Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Ƙazama

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙar Ƙazama

 Jagora : To bismillah Rabbana

 Amshi : To

 Jagora : Arrahamani Rabbana ya Ta’ala

 Amshi : To

 Jagora : Zam ma kashedi ba ni auren ƙazama

 Amshi : To

 Jagora : Da duk tab bani goma ‘ya’yanta goma

 Amshi : To

 Jagora : Kowace sahiya tana zana suna

 Amshi : To

 Jagora : In ko ka ƙiya shari’a ta kam ma

 Amshi : To

 Jagora : Akwai wani ɗan zane shina nan gare ta

 Amshi : To

 Jagora : Ba shi zuwa buki ba shi sallah

 Amshi : To

 Jagora : Ba shi zuwa ganin uwaye da rana

 Amshi : To

 Jagora : In ta haifi yan ɗiya wa ka ɗauka

 Amshi : To

 Jagora : Dag ga mijinta sai uwayenta mata

 Amshi : To

 Jagora : Kanta kwakwal-kwakwal kawat babu gashi

 Amshi : To

 Jagora : Ko gwiwar amali ta ja da baya.

 Amshi : To


Post a Comment

0 Comments