Ticker

6/recent/ticker-posts

Daga Taskar Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji

"Sarki ka haihwa Sarki
 shi ɗan Talakka duw
   wada yag girma ba ya
    yin Sarki.

Ko ya kai kamar Alasan
ya girma ba ya yin Sarki".

Inji Makaɗa Abdun Inka Bakura a faifansa na Marigayi Mai Girma Sarkin Ɓurmin Bakura, Alhaji Muhammadu Mai lafiya mai amshi "Mai Ƙasab Ɓurmi, gwarzon Bubakar na Alkali'.

Alasan da ya ambata a cikin wannan ɗiyan Waƙar ya na nufi Marigayi Alhaji Alasan Ɗantata Attajirin da aka yi a Kano. Ana kyautata zaton  Marigayi Mai Girma Sarkin Fawan Bakura, Alhaji Muhammadu ya ke nufi da waɗan nan ɗiyan Waƙar domin a lokacin da ya yi ta lamari ya yi tsamari sosai tsakanin Sarkin Ɓurmin da Sarkin Fawan har ma ana hasashen shi Sarkin Fawa dake da madafun iko a hukumance /gwamnatance a lokacin (Member ne na Sokoto State House Of Assembly a ƙarƙashin Jam'iyyar NPN mai mulkin Jihar) ya na shige da fice domin a cire Sarkin Ɓurmin.

Kafin waɗan nan ɗiyan Waƙar ya bayyana irin wannan shige da ficen a cikin Waƙar inda ya ke cewa... Kai mai son a hidda Sarki, gama tcegumin ka ko an hishshe shi ba ka yin Sarki... Sai kuma ya biyo da waɗan can ɗiyan Waƙar na sama.

Kenan dai maganar Malam Imrana da ke cewa a gare su Masartan Fada duk wanda bai da jinin sarauta a jikin sa komai girman sa Talaka ne ta fito a fili. Allahu Wa'alam!

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments