Tatsuniyar Sarkin Raggaye

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    Tatsuniyar Sarkin Raggaye

    Gatanan - Gatananku

    Wani mutum ne yake zaune a wani gari, to shi mutumin bai da wani aikin fari balle na baƙi sai hutawa kawai, kodayaushe sai dai ya yi ta zaman shan innuwa, idan wannan ta janye sai ya tashi ya koma wata inuwar, babu wata innuwar garin da bai san da zamanta ba. Saboda haka sai mutanen garin suka sa masa suna sarkin raggaye, wai shi baya iya aikin komai kodayaushe sai biyar innuwa yana kwantawa don hutawa.

    Tatsuniyar Sarkin Raggaye

    Wannan halayya tasa ce ta sa kowa ya rena shi a cikin garin, har baya da ikon sa bakinsa a cikin maganarsu! Da ya gaji da halin mutanen wannan garin nasu, sai ya riÆ™a fita garin yana zuwa bayan gari, sai in dare ya yi ya dawo, da safe idan ya tashi sai ya je cikin daji inda babu kowa ya sami inuwa ya ci gaba da zaman raggancinsa, idan wannan inuwa ta Æ™are ya je wata. Wata rana sai ya je wata innuwa mai sanyi ta wata bishiya ya kwanta, yana kwance har bacci ya kwashe shi, yana cikin bacci ashe akwai maciji a kan bishiyar, sai maciji ya sauko ya ce “kai wannan bawan Allah don Allah tashi ka shareman innuwata” sai ya ce “kai wannan maciji in ba wautarka ba? wa ka taÉ“a jin ya sa ni aiki?” “ba don gudun aikin na fito gari ba na dawo daji?” kuma kai yanzu har ka isa ka sani aiki?” “Wallahi bani iyawa”

    Tatsuniyar Sarkin Raggaye

    Sai ya ce “don Allah ka taimaka ka share man wannan innuwar”, ya sake cewa “a a wallahi ban iyawa, kai ba ka isa ka sa ni aiki ba”. Macijin dai ya yi ta rarrashinsa har dai ya shawo kansa, sai ya fara share masa innuwar da ya kai inda rana sai ya dawo, don kar ya ji zafinta, yana gama  sharewa sai ya ce masa “to nagode, tunda ka share man ni ma zan yi maka wata kyauta” sai macijin ya ba shi wata jaka ya ce masa “yanzu ka koma gari duk wanda ya sake kwatsuwarka ka buge shi da wannan jikar zai koma jaki”, “sai ka kama ka sayar da abinka”. Sai kuwa sarkin raggaye ya karÉ“a ya ce “to nagode Allah ya saka da alheri”, sai ya dawo cikin gari ya riÆ™a zagayawa, a duk in da ya iske mutane suna gardama, sai ya zo ya tsumbula bakinsa ya ce “kai ku tsaya ku tsaya”, sai wani daga cikinsu ya ce “kai yanzu har ka isa ka ba mu umurni mu ji? don kana wa?” “Kai ma da kake sarkin raggaye me ka amfana?” shi kuma sai ya ce “idan baka bari ba, yanzu ina mayar da kai jaki” Sai mutumen ya ce “ho É—an neman shawaraki! wa za ka mayarwa jaki?” ai kuwa sai ya buga masa jakar! Sai kawai a ga ya fara komawa jaki! sai ka ji kawai mutum yana kukan jaki “uugghhmm- uugghhmm-uhm-uhm” kawai sai a ga jaki ya tashi yana kuka, shi kuma ya kame shi ya É—aure.

    Tatsuniyar Sarkin Raggaye

    Haka ya dinga yi idan ya mayar da mutun jaki sai ya sa igiya ya É—aure shi. Da haka nan-da haka nan har ya tara jakai masu yawa, ya riÆ™a kai wa kasuwa yana sayarwa yana samun kuÉ—i. Wannan sana’ar tasa ta sa mutanen garin suka shiga taitayinsu, ba a sake rena shi ba, har tsoransa ake ji, duk abin da ya ce ko ba gaskiya ba ne dole a ce gaskiya ne don tsoron kar ya mayar da mutum jaki. Ya zama babban mutum a cikin garin, ko sarkin garin ba ya gardama da shi bare ya kwatse shi. Duk lokacin da sarki ya ce kaza, idan sarkin raggaye bai aminta ba sai sarkin ya ce Æ™arya nike yi! Likkafar sarkin raggaye sai gaba take yi babu abin da za a yi a garin sai ya yarda da shi, har maroÆ™a suna yi masa kirari suna cewa “kaway yi ba da kai ba ta tashi! Shi ya sa har yanzu Hausawa suke amfani da wannan karin maganar.

    Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

    Tambayoyi

    1.                  Me ya sa duka jama’ar gari suka rena sarkin raggaye?

    2.                  Wace riba ya samu ga wannan halayya tasa?

    3.                  WaÉ—anne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.