Ticker

6/recent/ticker-posts

Tattaunawar Ilimi Tsakanin Dr. Adamu Rabi'u Bakura Da Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji Da Malam Adamu

*****

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji

Mai Ƙaura /Sarkin Kiyawa Ummaru Ɗan Sarkin Kiyawa Mamuda kenan. Shi ne ake kira  Ummarun Mamuda. Shi kuma Sarkin Kiyawa Mamuda Ƙanen Muhammadu Namoda ne wanda ya ƙirƙiri Ƙaura Namoda kuma Sarkin ta na farko. Mamuda ne ya gade /gaje shi kuma daga gare shi ne laƙabin Sarautar ya canza/canja daga Sarkin Yaƙi zuwa Sarkin Kiyawa da ake amfani dashi ya zuwa yau.

"Jitaun Mai Ƙaura" kenan ya danganta wanda ya yi wa Waƙar da Kakanshi ne. Jitau wata siffa ce ta jicewa/jice wani abu da aka fi ƙarfin sa har ma ana iya samar da rauni ko rasa rayuwa ta wannan hanyar. Shi ne ma dalilin da yasa ake yi wa wata halitta da ke cikin ruwa mai al'adar jice/jicce duk wani wata halittar da ba irin ta ba ce ba, kamar Ɗan Adam ko wata dabba a cikin ruwa idan tsautsayin hakan ya samu inkiya da "Jitakukku".

Sarkin Kiyawa Mamuda ne ya ɗauko fansar kisan da aka yi wa yayan sa /wan sa Sarkin Yaƙi Malam Muhammadu Namoda wanda ya ƙirƙiri Ƙaura Namoda a shekarar 1807 a hannun Zamfarawan Kiyawa(Kiyawa a halin yanzu ta na cikin Masarautar Birnin Magaji ta Jihar Zamfara) a wani Ƙauye da ake kira Bukut ya na Sallar Asr daga umurnin Sarkin Kiyawa Dagazau Na Ma'inna. Malam Mamuda ne ya kashe Sarkin Kiyawa Dagazau Na Ma'inna a matsayin fansar kisan Ɗan Uwan na sa, Sarkin Yaƙi Muhammadu Namoda wanda Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya baiwa Tutar Jihadin jaddada addinin musulunci ta Daular Usmaniya. A lokacin da ya kashe Sarkin Kiyawa Dagazau Na Ma'inna, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio da jama'ar sa suna zaman Ribaɗi a garin Ƙauran Namoda. Da Malam Mamuda ya zo da kan Sarkin Kiyawa Dagazau a tsire ne Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya tambaya cewa me ne ne laƙabin Sarautar Kiyawa inda Dagazau ke mulki aka ce masa 'Sarkin Kiyawa' sai ya naɗa Malam Mamuda a matsayin Sarkin Ƙaura Namoda na biyu da laƙabin "Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda".

Sarkin Kiyawa Ummaru Mamuda ne sanadiyar kiran duk wani mai suna Ummaru /Umaru /Umar /Sanda a yankin Ƙaura Namoda da laƙabin "Mai Ƙaura".

*****

Dr. Adamu Rabi'u Bakura

A'a lamarin ba haka yake ba a tarihance. Wannan ya faru ne sakamakon rasuwar Sarkin Musulmi Umaru (1881 - 1891) wanda ya rasu a Ƙaura Namoda, kuma aka rufe shi a can. Wato Ƙaura ta kasance garinsa na dindindin. Don haka, duk mai suna Umaru, saboda alkunyar Hausa ta ambaton sunan yanka na shugabansu, sai aka dinga kiran mai sunan da Maiƙaura. Wannan ya faru bayan wafatinsa a 1891. Allah ya sa mu dace. Amin.

*****

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji

Wafatin sa a Ƙaura Namoda ne dalilin yi wa Abdulrahaman Ɗan Atiku mubayi'a a matsayin sabon Sarkin Musulmi anan garin Ƙaura Namoda a shekarar 1891. Allah ya kyauta makwanci, amin.

