𝗕𝗔 𝗞𝗔𝗬𝗔𝗡 𝗡𝗔𝗨𝗬𝗜 𝗕𝗔 𝗡𝗘, 𝗗𝗔𝗡'𝗨𝗪𝗔𝗡𝗔 𝗡𝗘

    𝗕𝗔 𝗞𝗔𝗬𝗔𝗡 𝗡𝗔𝗨𝗬𝗜 𝗕𝗔 𝗡𝗘, 𝗗𝗔𝗡'𝗨𝗪𝗔𝗡𝗔 𝗡𝗘
    A ƙasar Japan a lokacin ana cikin wani yaƙi, an ga wannan yaro yana ɗauke da gawar wani ƙaramin yaro a baya, yana neman wurin da ya dace saboda ya binne shi, wani soja ya ga wannan yaro, ya neme shi ya jefar da wannan kayan nauyi a bayansa, saboda zai gajiyar da shi! 
    Yaro: A'a ba kayan nauyi ba ne, ɗan'uwana ne!
    Sojan ya fahimci irin raɗaɗi da zafin da yaron ke ji na rabuwa da ɗan'uwansa, sai ya fashe da kuka!

    Aka ce tun a wancan lokaci wannan hoto ya zama wata alama ta haɗin kai a ƙasar Japan.

    Ni kuma na ce: Ina ma a ce darasin da ke cikin wannan hoto zai zamto tamu alamar haɗin kai, ba kayan nauyi ba ne, ɗan'uwana, ba kayan nauyi ba ne ƴar'uwata ce, idan ɗan'uwanka ya kasa ka taimake shi, idan ya gaji ka kama masa, idan ya yi rauni zama majingina gare shi, idan ya yi kuskure ka nemo masa uzuri, idan duniya ta juya masa baya ka goya shi a baya. Ka sani ba kayan nauyi ba ne, ɗan'uwana!

    𝗔𝗕𝗕𝗔𝗦 𝗠𝗨𝗦𝗔 𝗝𝗘𝗚𝗔
    26011445𝗛
    13082023𝗠.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.