Ticker

6/recent/ticker-posts

TATSUNIYAR DILA DA BIRI

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

TATSUNIYAR DILA DA BIRI

Gatanan - gatananku

An yi wani biri mai girma da ƙarfi, wanda yake ganin babu wanda ya yi ƙarfinsa a wancan zamani, don haka ba ya tsoron kowa kuma ba ya tsoron komi, koyaushe ya ci abinci ya ƙoshi sai ya ce “Allah ya kawo tashin hankali” shi kuma malamin daji wato dila wannan maganar tana damunsa, koyaushe biri ya yi ta, har ma dila yakan kwatse shi ya ce “kai dai Allah ya sawwake, tashin hankali ba kyau”. To wannan maganar tana ɓata ma biri rai har ta tunzura shi! Da zarar dila ya ce haka sai biri ya ji kamar ya mutu saboda zuciya, sai ya sake cewa “in ka san inda tashin hankalin yake mu je ka kai ni” wannan maganar kuma ta dami malamin daji, koyaushe biri ya yi masa ita sai dai ya haƙura ya haɗiye don haushi, da mamakin yadda har wani zai yi ta neman tashin hankali! Daga nan sai dila ya yi alkawalin nuna ma biri inda tashin hankalin yake, koyaushe suka ga juna babu wata magana sai ita.

TATSUNIYAR DILA DA BIRI

Wata rana dila ya fita wajen yawace-yawacensa sai ya cimma magasa, wato inda ‘yan farauta suke gasa namun dajin da suka farauto, ya lura da irin wulakancin da mafarauta suke yi wa dabbobin da suka kaso, wani a feɗe shi a cire fatar, wani a tsire shi, wani a babbake har fatar, wani kuma a yi masa gunduwa-gunduwa, da sauran nau’o’in cin mutunci iri-iri, wasu ma sai su cire wani abu su jefar da wani abu, ga kuma makamai iri-iri sun aje gefe, ga wani ƙamshin nama yana tashi, yara suna tariyar man da ke darara daga irin waɗannan dabbobin da ake gashi! Malamin dawa bai taɓa ganin iri tashin hankalin da ya wuce wannan ba.

Bayan ya dawo sai suka haɗu da biri, sai biri ya yi irin addu’ar da ya saba, shi kuma dila sai ya ce “ka shirya zan kai ka gobe”, ai da jin haka sai zumuɗi biri yake yi, kafin lokacin da dila ya sa masa har yana cewa “wayyo ni biri zan haɗu da abin da nike nema” wato tashin hankali. Tun kafin safiya ta waye sai biri ya iske dila ya ce “tashi mu je”, shi kuma malamin daji ya ce wa biri “yi haƙuri mi kake tauna na baka na zuba?” Dila ya sani cewa sai can da yamma ne tashin hankalin ya fi tsanani (wato lokacin gashi) don haka bai yi wani uzuri ba, sai da ya ga lokaci ya matso sannan ya shiga gaba biri na biya har ya kai shi gindin inuwar gashi, wato innuwar iccen da mafarautan ke gashi idan sun dawo daga farautar! Biri ya ce “to ina tashin hankalin yake?” Sai dila ya nuna masa kofatai da fatu da kanun waɗanda ake jefarwa, sai biri ya yi tsaki mts! Ya ce, “wannan shi ne tashin hankalin?” Sai dila ya ce “ai wannan kaɗan ka gani, abin da za a yi, ka hau wannan iccen ka laɓe zuwa an jima zaka ga tashin hankali”

Ɗaram, sai biri ya haye sama, da ma hawan bishi ga biri gado ne, shi kuma dila ya ce “sai mun haɗu in sha labara”. Ya bar wurin da nisa saboda tsoron kar tashin hankalin ya rutsa da shi. Biri sai waige-waige yake yi don ya ga ta inda tashin hankalin zai ɓullo, da an jinjima sai ya yi tsaki ya ce “wai har yanzu tashin hankalin bai zo ba?”

TATSUNIYAR DILA DA BIRI

Can da la’asar sansanya, sai biri ya fara jin kiɗan mafarauta yana tashi, idan kiɗin ya matso sai ya tsaya har dai aka iso gindin wannan bishiyar gashin, inda birin yake jiran don ya ga bala’i. Biri ya fara ganin ana sauke matattun dabbobin da aka kaso, daga ciki har da waɗanda ya sani domin akwai wani biri wanda ya fi shi girma! Sai jefar da su ake yi tim! Tititim! Titim! Biri na ganin haka sai ya ƙara fakewa, ya karyo wani reshen bishiyar ya kare idanunsa don kar a gane shi!

TATSUNIYAR DILA DA BIRI

Mafarauta tare da yaransu sai fiɗa suke yi, suna zagin wasu namun waɗanda aka sha wahala wajen kamunsu, musamman wannan goggon birin! Bayan sun gama fiɗa sai ake haɗa gwami[1]. wuta ta kama sai aka fara gashi, biri yana dai sama abin duniya ya dame shi, babu halin ya sauko don ya san ko yaransu bai tsere ma da gudu, balle manyan! Ƙamshi sai tashi yake yi, a janye wannan a sa wannan har dai suka gama, suka kwashi kayansu suka yi gaba. Da biri ya ga sun tafi ba a bar kowa ba sai yara masu nawar gashi, sai ya buɗe fuskarsa ya fara karyo ‘yan itatuwa ta jefo su ƙasa, idan ya jefa cikin wuta sai yaran su ɗauke su aje gefe, har wani ya ɗaga kai sama ya ga biri, sai ya fara ihu yana cewa kai jama’a ku dawo biri a sama, to da ma manyan ba su yi wani nisa ba, sai suka shiga dawowa, sai da suka taru sai aka fara harbin biri da kibau, wasu su yi jifa da duwatsu, wasu da sanduna! Idan ya yi tsalle a wannan reshe ya koma wancan. Can sai wani ya sami biri ga ciki da kibiyarsa, sai kuwa birin ya faɗo ƙasa tim! A buga a buga har dai ya gudu da kibiya soke ga cikinsa.

TATSUNIYAR DILA DA BIRI

Ko da dila ya hangi biri aguje sai ya mayar da gaba Gabas ya fara sallah, har ya iso, yana wata irin ƙyaƙya[2], yana kama kibau ya girgiza shi ya busa iska yana faɗuwa yana tashi, amma dai dila bai damu ba sallarsa kaɗai yake yi, said a ya ga biri ya fara laushi sai ya sallame, da biri ya gay a sallame sai ya fara murna, shi kuwa dila sai ya tashi ya ƙara kabbarawa. Da ya fajimci biri ya fara galabaita sai ya sallame sallar, ya riƙa masa suka cire kibau. Daga nan sai malamin daji ya ce “Allah ya raba mu da tashin hankali” sai biri ya yi farat ya ce “amin malam – amin malam”, 

Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

Tambayoyi

1.                  “Kowa ya ƙi ji ba zai ƙi gani ba” tattauna wannan karin magana kamar yadda take a wannan tatsuniya.

2.                  Mene ne tashin hankali a cikin wannan tatsuniyar?

3.                  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?



[1]  A kunna wuta ta kama sosai.

[2]  Kukan wahala mai ƙarfi.

Post a Comment

0 Comments