*****

Dr. Adamu Rabi'u Bakura

Kamar yadda masana tarihin suka bayyana, a daidai lokacin da Allah ya karɓi rayuwarsa babu wani wanda ya cancanta a yi wa mubaya'a da ke kusa, sai Abdurrahman da ke zaune a ƙauyen nan da ake kira Unguwar Sarkin Musulmi. Saboda haka ne suka yi yarjejeniya a tsakaninsu a bisa sharaɗin zai naɗa shi Sarkin Musulmi, amma duk abin da ya aikata kada ya ce masa uffan. A kan haka ne ya zama Sarkin Musulmi na goma sha ɗaya. Kamar yadda kuka ambata ne ya kumbo ya kayanta. An yi masa laƙabi da ɗanyan kasko ne, saboda bai yafe wa duk wanda ya yi masa laifi ba a lokacin da yake ɗan sarki. Domin da ya hau karagar sai da ya ɗauki fansa a kansu. Misali, ya yi turken doki da wani hakimin ƙasar Ɓurmi, wato Damrin Damri, saboda kawai ya ƙi bayar da umurnin a buɗe masa ƙofar garin Damri wanda hakan ya sa ya kwana a bayan gari, sai da gari ya waye Sarkin Ƙofa ya buɗe masa kamar yadda dokar lokacin ta shata. Yayin da suka gamu, sai ya ce masa ka nuna mini kai ke da ikon gari. 

A sakamakon wasan Fulani da Barebari, sai Damrin Damri ya ce, bari in ka zama Sarkin Musulmi ka yi turken doki da ni. Yayin da ya zama, sai Damrin Damri ya je waje mubaya'a, a lokacin ya bayar da umurnin a yi turken doki da shi. Haka kuwa aka yi, aka ɗaure doki a wuyansa. Kuma shi ne silar waƙin basasar da ya auku a Kano tsakanin Tukurawa da Yusufawa. Wannan yaƙin an yi masa laƙabi da " yaƙin basasa" ne saboda lissafin alƙalumman shekarar yaƙin ne suka bayar da 'BASASA'. Kuma shi ya sa duk wani yaƙin cikin gida da ya auku ake masa laƙabi da yaƙin basasa. Ƙarin bayani sai a duba "Kano Ta Dabo" na Abubakar Dokaji, da kuma "Mu San Kanmu" na Alƙali Husaini Sufi. Idan aka duba littafin nan mai suna "Tatsuniyoyin Hausa" na Edigar za a ga bayanin da Baturen ya kawo game da su dangane da yadda suka rinƙa yi wa talakawansu kisan gilla ba laifin zaune ba na tsaye. Allah ya arzuta mu da cikawa da imani. Amin. Wajibi ne al'umma su fahimci cewa, tarihi ba ya lamuni.

*****

Malam Adamu

Wani cikin jikokin Sarkin Musulmi Abdu Ɗanyen Kasko ya gaya muna cewa a lokacin da Sarkin Musulmi Umaru ya yi wannan fita ba tare da Abdu aka yi ta ba amma wani Busoji/Budeji ya je wajen shi ya gaya mishi cewa kome ya ke yi ya bari ya je inda Sarkin Musulmi a wannan domin gobe Sarki zai rasu kuma idan yana a wurin shi za a zaɓa Sarkin Musulmi. Haka ko aka yi. A cikin dare sai ciwon ciki ya kama Sarki kuma Allah Ya karɓi abin sa. Bayan an naɗa shi ya dawo Sakkwato sai ya aika a ka kira mishi wannan Malamin/Budeji ya sa aka kashe shi wai domin kada ya ɓatar da shi. Amma ka ga ai tun farko ya yi imani da shi amma bayan ya cimma biyan buƙatar shi ya kashe shi wai domin kada ya ɓatar da shi. Allah Ya jiƙan magabatan mu.

*****

Dr. Adamu Rabi'u Bakura

Kamata ya yi a binciko sanadin samuwar sunayen sarautun ne da yadda lamarin ya faru. Misali, a ɗan ƙwarya-ƙwaryar binciken da na yi dangane da sarautar Sarkin Zamfara. Na gano cewa a zamanin haɗin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, Allah ya yi masa kuben rahama, amin. Duk wata gundumar ƙasar Zamfara da aka ci da yaƙi, akan naɗa wani daga cikin jagororin ne tare da ba shi wannan sarautar. Shi ya sa yayin da Zurmi ta zo hannu, aka danƙa ta ga Abu-Hamidu, jagoran Fulani Alibawa, da muƙamin Sarkin Zamfaran Zurmi. Haka lamarin ya kasance a Dancaɗi, inda suke da Sarkin Zamfaran Dancaɗi. Haka Dingyaɗi. Abin kula a nan shi ne kafin zuwan Gobirawa tungar Alƙali, wajen da ya zama Alƙawarin har Sakkwato da sashen Shagari duk farfajiyar Zamfara ce. Daga wajen sashen da ake kira Milgoma ya zarce zuwa Boɗinga, Sifawa, Silame, Karɓe abin da ya yi gaba har Yabo duk ƙasar Kani ce.

