Ticker

6/recent/ticker-posts

Samari Yanga Fama

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Samari Yanga[1] Fama

Mawaƙin wato Alhaji Abu Ɗankurma Maru yana waƙe wata ƙungiyar manoma ce wadda ake kira “Samari Young Famers”. Yana yaba yadda take tafiyar da aikinta na haɓaka noma. Ƙungiyar ce gabaɗaya ya yi wa waƙar ba mutun guda ba, idan ka ji ya anbaci sunan wani to yaba kyauta ne, wanda Hausawa ke ce wa Tukuici. Ga yadda waƙar tasa take kamar haka:

 

G/Waƙa: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga[2] fama.

 

Jagora: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

‘Y/ Amshi: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

 

Jagora: Ga noma arzikin ƙasa.x2

‘Y/ Amshi: Yanke talauci noma,

: Muna zwaci da aikin,x2

 

Jagora: Ana sa taki na zamani,

: Gun gero da dawa.x2

‘Y/ Amshi: Balle wanda ad da gujiya,

: Shi ad da riba.x2

 

Jagora: Waken soya yana da daɗI,

: Daidai da daida,

‘Y/ Amshi: Wannan mun ga ranas shi,

: Samo wani mu ƙara.

 

Jagora: Maganin ƙwari na da martaba,

: Ya hana tone shikka,

‘Y/ Amshi: Wannan mun ga ranas shi,

: Samo wani mu ƙara,

 

Jagora: Akwai gamelan en ka maganin,

: Kimshen[3] ɓoye tsaba.

‘Y/ Amshi: Wannan mun ga ranas shi,

: Samo wani mu ƙara.

 

Jagora: Irin gujiyag ga kehhifti[4],

: Kin  ba ni shawa.

‘Y/ Amshi: Wannan mun ga ranat ta,

: Samo wata mu ƙara.

 

Jagora: Ga tozo  ba ni cin daɓiri,

: Mi ad dalili?x2

‘Y/ Amshi: In ga kehifti na gani,

: Ba ni sayen Bahausa.x2

 

Jagora: Ke kehifti ke riga ke bambanta,

: Gun duk irin gujiyad da an nan.

‘Y/ Amshi: Ke hi tsawon gaɓa,

: Ke hi ƙwayu manya-manya.

: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

 

Jagora: Ko da Esikisti[5] wannan sabon irin.x2

‘Y/ Amshi: Wannan sabon irin gyaɗa na ƙwarai,

: Wanda ad da gona,

: Ya taho ya shikka.x2

 

Jagora: Mai gona shi ka korab biri .

‘Y/ Amshi: Duk anka zo bayani,

: Sai an biɗe ka.

Jagora: Dr. malam Aliyu Attah,

: Babban sakartare,

 ‘Y/ Amshi: Babu guda kamak ka.

 

Jagora: Ko can kayan amali sun hi na goga[6].

‘Y/ Amshi: Ka dakata jakki babu hali.

 

Jagora: Ga Ummaru Sanda E.O,

: Sa’a tai mun wadata.

‘Y/ Amshi: E.O sa’a tai mun wadata,

 

Jagora: Ko can Tsari da Ɗan kada,

: Ba ɗai ne ba,

: Diba kurun mi sunka tara?

‘Y/ Amshi: Muhammadu Augi ko dori,

: Bai wargi da aiki.

 

Jagora: Aiki gaba yau samari,

: Mun cim ma sa’a,

‘Y/ Amshi: Adamu Wara ya hau halifar Augi,

: Murna mukai,

: Girma ya ƙara.

 

Jagora: Jama’iyyar Yanga fama[7],

: Shin wa a Ubanta?

: Mani tambaya nikai,

: Nuna man Ubanta?

‘Y/ Amshi: Malan Audu Ingaski na,

: Shi a ubanta.

 

Jagora: Allah ya taimaki Audu Ingaski. 

‘Y/ Amshi: Audu Ingaski mai komi ga Allah.

Jagora: Ga mallan Audu Ingaski,

: Ga Isah da Mamman,

‘Y/ Amshi: Ga Adamu Wara mun kammale,

: Sai hamdalewa.

 

Jagora: Birnin Ingaski gaskiya take,

: Hili miraran.

‘Y/ Amshi: Can kura ka kama akuya,

: Ta mayat ta ɗaure,

: Don halin yakamata.

: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

 

Jagora: Allah sarki ya gyara,

‘Y/ Amshi: Ya gyara kada maƙiya su dara.

 

Jagora: Malan Muhammadu Bagudo,

‘Y/ Amshi: Yana halin yakamata.

: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

 

Jagora: Tukur Ilo.

‘Y/ Amshi: Wannan muna gaisai da aiki.

: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

 

Jagora: GodiyaTukur Ilo dattijo.

‘Y/ Amshi: Tukur Ilo dattijo,

: Wannan muna gaisai da aiki.

: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

 

Jagora: Malan Ummaru Hasaan.

‘Y/ Amshi: Hwaɗa mai muna,

: Gaisai da aiki,

: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.

 

Jagora: Godiya Sule Bawa.

‘Y/ Amshi: Hwaɗa mai muna,

: Gaisai da aiki.

