Ticker

6/recent/ticker-posts

Wa Dr. Mamman Shata ya fi yi wa waƙa?

Shata, Sarkin Daura Bashar, Alhaji Adamu Dankabo Da Bello Maitama Yusuf

An jima ana kai ruwa rana tsakanin masoya da masana waƙoƙin Shata a kan wa Shata yafi yiwa waka a tsakanin mutanen nan da a ka ambata a sama.

Wasu masanan da masoyan sun tsaya kai da fata cewa Shatan yafi yiwa babban basaraken sa kuma maigidan shi Alhaji Muhammad Bashar marigayi Sarkin Daura waka. Idan a ka kalli wannan raayi na su ta wata fuskar sai a ce suna da gaskiya, domin banjin akwai mutum daya da Shata yayiwa waka kuma ya rinka maimaita waƙoƙin sa a duk inda yayi wasa ko waka kamar Sarkin Daurar. Domin wani masani a kan waƙoƙin Shata ya gaya min cewa Shata ya maimaita Kwana Lafiya da Lafiya Zaki sau kusan dubu-dubu. Hakazalika wannan masanin dai yace min Shatan yayi kuma ya maimaita wakar Bello Maitama mai amshi Mai Shata Na Yelwa ya gode Bello Maitama itama kusan sau dubu.

Amma abin da na sani kuma na kididdige da kai na shine a duk fadin sararin duniyar nan ba mutum daya da Shata yayiwa waƙoƙi masu amshi daban-daban kamar Bello Maitama. Domin nasan waƙoƙin shi masu amshi daban-daban sunfi Sittin (60).

Amma waƙoƙin da Shata yayiwa Sarkin Daura Bashar da Alhaji Adamu Dankabo masu amshi daban-daban basu wuce Sha Biyar -Biyar (15) ba.

To don in tabbatar muku Dodo yafi yiwa BELLO MAITAMA waka masu amshi daban-daban zan kawo muku amshin waƙoƙi kamar *41 da Shatan yayiwa Bello Maitama.

Sannan kuma zan kawo waƙoƙi Sha Biyu (12) da Shatan yayiwa Sarkin Daura Bashar in kuma karkare da amshin waƙoƙi Sha Daya (11) da Shatan yayiwa Alhaji Adamu Dankabo

Wanda yasan amshin wata wakar daya daga cikin wadannan iyayen gidan Shatan da ban sako ba sai ya taimaka ya sako mana.

Waƙoƙin Bello Maitama

1. Haji Maitama Baban Maijidda

2. Dan Isuhu Maitama Bello

3, Zakin Gaba Kanin Baffane

4. Nagodewa Minista Bello

5. Zakin Mutane Dan Isuhu

6. Nagodewa Lauya Bello

7. Bello Kanin Malam Baffa

8. Haji Maitama Bello Danuwan Ali

9. Mamman yagode Bello

10. Nagode Sardauna Bello

11. Nagode Sardaunan Dutse

12. Bakandamiyar Bello

13. Alhaji Sardauna Bello Dan Namijin Duniya

14. Alhaji Sardauna Maitama ka gama Lafiya

15. Bello Jan Zakin Ali

16. Bello Karon Badar Uban Maijidda Kanin Ali

17. Bello Zakin Mutane Dan Isuhu

18. Bello Maitama Kanin Baffane

19. Bello Maitama Uban Maijidda

20. Bello Uban Maijidda Dan Isuhu

21. Ga Bello Sardaunan Dutse

22. Haji Sardaunan Kano Bello

23. Maitama Bello Maganin abu Allah Kanen Ali

24. Mai Shata na Yelwa Yagode Bello Maitama

25. Mutumin Kirki Bello Maitama

26. Maitama Mamman Bello

27. Maitama Bello Uban Maijidda

28. Maitama Babban Bako na Baffa Ikon Allah

29. Nagode Haji Maitama Bello

30. Zani Gwaram Albarkar Bello

31. Bello Sardauna Zakin Mutan Dutse

32. Nagode Maitama Bello

33. Zaki Maitama Bello

34. Maitama Nagode Bello

35. Maitama Bawan Allah Bello

36. Maje Haji Shata za shi Gwaram

37. Nagode Sardauna Maitama

38. Sardauna Bello Jan Zakin Gwaram

39. Sosai ne Na Yelwa Alhaji Mamman Kanin Ali

40. Rai yadade Sardauna Maitama

41. Nagode Sardaunan Gwaram

Waƙoƙin Sarkin Daura Bashar

 1. Nagodewa Bashar dan Musa Mamman mai mulkin Daurawa;

2. Dan Leko Baban Leko;

3. Dan Dattijo Bashar dan Umaru;

4. Kwana Lafiya mai Daura jikan Abdu gwauron giwa;

5. Lafiya zaki Mamman Baban Galadima Danmusa;

6. Mamman mai Daura na mai Daki;

 7. Mai Daura Bashar dan Sanda;

 8. Muje Daura mu gaida Bashar;

 9. Sadauki Shehu Magajin Mamman (Bashar yana Wanban Daura);

 10. Mamman jikan Abdu (yana Hakimin Baure):

11. Yara Muje Daura Garin Bashar

12. Malam Maihoro na Waziri

 Waƙoƙin Dankabo

 1. Bakandamiyar Dankabo;

2. Na Kabo Jarmai Mamman;

 3. Dafta Mamman Dankabo;

 4. Dankabo Jarmai Mamman;

 5. Jarman Kano Galadiman Panshin;

 6. Jarman Kano Mamman Dankabo;

7. Mai jirgi Mamman Dankabo;

 8. Nagode wa Dankabo Mamman;

 9. Nagode Jarman Kano Mamman;

 10. Sannu Turakin Panshin Mamman;

11. Haji Mamman Sardaunan Kagoro

 www.amsoshi.com

Rubutawa:

Barrister Suleh Umar

Hussaini Dogo

Sarkin Yaƙi

Post a Comment

0 Comments