah shi taimaki waldiban,x2
‘Y/ Amshi: Da sa’a don Rabbana,x2
Jagora: Garin da babu walda.
‘Y/ Amshi: Ai sai ku ƙyale
shi,
: Babban ƙauye ne.
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Waldiban ki kama mana.
‘Y/ Amshi: Kin gani shekara ta barkace.
Jagora: Uwam marar uwa.
‘Y/ Amshi: Mun gode furojet,
: Mutanen arziki.
Jagora: Su ka raya manoma.x2
‘Y/ Amshi: Su miƙe ƙahwahu ko’ina.x2
Jagora: Akwai gero waldiban.
‘Y/ Amshi: Don manoma tas saye..
Jagora: Akwai dawa waldiban.
‘Y/ Amshi: Don manoma tas saye.
Jagora: Da shinkahwa waldiban.
‘Y/ Amshi: Don manoma tas saye.
Jagora: Akwai sukari waldiban.
‘Y/ Amshi: Don manoma tas saye.
Jagora: Akwai masara waldiban.
‘Y/ Amshi: Don manoma tas saye.
Jagora: Had da kaji hwarhwaru.x2
‘Y/
Amshi: Don manoma tas saye.x2
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Waldiban ki kama mana.
‘Y/ Amshi: Kin gani shekara ta barkace.
Jagora: Ta yanka godabbu ko’ina.
‘Y/ Amshi: Don manoma anka yi.
Jagora: Ta gina dam na ruwa Gusau,
‘Y/ Amshi: Don manoma anka yi.
Jagora: Da mu da dabbobi mu sha,
‘Y/ Amshi: Don manoma anka yi.
Jagora: Ta gina ɗakin magani.
‘Y/ Amshi: Don manoma anka yi.
Jagora: Sun gina ɗakin
magani.
‘Y/ Amshi: Don manoma sunka yi.
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Waldiban ki kama mana.
‘Y/ Amshi: Kin gani shekara ta barkace.
Jagora: Dag Gusau sai Huntuwa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Ƙarmanje suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Ta kama Daudawa ta wuce.
‘Y/
Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Maska suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Cana Sheme da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan ‘Yankara na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Nan Kuceri da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Bilbil na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Magazu suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Ta kama Tcahe ta wuce.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: ‘Yandoton Daji suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Mada suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Ta kama Samawa ta wuce.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Tohwa suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Dashi suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Kwatarkwasawa murna sukai.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Riɓe suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Sankalawa murna takai.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Kura suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Ƙarazau na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Mutan Damɓa na hwaɗi.
‘Y/
Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Wanke na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Mutan Hurhuri na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Bunguɗawa murna sukai.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Rawayya da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Dogon kaɗe na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Cana Bela da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Kasuwad daji na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Modomawa na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Kyambarawa murna sukai.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Nahuce da tar riƙa.
‘Y/
Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Karakkawa murna sukai.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Kurya suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Sakajiki murna sukai.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Ta kama Ƙaura
ta wuce.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Gabake da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Birnin magaji suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Cana Zurmi da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Dauran na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Dumfawa na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Cana Moriki ta riƙa.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Kwangwami na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Dole suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Ciki suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Shinkahi da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Bahwarawa murna sukai.
‘Y/
Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Isa suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Gatawa na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Sabonbirni.
‘Y/ Amshi: Hwaɗi sukai an yo kanhwani.
Jagora: Anguwal lalle na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Tsamaye na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Nan Gwaranyo da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Gwadabawa na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Tangaza na hwaɗi.
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.
Jagora: Illela da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Kamba suna hwaɗi.x2
‘Y/ Amshi: An yi babban kanhwani.x2
Jagora: Cana Bunza da tar riƙa.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Kalgo suna hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Waɗan Jega suna hwaɗi.
‘Y/
Amshi: Ta yi babban kanhwani.
Jagora: Garin da babu walda.
‘Y/ Amshi: Ai sai ku ƙyale
shi babban ƙauye na.
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Waldibankin duniya,
: Mun yi alƙawali da ke.x2
‘Y/ Amshi: Da dut niz zaka waƙa,
: Mota kikai man sai ki ban.x2
Jagora: Gata nan ta riƙa anka.
‘Y/ Amshi: Ko alƙawal ya walwale?
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: In babu kyauta waldiban.
‘Y/ Amshi: Ba ni bashi sai baɗi.
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Mu gode mallan Adamu.x2
‘Y/ Amshi: Abu mai kiɗi ya taimaka.x2
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
Jagora: Godiya Ladan Gilbaɗi.x2
‘Y/ Amshi: Ya riƙa ya taimaka.x2
Jagora: Mu gode mallan Isah.x2
‘Y/ Amshi: Abu mai kiɗi ya taimaka.x2
Jagora: Shi Nafaru na gode.
‘Y/ Amshi: Ya yi man taimaka ya agaza.
Jagora: Isa direba na gode.
‘Y/ Amshi: Ya yi man taimaka ya agaza.
Jagora: Isah direba ya kyauta.
‘Y/ Amshi: Ya yi man taimaka ya agaza.
Jagora: Sani Maru na gode.x2
‘Y/ Amshi: Ya yi man taimaka ya agaza.x2
Jagora: Allah ya taimaki waldiban.
‘Y/
Amshi: Da sa’a don Rabbana.
Jagora: Godiya Audu wakili.
‘Y/ Amshi: Hairan yakai ya taimaka.
Jagora: Audu Yabo na gode.
‘Y/ Amshi: Ya yi man taimaka ya agaza.
Jagora: Godiya Alhaji Shehu.
‘Y/ Amshi: Hairan yakai ya agaza.
Jagora: Sarkin noman Tambuwal ina gode mai.
‘Y/ Amshi: Abu mai kiɗi ya taimaka.
Jagora: Godiya Kaka magaji.2
‘Y/ Amshi: Hairan yakai ya taimaka.x2
Jagora: Alhaji Muhammadu Maje.
‘Y/ Amshi: Abu mai kiɗi ya taimaka.
Jagora: Waldiban ki kama mana.
‘Y/ Amshi: Kin gani shekara ta barkace.
Jagora: Uwam maras uwa.
‘Y/ Amshi: Mun gode furojet,
: Mutanen arziki.
: Waldi bankin duniya,
: Furojet ita at tsaye.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.