Tatsuniyar Busa In Faɗi

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    Tatsuniyar Busa In Faɗi

    Gatanan - gatananku

    Wata kura ce da ɗiyanta, wadda take zaune cikin daji bata taɓa ganin raƙumi ba, sai wata rana tana shawaginta a cikin daji sai suka haɗu da raƙumi, tana ganinsa sai ta ce “kai ji wancen abu fa dogo” sai ta matsa wurin shi ta ce masa “kai wannan abu haka kake da tsawo?” to wai ma mene ne sunan ka? sai ya ce “sunana busa in faɗi” sai ta fashe da dariya ta ce “Allah sarki! kai hakanan kake da an busa ka sai ka faɗi?” sai ya ce “eh”sai ta ce “to yanzu da an busa ka faduwa zaka yi?” sai ya ce “eh”sai kawai kura ta je gabansa ta busa” da busawarta sai kawai ya faɗi ragwagwam! Da aka ɗauki ɗan lokaci sai ya tashi, sai ta ƙara busawa, shi kuma sai ya ƙara faɗuwa ragwagwam! ta dawo gefen sa ta sake busawa, sai sake yanke jiki ya faɗi!

    Tatsuniyar Busa In Faɗi

    Ai kuwa sai kura ta ce “kana jira na nan in je gida in dawo?” Shi kuma ya ce “ai ni ba ni zuwa ko’ina a nan nike kiyona”. Da ta je gida sai ta iske ɗiyanta, sai ta fara cewa “abun mamaki Ɗan auta zo ka ga wani ikon Allah wai wani abu ne babba mai tsawo, amma duk shi duk tsawonsa da ka busa shi, sai ya faɗi! kuma ta ce “ku biyo ni in gwada maku shi” ta ce “ku ɗauko igiyoyi” suka tambaye ta me za ta yi da su? Sai ta ce “babu ruwanku ubanku zan yi da su” ban son yawan tambayoyi. Da isarsu inda raƙumi sun iske shi ya tashi tsaye yana kiyo, sai ta ce “ku bari Ɗa’auta ya busa ku ganai” Ɗan’auta ya busa ya ga raƙumi ya faɗi richa! sai kura da ‘ya‘yan suka yi ta mamakin irin wannan ikon Allah, har suna faɗi a zuyiyarsu “wai wannan abu duk shi duk girmansa da an busa shi sai ya faɗi”, abunka da kura da mugun son banza, sai ta ce wa ‘ya’yan ta “ku zo idan na busa shi ya faɗi zan hawo bayansa, sai ku ɗaure ni saman shi” haka kuwa aka yi, kura ta hau raƙumi ‘ya’yanta suka ɗaure ta kamar yadda ta umurce su saboda ta hana su yawan tambayoyi, duk inda kura ta ji bai tsuku ba sai ta ce masu “kai nan fa bai tsuku ba, ku ƙara tsuka wa”

    Tatsuniyar Busa In Faɗi

    Bayan an ɗaure ta tam, sai raƙumi ya tashi ya zuba da gudu! Kura sai ihu take yi tana cewa “kai ɗan auta matso gaban shi ka busa” da ɗan auta ya matsa gaban raƙumi domin ya busa shi ya faɗi, sai ya ga za a take shi, sai ya janye, ya tafiyarsa, har raƙumi ya wuce ta ƙarƙashin wata ƙayar aduwa, a nan ne fa sai kura ta fizgo wani tsumman da iska ya sagale, ta yi rawani da shi,  raƙumi bai dakata ba sai da ya shigo gari, kuma bai garje ko’ina ba, sai cikin kasuwa. Yana shiga sai mutane suka yi ta cewa “la! ga kura cikin gari!” sai kura ta fara ƙarya tana cewa “ba kura ba ce”, “irin buzayen nan ne na Tabotaki”, raƙumin dai bai tsaya ba, sai ƙara shiga jama’a yake yi, bai zame ba sai a tsakiyar kasuwa. Raƙumin yana zuwa tsakiyar kasuwar sai ya faɗi kwance, ga kura ɗaure a bayansa. Ganin haka sai wani mutum ya ce “to jama’a kowa ya kwantar da hankalinsa ya samo abin bugu mai kyawo”, sai kawai mutane suka sami sanduna da faskare miƙaƙƙu lafiyayyu, wanda ya sami mai bandarwa ya aje ya sake wani, suka fara danƙara mata duka, suna ta bugun kurar hankali kwance, ba tsoro babu ja da baya, ita kuma sai faman fesa zawo take yi, tana ta zawo, su kuma mutanen sai ƙara bugunta suke yi tana ihu. To kun san halayen mutane daban-daban suke, ana cikin haka sai wani mutum mai karambani da shisshigi ya ce kowa ya tsaya, shi zai yi mata bugu guda guntu uku, sai jama’a suka saurara, sai kawai ya gyara kulkinsa ya shiri-shiri ya buga mata wannan kulkin ga baya! Ai kuwa sai da tsawon (igiyoyin) da aka ɗaure ta da su suka tsunke, daga nan kawai sai kura ta faɗo daga bayan raƙumi ta tashi ta zura da gudu, duk jama’ar da ta nufa sai su watse! kafin ta fita sai ta bi ta teburin sarkin fawa ta ɗauke cinyar sa ɗaya, ta hurce da ƙyar, tana gudu jama’a suna biyar ta har ta tsere.

    Tatsuniyar Busa In Faɗi

    Da isarta gida sai Ɗan’auta ya fara cewa “Mama ashe ke kika iya bushin abinki, sai da muka dawo sannan kika busa abinki?” Kura ta ce “ba ni na iya bushin abina ba ubanka ɗan iskan marar kunya!” Sauran ‘ya’yan suka fito suna ta yi mata sannu da zuwa, kowa ya matso sai ta harare shi, ta ce masu ko tsunki ba wanda zata ba daga cikin namanta da ta ƙwato daga teburin sarkin fawa. Sai ta ɗora suyar naman ta yi ta suya har ta soye ko lasa hannunta ba ta yi ba, Ɗan auta da danginsa suna ta haɗiyar yawu, daga nan sai wata dabara ta ɓullo masa ya ce “mama inshawo ruwa” sai kura ta ce masa “eh tafi ka shawo ruwan, don su kaɗai ne zaka sha, don ba wanda zan ba wa naman nan ko tsunki” da ɗan auta ya ji haka sai ya ƙara cewa “mama in shawo ruwa?” ta sake ce masa kamar yadda ta ce masa a baya, sai ɗan auta ya yi tunanin wai ya za a yi ya ci naman nan da mamarsa kura ta hana mashi? A lokacin da ya je shan ruwan sai ya je da ƙwarya, sai kawai ya aje ƙwaryan nan ƙasa ya sa ƙafa ya taka ta ta fashe ramamas! Sannan ya yi ihu! Ya ce wallahi sarkin fawa ba ni ba ne! Ko da kura ta ji haka sai kawai ta tashi ta ce “Ƙafa me na ci na hana maki? Sai kuwa ta zuba da gudu, ta ɗauka sarkin fawa ne ya biyo sawunta har gida, daga nan sai su ɗan auta suka canye naman sarai. Tun da kura ta wuce ba ta sake waiwayo gidanta ba, sai can cikin dare ta dawo tana ‘yan raɓe-raɓe don tsoron kar sarkin fawa ya yi mata wani makircin.

    Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

    Tambayoyi

    1.                  Me ya sa raƙumi ya yi dabarar faɗuwa idan kura ta busa shi?

    2.                  Saboda me ‘ya’yan kura suka ɗaure kura a bayan raƙumi?

    3.                  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.