*****

Malam Adamu

Waɗannan yankuna da aka ambata na Boɗinga, Danchaɗi, Dingyaɗi, Silame da Yabo, da Kebbe dukan su suna cikin yankunan Daular Kabi ne. Kuma Sarautar Danchaɗi ta yi ta canja suna tsakanin Sarkin Zamfara da Bunun Danchaɗi. Wannan ko ya kan faru ne idan an yi juyi (transfer) na Sarakunan Danchaɗi da Tangaza. Yau idan an ɗauke Bunun Danchaɗi an kai Tangaza sai ya koma Bunun Tangaza shi ko Sarkin Zamfaran Danchaɗi ya koma Sarkin Zamfaran Tangaza. Amma daɗai ita Kebbe gidan Sarautar Kabawa ne. An ce ɗan Autan Muhammadu Kanta ne ya fara zama a can. Silame da Binji su dama suna kusa da helkwatartar Masarautar Kanta wacce ake kira Surame. Nan ne helkwatartar Daular Kabi kafin Sarkin Kabi tomo ya koma kauyen Takalafiya inda ya zama Birnin Kabi/Kebbi saboda yana son ya yi nisa ga wasu Dauloli.

Wani lokaci ana sa sunan Sarauta ba tare da wata alaƙa da wannan wuri ke da da wannan sunan ba. Ko a cikin garin Sakkwato akwai shiyar da  ke da Sarautar Sarkin Adar da Sarkin Zamfara. Ga Sarkin Gobir na Kalgo da na Lailaba a cikin masautun Gwandu da Argungu. Kalgo mafi yawan mutanen ta Zabarmawa ne ita kuma Lailaba Kabawa ne.

*****

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji

Da aka canza hedikwatar gundumar Kadassaka daga garin Kadassaka zuwa garin Gada a cikin shekarar 1939, Mai sarautar gundumar da ya tashi zuwa garin Gada ya tafi da laƙabin sarautar Marafa da ya yi amfani da ita a lokacin da yake Kadassaka. Ya zuwa yau laƙabin sarautar Gada Marafa ake amfani da ita.

Sarkin Kudun Sifawa Muhammadu ya taho Gusau a matsayin Hakimin Gundumar Gusau /Uban Ƙasar Gundumar Gusau a cikin 1940s ya taho da laƙabin Sarautar shi ta Sifawa watau Sarkin Kudu a Gusau. Haka Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III da ya yi Hakimcin Talata Mafara na watanni 4 a cikin 1938 kafin ya zamo Sarkin Musulmi da laƙabin shi na Sardauna ya yi amfani. Haka ɗan shi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III da ya yi Hakimcin Talata Mafara daga shekarar 1953 zuwa 1956 da laƙabin Sarautar shi ta Sarkin Kudu ya yi amfani, wanda ya canje shi daga Tangaza aka ɗauko shi ya taho Talata Mafara da  sarautar shi ta Sarkin Zamfara da ya yi da ita a Tangaza.

*****

Dr. Adamu Rabi'u Bakura

Abin la'akari a nan shi ne, akwai bambanci tsakanin a tura wani jinin sarautar Daular Usmaniyya wata gunduma domin ya kula da ita, da a ba wani haƙƙin jagorancin wani wajen a matsayin shugaban yankin. Misali, yayin da Daular Gobir ta sami gindin zama a farfajiyar Zamfara, Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo ne ya naɗa Sarkin Fulani Bunguɗu na farko. Ai ma an ɗau lokuta da dama da aka dinga turo jinin sarautar Daular Usmaniyya zuwa Bunguɗu a Matsayin uwayen ƙasa, waɗanda kan zo da sarautar da suke riƙe da ita. A Talata Mafara Sarkin Kudu Mamman an tura shi ya kula da ita, amma yana rike da matsayinsa. Haka an tura Sarkin Gabas Shehu, ya kula da Talata Mafara, ya kuma cigaba da karɓar sunan sarautarsa. Yayin da  aka tura Ma'azu Lamiɗo ya kula da T/Mafara, shi kuma sai ya rinƙa amfani da sarautar Sarkin Gabas, maimakon muƙaminsa na Magatakarda, wanda aka naɗa shi tun kafin ya zama minista a jamhuri ta farko. Idan aka karkata gundumar Moriki kuwa, a can ma za a tarar cewa, ai Fulani ne ke riƙe da sunan sarautar Sarkin Ɓurmi ba Barebari ba kamar yadda ya kasance a Masarautar Bakura. Hasali ma idan ka je garin Moriki, za ka tarar da al'ummar Ɓurmawan na asali da fashin goshi tamkar na al'ummomin Ture ta da Jabo.

