Ticker

6/recent/ticker-posts

La la la la Duniya

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

La la la la Duniya

 Jagora: La la la la Duniya

 Amshi: To

 Jagora: Inda masoyi ya mutu

 Amshi: To

 Jagora: In ɗebi ruwa ga buta

 Amshi: To

 Jagora: In bi rana in bi farin wata

 Amshi: To

 Jagora: Suna suna na sani

 Amshi: To

 Jagora: Wanda malam ya ce in faɗi

 Amshi: To

 Jagora: Ni kuma nicce ban faɗi

 Amshi: To

 Jagora: Amma yanzu faɗi nikai

 Amshi: To

 Jagora: Tun da ban iya kwana ban ci ba

 Amshi: To

 Jagora: Sunan dambu maƙura

 Amshi: To

 Jagora: In babu ruwa ɓanna yakai

 Amshi: To

 Jagora: Sunan kwaɗɗo Macciɗo

 Amshi: To

 Jagora: Su Macciɗo sai sanyin ɗuwai

 Amshi: To

 Jagora: Sunan zaure Babuga

 Amshi: To

 Jagora: Sunan tantabara Kulu

 Amshi: To

 Jagora: Sunan hankaka Ige

 Amshi: To

 Jagora: Sunan hanya Lailatu

 Amshi: To

 Jagora: Sunan luddai Ummaru

 Amshi: To

 Jagora: Su Ummaru ɗebo tsaki akai

 Amshi: To

 Jagora: Sunan randa Maimuna

 Amshi: To

 Jagora: Su Maimuna sai ƙaton ciki

 Amshi: To

 Jagora: Sunan mota Gargaɗa

 Amshi: To

 Jagora: A gargaɗa kaya sai Kano

 Amshi: To

 Jagora: Sunan hanwawa Ige

 Amshi: To

 Jagora: Sunan maciji Awwalu

 Amshi: To

 Jagora: Su Awwalu ga kyau ga faɗa

 Amshi: To

 Jagora: Sunan jirgi Sumbuƙa

 Amshi: To

 Jagora: Su sumbuƙa ga tashi sama

 Amshi: To

 Jagora: Tuwon masara Malam Hassan

 Amshi: To

 Jagora: A gama shi da sure Alhaji.

 Amshi: To


Post a Comment

0 Comments