Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakokin Noma Na Bako Rugum Kiri

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙoƙin Noma Na Baƙo Rugum Ƙiri

Baƙo Rugum makaɗin noma ne wanda yake amfani da gangar noma wato irin wannan da ake kira ta guiwa ko tallabe. Kuma ‘yan amshinsa mata ne matansa ne na aure su uku suke tafiya tare da shi suna yi masa amshin.

Taƙaitaccen Tarihin Rayuwarsa

An haife shi a shekarar 1873 ne a garin Gada Ƙiri ta jihar Sakkwato. Sunansa na yanka shi ne Salihu, ya gaji kiɗan ne daga mahaifinsa wanda sunansu ɗaya da shi wato Salihu wanda yake makaɗin yaƙi ne daga baya ya koma yana kiɗin fatake. Mahaifiyarsa kuwa sunanta Inno, ’yar asalin garin Gada Ƙiri ce. Matan aurensa uku ne da Haddi da Maimuna da ‘Yat tunga. Bayan ‘yan amshinsa wato matansa akwai wasu maza su biyar masu yi masa kiɗi a lokacin da yake waƙoƙinsa, su ne Ummaru da Mamman Ɗanhulai da Audu da Jabba da kuma Roro. Babu wata waƙa da yake yi daban in banda waƙoƙin noma.

Ya rasu yana da shekara ɗari da talatin da huɗu a shekara ta dubu biyu da bakwai (2007), yana da shekara goma sha shida da rasuwa kenan a yanzu (2023).

Post a Comment

0 Comments