Akwai abubuwan tarihi a farfajiyar Zamfara da ya kamata a taskance, amma abin nan da ya tarwatsa birnin Zamfara da Zamfarawa ne ke kawo cikas wanda hakan ya haifar mana da koma baya. Sai dai kawai mu roƙi mai kowa da komai ya yaye mana nau'o'in matsalolin.

*****

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji

Ban fahimce ka ba Babban Dakta. Maganar naɗa Ɗan Zundumi a matsayin Arɗo ko Sarkin Fulani a Bunguɗu da Mai Martaba Sarkin Gobir, Malam Ummaru Bawa Jan Gwarzo ɗan Sarkin Gobir Ibrahim Babari ya yi shi ne domin a lokacin inda suka kafa Bunguɗu a ƙarƙashin Daular Gobir ne. Saboda haka ba ɗauko wani ya yi ba daga can Alƙalawa ya kawo a Bunguɗu ba ballantana ya zo da laƙabin Sarautar sa ta Gobir.

Da wannan nike neman ƙarin bayani akan wannan sharhi da Mai Girma Dr. Adamu Rabi'u Bakura ya yi.

*****

Dr. Adamu Rabi'u Bakura

Ai shi arɗon ne ke da ma'anar Sarkin Fulani. Kuma Ɗanzundumi Sarkin Gobir Bawa ne ya naɗa shi don ya kula da yankin. A daidai wancan lokacin Bunguɗu ba ta haɓaka ba. Hasali ma a duk farfajiyar ba garin da ya kai kamar garuruwan Gada da Kanoma. A daidai lokacin masana tarihi sun kira su da sunan Birni. Misali Birnin gada wanda ya kasance wurin da aka bayar da tutocin ga waɗanda suka gudanar da Lahadi. Hasali ma duk suna da gidaje, kamar yadda aka samar da gidajen manyan sarakuna a garin Kaduna. Turawa sun kwaikwaya ne daga Daular Usmaniyya. 

Wani abin kula a nan shi ne akwai wasu garuruwa da babu su. Wasu kuma suna ƙarƙashin kulawar wani yanki ne. Masai, Maru na ƙarƙashin kulawar Kanoma ne a can da. Maradun na ƙarƙashin Talata Mafara ne. Haka a daidai shekarar 1805 ko kafin lokacin Sarkin Sarkin Zamfara Barshi ba wanda ya san shi da sunan Sarkin Zamfaran Anka. An ma dauki dogon lokaci babu ɗuriyar Zamfarawa balle sarkinsu. Sakamakon kisan kiyashin da Gobirawa suka yi musu. Shi kansa Sarkin Barshi, an tsito shi ne cikin gawawwakin Jinin sarautar da aka kashe, yana jinjiri. Yayin da aka kawo sa gun Sarkin Gobir da nufin ya bayar da umurnin kashe shi, sai ya ce: "bar shi"tun da kuka ga Allah ya bar shi. 

Tun daga lokacin ne aka dinga kiransa Barshi. Ya girma a gidan Sarkin Gobir. Ta yadda ya ji ana bayanin yadda aka yi wa Zamfarawa kisan gilla, shi ya sa da ƙarfi da ya kawo, ya dinga tara makamai tare da ƙoƙarin tara Zamfarawa waje ɗaya. Samun labarin halin da yake ciki ne ya sa Sarkin Gobir ya kurbatse shi. Ya gudu ya koma Kuryar Madara, daga can ya koma Tunfafiya. Yana Tunfafiya ne ya sami labarin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya dawo Sifawa, sai ya je ya yi masa Mubaya'a. 

