Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Ba’u

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙar Ba’u

Bismillahi Allah na roƙe ka,

Ina bara ka san da nufata.

Ka taimake ni ka bani bayanin.

Sanin Muhammadu in yi yabo nai,

Ga haihuwa tai Manzon Allah,

Ƙaunar uwatai ta yi yabo nai.

Aminatu ita ta haife shi,

Halimatu ita ta yi yabo nai.

Halimatu ta yi reno mai kyawo,

 Tay yi arziki domin yabo nai.

Tubarakallah wanga maraya,

 Tana daɗawa al’ajabinai.

Inda na san bani da ilmi,

 Da na yi wauta gun bege nai.

Na gode Allah na yi salati,

 Ga Sidi Manzo Almuhtari.

Kai an na farko tun ga halitta,

Ga Annabawa babu kamatai.

 Yabon Muhammadu ya wajabta,

 Ɗiya Musulmi mui ta yabonai.

 Kai ad da suna hairun haƙƙun,

 Maza da mata mui ta yabonai.

 Komih hi lada ci da maraya,

 Riƙon gida bai zan laifi ba.

 Mai ci da maraya ko miskini,

 Ka ce da wannan albishirinai.

 Ci da uwaye ya wajabta,

 In babu kyauta ai masu ranko.

 Haƙƙin uwaye haƙƙin Allah,

 Sai an rage aka samun tsira.

 Duk wanda Allah ya yi wa ɗa’a,

 Ba za ya rena uwa da uba ba.

 Mai son zumunci ya so Allah,

 Allah ka gyaran al’amarinai.

 Mai gaskiya na tare da Allah,

 Kowaf faɗe ta a ba shi abutai.

 Ba rikici addini Allah,

 Halinmu ne shi kan rikita mu.

 Koway yi noma bai zakka ba,

 Ko ya yi sallah ba ta da lada.

 Abinda duk Allah yab baka,

 Saboda Allah ɗebi ka bayar.

 Duniya matar zakka ce,

 Shigo-shigo taka yi ba zurhi.

 Waɗansu na tsoron su shige ta,

 Waɗansu sun ɗaura mata aure.

 Sun yi gida sun gina sumunti,

 Wurin rabo a rabar ba daɗi.

 Koway yi talauci yas saki hanya,

 Ku ce ma wannan ba shi da komi.

Post a Comment

0 Comments