Ticker

6/recent/ticker-posts

Tatsuniyar Halilu Da Akilu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

Tatsuniyar Halilu Da Akilu

Gatanan - Gatananku

A wani gari an yi wasu yara ne su biyu babansu guda, amma ba uwarsu  guda ba, Sunan ɗayan Halilu shi kuma guda an ce masa Akilu. Akilu yana da shanu da yawa da kare, su kuma su Halilu ba su da ko ‘yar akuya! Wata rana sai mahaifiyar Akilu ta tambayi mahaifiyar Halilu ta ce “in faɗi in mutu kuna riƙe man ɗana amana?” Sai mamar Halilu ta ce “eh”, kamar wasa sai kuwa ta faɗi ta mutu! Bayan wani ɗan lokaci, sai kishi ya taso ma uwar Halilu, ganin irin yadda Allah ya hore masa arziki bai ba ɗanta ba. Ta yi ta yi ta ga ya koma baya, amma dai ina Aƙilu sai gaba yake ciga harkokinsa. Wata rana sai ta shinkafa da miya ta sa masa kitse da man shanu ta haɗ da guba don ya ci ya mutu su huta! Akilu bai sani ba yana wurin kiyo, yana kiyonsa tare da karensa sai ya ji karen ya fara waƙa yana gaya wa Akilu yana cewa;

            “Kai Akilu zam-zam-zam

Shinkafar gidanku zam-zam-zam

Kar ka cita zam - zam -zam

Kashe ka za a yi zam - zam -zam

A anshe shanun zam - zam -zam

Tatsuniyar Halilu Da Akilu

A ba Halilu zam - zam –zam”.

Da Aƙilu ya ji wannan bayanin sai ya ce ma karen “da gaske kake yi?” Shi kuma ya ce “eh” sai ya yi godiya, da lokacin tashinsa kiyo ya yi sai ya tashi ya koma gida, da isarsa sai matar ta ce  “Aƙilu zo ka ci abinci” sai ya ce “a’a na na ƙoshi domin na ciyo daga gidan abokina”, sai ya shige ɗakinsu ya kwanta har ya yi bacci, da safiya ta yi, sai ya tafi wurin kiyon dabbobimsa kamar yadda ya saba. Bayan fitarsa sai kishiyar uwar tasa da girka tuwo, shi ma aka sa kitse da man shanu aka sa guba! Yana can wurin kiyon sai karensa ya fara waƙa yana cewa:

“Kai Akilu zam-zam-zam

Tuwon gidan ku zam-zam-zam

Kar ka ci shi zan-zan-zam

Kashe ka za ai zam-zam-zam

A anshe shanun zan-zan-zam

A ba Halilu zan-zan-zam”.

Tatsuniyar Halilu Da Akilu

Sai Aƙilu ya dafa karen ya kuma tambaye shi ya ce “da gaske kake yi?” Karen ya ce “eh”, saboda jin haka sai ya yi dare bai dawo gida ba, yana komawa gida sai ya kwanta ya yi bacci abinsa, da safiya ta waye sai kishiyar uwar ta je wurin bokanta ta ce “maganin bai yi ba”, sai ya ce “ta koɗa wuƙa in dare ya yi Aƙilu ya kwanta yana barci sai ta yayyanka shi!” Lokacin da ya tafi wurin kiyo sai karensa ya fara waƙa a ciki yana faɗin:

“Kai Aƙilu zan-zan-zam

Inka koma gida zan-zan-zam

Ka cire kayanka zan-zan-zam

Ka sama halilu zan-zan-zam

Ka cire nashi kasa gare ka zan-zan-zam

Ka ɗauke halilu zan-zan-zam

Ka kai shi wurin kwanan ka zan-zan-zam

Ka kwanta wurin kwanan shi zan-zan-zam”

Tatsuniyar Halilu Da Akilu

Yana komawa gida ya yi haka nan, ai sai ta yanke ɗanta, ta yi mai gunduwa-gunduwa ta zuba cikin buhu! safiya ta yi Aƙilu ya tsere babu abin da ya same shi. Ita kuma sai kuka da ihun baƙin cikin muguntar da ta yi wa kanta.

Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

Tambayoyi

1.  Yaya dangantakar Halilu da Aƙilu take?

2.  Wa ya riƙa ceton Aƙilu daga cin gubar da aka sa masa a cikin abinci?

3.  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?

Post a Comment

0 Comments