Yayin da ya dawo, sai Sarkin Mafara ya nemi ya bar yankin ƙasarsa tare da alƙawalin dinga biyan kudin ƙasa gare shi. Da nan sai ya nemi mafaka ga Sarkin Ɓurmin Bakura. Sarkin ya lamunce masa ya zauna duk inda yake buƙata a ƙasarsa. Daga Tunfafiya ne ya koma wurin da ake kira Haɗar Askunne. Idan an wuce 'yargeda wajen da ake sayar da dankali (kudaku/lawuru). Za a ga jikoki a hannun dama in an fito daga 'Yargeda za a je Sakkwato. Daga bisani Sarkin Ɓurmi ya tanadar masa da mazauni tare da sanssninsa a wajen Damri. Bayan watanni uku da tarewarsa, ya amsa kiran Mahaliccinsa. Mu kwana nan.

*****

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji

Ɗan gyara kaɗan, babu lokacin da babu ɗuriyar Zamfarawa duk kuwa da mamayar da Gobirawa suka fara yi masu a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Gobir Ibrahim Babari a cikin 1762 daidai lokacin mulkin Sarkin Zamfara Marok'i. Bayan karɓe Ƙasar Zamfara daga gare su ai Zamfarawan sun yi ta gungu a wurare daban daban irin su Kiyawa da Banga da Kuryam Madaro domin a Kuryam Madaro ma ne Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya same su suna rigima akan wanda zasu naɗa Sarkin su, ya basu shawarar su zaɓi Abarshi. Bayan sun naɗa shi Sarkin Zamfara anan Kuryam Madaro Gobirawa sun bi su har sai da suka gudu zuwa Tumfafiya  inda suka taras da Zamfarawan Mafara kafin su mayar da hedikwatar su a Talata Mafara. Anan suka baiwa Sarkin Zamfara Abarshi da Jama'ar sa mafaka, daga baya kuma su ka neme shi da ya tashi ba za su iya ci gaba da zama dashi.

Wannan ne dalilin da yasa ya nemi amincewar Sarkin Ɓurmin Bakura na lokacin cewa ya na son ya zauna a cikin Ƙasar shi, ya bashi izni shi kuma ya zaɓi ya zauna a Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura inda anan ne ya yi wafati. An yi Sarkin Zamfara guda biyu a Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura, na biyun shi ne Ɗan Baƙo wanda shi ne ya tashi daga Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura zuwa Anka. Ya yi sarauta daga shekarar 1815 zuwa cire shi a shekarar 1824. Ko da suka koma Anka sun tarad da ginannen Birni ne wanda Banaga Ɗan Bature ne ya yi shi, a ruyawa mafi rinjaye an ce sun fitar da shi ne daga Anka ta hanyar sammu shi ne dalilin da ya sa ya ƙirƙiri Sabon Birnin Banaga inda a can ne ya rasu, su kuma sai suka dawo Anka inda su ka ci gaba da zama da sarautar su ta Sarkin Zamfara ya zuwa yau. Saboda haka tun daga shigowar su a 1300 da kaddamar da hedikwatar su ta farko a Dutci ta hannun Jagoran su mai suna Dakka har samar da sabuwar hedikwata a Birnin Zamfara ta hannun Sarki Bakurukuru Ɗan Dakka har zuwa samar da hedikwatocin wucin gadi a Kiyawa da Banga da Kuryam Madaro da Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura ya zuwa Anka ya zuwa yau babu lokacin da babu ɗuriyar waɗan nan Zamfarawa. Anka kuma da ka ce babu ta sai daga baya to akwai domin bayan an kori Banaga Ɗan Bature daga Birnin shi da ake kira Birnin Banaga dake Kasar Maru ta yanzu aka dawo da mazaunin Masarautar a Maru, aka naɗa Ummaru Ɗan Malam Muhammadu Da'e a matsayin Sarki da laƙabin Banaga da ta samo asali daga korarren wanda ya zauni yankin, watau Banaga Ɗan Bature wanda Bazamfaren Mafara.

Bayan fitar shi daga yankin ya je ya ƙirƙiri Morai daga nan ya samar da Anka da Sabon Birnin Banaga inda anan ne ya rasu.

A duba ayyukan Dr. Garba Nadama da Farfesa Kabiru Chafe da na Mr. Krieger da na Dr. Sanusi Maradun da Infakul Maisur na Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi za a samu waɗan nan bayanai a ciki.

Post a Comment

0 Comments