Ticker

6/recent/ticker-posts

Baka

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Baka

Jagora : Assalamu alaikum masu gida muna muku sallama,

Amshi : Baka.

Jagora: Muna muku sallama don ɗai ku ba mu na Annabi,

Amshi: Baka.

 Jagora: Sai zuciya ta daure in zuciya ta dangana,

Amshi: Baka.

Jagora: In bata dangana ba ilmi ya fi ta ya dangana,

Amshi: Baka.

Jagora: Inna uwata ce daga duniya hal lahira,

Amshi: Baka.

Jagora: Baba ubana ne daga duniya hal lahira,

Amshi: Baka.

Jagora: Bara a gidan malam daɗi gare shi kamar zuma,

Amshi: Baka.

Jagora: Wani na tuƙin mota ya bar ta ya tahi lahira,

Amshi: Baka.

Jagora: Wani na tuƙin jirgi ya bar shi ya tahi lahira,

Amshi: Baka.

Jagora: Wani na da gidan sama ya bar shi ya tahi lahira,

Amshi: Baka.

Jagora: Wani na da gidan ƙasa ya bar shi ya tahi lahira,

Amshi: Baka.

Jagora: Baka bakariya baka da manyan kunnuwa,

Amshi: Baka.


Post a Comment

0 Comments