Ticker

6/recent/ticker-posts

TATSUNIYAR KURA DA ƊAN MAI KUNNE

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

TATSUNIYAR KURA DA ƊAN MAI KUNNE

Gatanan - gatananku

Da kura da ɗan mai kunne suka ƙulla ƙawance, ko wane cikin su yana da ‘ya’ya, ana nan wata rana sai kawai ɗan mai kunne ya yi wani tunani na yadda zai tsira ga sherin kura kuma ya yi mata dabara, dama ya fi kura wayo sai kawai ya ce ma kura “yanzu ke kura ga wata dabara” ta ce to “mu hade ɗiyan mu mu rinƙa kawo masu abinci tare”, sai kura ta ce “eh” “gaskiya haka ya kamata”, sai kuwa suka haɗe ɗiyansu a rame ɗaya, idan kura ta kawo abinci sai tasa cikin ramen, ana nan sai ɗan-ɗan ɗan mai kunne ya ce ma ‘ya’yan kura shi sunan shi Namuduka.

TATSUNIYAR KURA DA ƊAN MAI KUNNE

Idan kura ta kawo abinci sai Namuduka ya ce nasa ne, sai ‘ya’yan kura su tambaye ta su ce “mama wai na mu duka ne?” ita kuwa sai ta ce “to in ba ku duka ba to wa zan ba abinci?”, shi kuma Namuduka sai ya cinye, akwana a tashi saboda yunwa sai kawai ɗiyan kura suka yi ta ramewa! Da tafiya ta yi tafiya sai wata rana kura ta ce ma ɗan mai kunne “yanzu ya kamata mu fitar da ɗiyanmu mu gani in sun yi ƙiba”, sai Ɗan mai kunne ya ce ma kura “ke dai ki bari sai nan gaba sannan a fitar da su sai a gani”, da tafiya ta ƙara matsawa, duk kura ta kawo abinci sai Namuduka ya ce ai shi kaɗai aka kawo ma, sai can kura ta ce to yanzu a fitar da su, sai Ɗan maikunne ya ce “to shi kenan” sai kuwa  kura ta fara fitar da nata sai ta ga ɗiyanta sun koma ‘yan hingil (duk sun rame) sai tai ta yin mamaki, daga nan sai ta tambayi ɗiyanta ta ce “ya aka yi haka?” “wai ina duk abincin da nike kawo maku?” sai suka ce “to mama idan kin kawo cewa ki ke yi Namuduka ne, shi kuma sai ya karɓa ya cinye ya ƙyale mu, sai ran kura ya ɓaci (ta hasala) ta ji kamar ta kashe ɗan mai kunne, ana nan kuma Namuduka yana cikin rame ya rasa yadda zai yi ya fito, yana gudun kar ta ga shi ya yi ƙiba, sai kawai ya yi wani tunani ya ce “ke kura don Allah riƙe man talkami na” sai kawai ya turo kunnuwasa bakin ramen, da kura ta hasala tana ganin ya turo kunnuwa nai ta ɗauka talmin ne, sai kawai ta jawo su da ƙarfi ta jefar. Ashe na muduka ne ta wurgar, kafin ta ankara shi kuma Namuduka har ya tashi ya zura da gudu da shi da mamarsa.

TATSUNIYAR KURA DA ƊAN MAI KUNNE

Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

Tambayoyi

1.                  Wace dabba ce Hausawa suke kira Ɗan mai kunne?

2.                  Da kura da Ɗan mai kunne wa ya fi wayo?

3.                  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?

Post a Comment

0 Comments