Ticker

6/recent/ticker-posts

Tatsuniyar Musa Ɗan Sarki

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

Tatsuniyar Musa Ɗan Sarki

Ga ta nan, ga ta nan ku.

A wani gari an yi wani ɗan sarki wai shi Musa. Shi kuwa Allah ya yi masa ƙira mai kyawo, sannan ga iya magana, kuma a lokacin da ya yi wayo babansa ya sa shi makaranta. A cikin wannan gari kuwa akwai wata kyakkyawar yarinya, son kowa ƙin wanda ya rasa. Saboda kyawonta da farin jininta a wajen samari har ana yi mata kirari “Allurar cikin ruwa, mai rabo ka ɗauka”. Musa da ya ga wannan yarinya sai ya ce yana son ta. Ita kuma ta amsa. Nan da nan sai soyayya mai tsanani ta shiga tsakaninsu, kai har ta kai yarinyar ta daina faɗar sunan Musa. Ba ma shi kaɗai ba, duk wani mai suna Musa. Har ma lokacin da aka zo maganar ɗaurin aure a tsakaninsu. Sai Musa ya dage ba za a ɗaura auren ba sai lallai ta faɗi sunansa. Ita kuma ta ce ba za ta faɗa ba. Daga nan, Musa ya ɗauki alwashin sai ya yi sanadin da ta faɗi sunansa kafi a ɗaura aurensu.

Ana nan, ana nan, rannan sai yarinyar da ƙawayenta suka tafi wanka a bakin rafin garinsu kamar yadda al’adar garin take. Da zuwansu, sai suka tuttuɓe[1] suka shiga cikin ruwa suna wanka. Ashe duk abin da suke yi Musa yana biye da su ba su sani ba, sai ya faki idonsu bayan sun shiga rafi suna wanka, ya kwashe duk suturarsu, ya je ya hau kan wata doguwar bishiya a kusa da kogin.

Tatsuniyar Musa Ɗan Sarki

Da ‘yan matan nan suka ƙare wanka suka fito, sai suka ga babu kayansu! Don haka sai suka fashe da kuka.

Can sai suka ɗaga kansu sama suna hange-hange, sai suka hango Musa a kan bishiya riƙe da kayansu. Nan da nan suka shiga roƙon sa don ya ba su kayansu, amma ya ƙi. Sai dabara ta faɗo wa wata a cikin su, sai ta shiga rera wa Musa waƙa tana cewa:

“Kai Musa, kai Musa,

Musan gayya,

Musa ɗan makaranta,

Musa ɗan sarki,

Musa kai wa Allah,

Musa ba ni bantena,

Musa ba ni zanena,

Musa ba ni fatalata”.

Wanan yarinya tana ƙare waƙarta, sai Musa ya zubo mata kayanta. Ganin haka, sai ‘yan mata da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai suna zuwa gindin bishiya suna rera wa Musa irin wannan waƙar. Kowace yarinya kuma ta gama waƙar sai Musa ya zubo mata kayanta. Sai ya rage ɗaya tak, wato budurwar Musa. Ita kuma da ta zo sai ta ce.

“Kai wane, kai wane,

Wanen gayya,

Wane ɗan makaranta,

Wane ɗan sarki,

Wane kai wa Allah,

Wane ba ni bantena,

Wane ba ni zanena,

Wane ba ni fatalata”.

Da Musa ya ji ba ta ambaci sunansa ba, sai ya hana ta yana cewa:

“Na ƙi ba ki,

Na ƙi ba ki,

Sai kin ce,

Kai Musa, kai Musa,

Musan gayya,

Musa ɗan makaranta,

Musa ɗan sarki,

Musa kai wa Allah,

Musa ba ni bantena,

Musa ba ni zanena,

Musa ba ni fatalata”.

Amma ita yarinyar, sai ta ƙi faɗar yadda Musa yake so ta faɗa. sai ta ci gaba da yin waƙarta ta da, ba tare da amabton sunan Musa ba. Kuma duk sa’ar da ta maimaita waƙar sai ruwa ya kama ta. Tun ruwan yana kama ƙirjinta, har ya kusa cinye ta duk. Da Musa ya ga haka sai ya sauko ya ba ta kayanta, suka koma gidansu, aka ɗaura aure, aka yi gagarumin biki, aka kai amarya gidan mijinta.

Ƙurungus kan ɓera, ba don Gizo ba da na yi ƙarya da ma ƙarya ce na malalo muku

Tambayoyi

1.                  Mene ne sunan saurayin? Kuma wece ce yake son ya aura?

2.                  Waɗanne dalilai kuke ganin suka sa yarinyar ta ƙi faɗin sunan Musa?

3.                  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?



[1]  Cire tufafin da ke jikin mutum.

Post a Comment

0 Comments