 

Jagora: Isa Moriki na gode,

‘Y/ Amshi: Ya yi man bajinta,

: Girma ya ƙara.

 

Jagora: Mamman Nakwada.

‘Y/ Amshi: Ya yi man bajinta,

: Girma ya ƙara.

 

Jagora: Alhaji Isah Abdullahi. 

‘Y/ Amshi: Yana halin yakamata.

 

Jagora: Ga Noma arzikin ƙasa,

‘Y/ Amshi: Yanke talauci noma,

: Muna zwaci[8] da aikin.

 

Jagora: Garba Dauran na gode.

‘Y/ Amshi: Yai man bajinta,

: Girma ya ƙara.

 

Jagora: Ibrahima Dauran na gode.

‘Y/ Amshi: Ya yi man bajinta,

: Girma ya ƙara,

 

Jagora: Ai ga kura da shan bugu,

: Gardi da ƙwace samu.

: Su wane ka shan wuya,

: Wajen aikin Yanga famas.

‘Y/ Amshi: Su wane ana gida,

: Sai ana hwama da wanki.

 

Jagora: A wankekke a goge.

‘Y/ Amshi: Anai muna gaye-gaye.

 

Jagora: Su burgu su ka sata,

: Irin gujiya su ɓoye.

‘Y/ Amshi: Sai in an jima sai a ce,

: Kusa ka iba.

 

Jagora: Muna zaton gahiya ita ɗai ka sata.

‘Y/ Amshi: Ba ita ɗai ba ta,

: Jaɓa na nan had da kusu.

 

Jagora: Jama’iyya Yanga famas,

: Jam’iyyar arziki ta.

‘Y/ Amshi: Kowa kag gani ciki,

: Baya zama da raga.

 

Jagora: Suna iya ba ka bashin,

: Irin gujiya ku shibka.

: Sai an kai ga kaka,

:Mun kai gun namu zak kyau.

‘Y/ Amshi: Sannan mu biya ta zak kyau.

 

Jagora: Ai ga shanu na noma,

: Kuma ga shanu na twatsa.

‘Y/ Amshi: Komi munka so,

: Ga jam’iyya sai ɗai ta bamu.

 

Jagora: Mai sukay yanga famas.

‘Y/ Amshi: Allahu ya ƙaddara,

: A bashi takardad dumoshin.

 

Jagora: A yi yamma da shawaraki.

‘Y/ Amshi: A sa shi cikin ɗagera.

 

  Jagora: Kowa nas soki ‘yan kulob.x2

 ‘Y/ Amshi: Allat tuskuna[9] shi,

: Had da bisashe su ƙi shi.x2

 

Jagora: Direban gona Charanche.

‘Y/ Amshi: Kai ka gudu babu shakka.

 

Jagora: Charance canza giya.

‘Y/ Amshi: Yanzu ko akwai,

: Mai ja ma ya hwasa.

 

Jagora: Ai da gulbin Bakura,

: An ce muna baya takuwa.

‘Y/ Amshi: Ran nan sai Charanche,

: Yac canza munka take.

 

Jagora: Mai tsoro baya suna.

‘Y/ Amshi: Bai gajiya ko kaɗanna.

 

Jagora: Garba mai shaƙe,

‘Y/ Amshi: Ya hi iska gudu,

: Na tabbata yau.

 

Jagora: Waɗan Kanji hwaɗin sukai,

: Garba aljannu garai.

‘Y/ Amshi: Waɗan Wawa hwaɗin sukai,

: Guguwa ta hwara tashi.

 

Jagora: To haka nis san ana gudu.

‘Y/ Amshi: Ba a shigo gari da mata ba,

: A sake canji ana watci da danja.

 

Jagora: Ga Charabahe ga,

: Yakubu ga Abubakar Shaƙe,

‘Y/ Amshi: Waɗanga dud da iska,

: Ya san akwai su.

 

Jagora: In dai mota tana hawa sama.

‘Y/ Amshi: Ka san muna hawa bisa ko babu canji.

 

Jagora: Godiya nikai Daudawa.

‘Y/ Amshi: Hwaɗa mai muna gaisai da aiki.

 

Jagora: Mani Kwatarkwashi na gode.x2

‘Y/ Amshi: Hwaɗa mai muna gaisai da aiki.x2

: Tana shiryad da aikinta,

: Daidai babu kissa,

: Jama’iyyam manoma,

: Samari yanga fama.



[1]  Kalmar Turanci ce ya Hausance “Young fermers”

[2]  Kalmar Turanci ce makaɗin ya Hausantar wato young.

[3]  Adana amfanin gona a cikin rumbu, ana kwance damman gero ko dawa a tsara su a cikin rumbu, ko a zazzage wake ko gyaɗa da sauran duka abinda ake son a kimshe.

[4]  Wani iri ne na gyaɗa K.50.

[5]  E.60 shi ma wani nau’in irin gyaɗa ne.

[6]  Bajimin sa.

[7]  Wanna Turanci ne ya faɗa a Hausance wato “Young farmers”

[8]  Murna/shauƙi.

[9]  Wulakantawa/sa baƙin jinni.

Post a Comment

0 Comments