Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Tatsuniyar gizo da mata mai sa.
Ga ta nan, ga ta nan ku
Wata rana wata mata tana tallar
santa, amma idan mutum ya saya biyan shi ne, idan shekara ta zagayo ya faɗi sunanta. Wanda ya karɓi san idan shekara ta gewayo ya
kasa tuna sunan nata, to za ta jefa shi cikin ruwan gulbi[1] ya
mutu.
Matar nan ta dinga bi
rariya-rariya, lungu-lungu, titi-titi, tana shela, tana cewa, “ku sai sa, ku
sai sa”. Da mutum ya kira ta, ta faɗa masa yadda za a biya san, sai ya fasa. Ana cikin haka, sai Gizo ya sami
labari, kuma aka gaya masa sharuɗɗan karɓar sa, sai ya amince. Mata mai sa
ta ba Gizo san, sannan kuma ta shaida masa sunanta, wato “Allazi take matar
Lazi amanu”. Gizo ya tafi da sa gida yana murna.
Da isar sa ya faɗa wa matarsa Ƙoƙi yadda aka yi har ya
sami ƙaton sa. Ya kuma ce “ke ce ba ki da mantuwa, don haka ki riƙe sunan tsohuwar nan
da kyau”.
A halin da ake wannan zance, da ma
can Gizo ya yi sabuwar amarya wato abokiyar zaman Ƙoƙi, amma kuma bai son
ta sosai, sai kawai aka gaya mata ta riƙe sunan matar nan, ba tare da ta san wani abu game da sa
ba.
Gizo ya yanke sa ya sa Ƙoƙi ta soye shi raɗau, amma ya jaddada mata cewa, “ba
na son amarya ta ji ko ƙamshin wannan nama”.
Sai Ƙoƙi ta yi farin ciki
domin an sosa mata inda yake yi mata ƙaiƙayi. Ta yi ta suyar nama har ta ƙare ƙaf. Da ya huce aka kai
shi cikin ɗaki, suka yi ta shagalinsu ba tare
da amarya ba. Da sannu-sannu nama ya ƙare.
A kwana a tashi shekara ta zagayo,
sai matar nan ta zo wurin Gizo wanda ya ɗauki alƙawarin faɗin sunanta. Haba ina! Gizo ya
manta da sunan mata, ballantana sa da aka soye masa ya cinye. Ita ma
uwargidansa Ƙoƙi ta mance da sunan matar. Sai kawai matar ta ja Gizo za ta kai shi rafi ta
jefa. Tirƙashi!
Rana ke nan take ƙoƙarin ɓaci wa Gizo, babu abin da Ƙoƙi za ta iya yi sai kallo. Matar ta ja Gizo a ƙasa ta soma kama ƙafafun Gizo, ga shi kuma yana cikin tsananin wahalar jan da aka yi masa a ƙasa.
To ashe amaryar Gizo ba ta mance da sunan matar ba. Don
haka, ta aiki yaro ta ce “ sheƙa da gudu ka gaya masa cewa ga yadda sunan matar yake.
Sai yaro ya ruga aguje, ya cim ma Gizo, ruwa kuwa har ya kai ga kunkurunsa. Da
isar sa bakin rafin, sai ya rera waƙa yana cewa:
Kai Gizo, kai Gizo,
Sunan matan nana
Allazi take matar Lazi amanu
Daga can sai Gizo ya ji wannan waƙa, sai ya yi farat ya
caɓa, yana maimaita cewa:
‘Allazi take matar Lazi tsuliya’
Haba, sai matar ta ƙara yin gaba da Gizo,
wannan karon har ruwa yana kusa ya
nutse shi. Shi kuma yaro ya daɗa cewa:
Kai Gizo, kai Gizo,
Sunan matan nana
Allazi take matar Lazi amanu
Sai matar nan ta saki Gizo, ya
samu ya fito daga ruwan da sauri. Alla-alla Gizo yake yi ya iso gida. Da
isowarsa, ya hau Ƙoƙi da faɗa yana cewa:
“Ashe Ƙoƙi ba ki sho na,
Kika ƙyale ni za a kashe
ni”.
Nan da nan yamutsi ya kaure
tsakanin Gizo da uwargidansa Ƙoƙi, har ta kai ya sake ta, ya zauna da amaryarsa lafiya wadda ita ce ta nuna
masa ƙauna ta cece shi daga halaka. Daga nan gizo ya gane cewa ba koyaushe wanda
kake so yake son ka ba .
Ƙungurus kankusu, ba don Gizo da amaryarsa ba da na yi ƙarya. Da ma ƙaryar ce na shimfiɗa maku.
Tambayoyi
1.
Wane dalili
ne ya sa jama’a da yawa suka ƙi sayen san Tsohuwa?
2.
Mata
nawa gizo yake da su? Ko yana yi masu adalci?
3.
Waɗanne irin darusa ne aka koya daga
wannan tatsuniyar?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.