1. Ƙarya ba ta sa amarya lalle.

lalle
2. Faďi ke matar aure ni saďaka in na faďi gida nika kwana.
3. Mai son ďan Ƙwarai, ya auri isassa.
4. Barewa ba ta gudu ďanta ya yi rarrafe.

barewa
5. Larura auren namiji da ‘ya’ya
6. Arahar banza auren bashi, in an haihu a biya
7. Aure ba ka da malam
8. Ƙoshin takaba aure da mai Ƙararren kwana
9. Larura, auren namiji da ‘ya’ya
10. Abin da ke ga amarya shi take ba ango
11. Komai wayon amarya sai an sha manta
12. Kurum baka, amarya ta ci ďan masu gida
13. Kwana nawa ne? maye ya yi amarya
14. Jin dadin aure, har da ce wa miji baba
15. Izgili, angaye bakin rijiya
16. Na gaji, mai hana wa mata lada
17. Abin ya ci matar lifidda
18. Matar in tashi, ba ta Ƙosar da mijinta
19. Dace da masoyi, riba
20. Son maso wani Ƙoshin wahala
21. Ba haka aka so ba, Ƙanin miji ya fi miji kyau
22. Matar na-gode, ba ta rasa mijin aure
23. Mai zanin gamin baki, ba ta wa miji yanga
24. Ban faye musu ba, an ce da bazaura ta hau gado
25. Daki-bari turmin gidan miji
26. Ƙarya ba ta sa amarya lalle
27. Kilin kiso da balanƘwalma, kiran miji da akaifa
28. Faďi ke matar aure, ni saďaka in na faďi gida naka kwana

 

karanta wasu

https://www.amsoshi.com/2017/07/04/karin-magana-game-da-mutuwa/