Ticker

6/recent/ticker-posts

TATSUNIYAR DILA DA KURA

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

TATSUNIYAR DILA DA KURA

Gatanan - gatananku

Wani dila ne ya sami wani gidan Fulani ya riƙa zuwa kullum yana shan ƙwan zabbi, koyaushe haka yake yi, saboda haka ya fara yin kashin wannan shagalin! Ita kuma kura tana yawonta sai ta fara ganin kashin dila, da ta sunsuna sai ta ji wani irin ƙamshi, don haka sai ta lashe! Ai kuwa sai ta cigaba da yawo don ta nemi wannan kashin, idan ta samu sai ta riƙa cinyewa, har ta raya a ranta cewa duk mai yin wannan kashin Allah kaɗai ya san irin shagalin da yake yi. Ta ce “Ubangiji Allah ya haɗa ni da mai yin wannan kashin.

TATSUNIYAR DILA DA KURA

Daga nan sai kura ta fara fakewa tana son ta gamu da mai yin wannan kashin, ai kuwa sai ga dila ya gitta ta wurin, har ya sake yin irin wannan kashin. Sai nan take kura ta fito ta ce ashe kai malamin daji kai ne kake yin kashin nan? Bayan ta cinye wannan sai ta ce ma dila “malam ƙaro kashi”, Dila ya ƙara kashin, kura ta lashe, ta sake cewa ya ƙara, haka dai suka cigaba da yi har dila ya kai baya iya yin wani kashin! Sai kura ta ce da shi sai ya kai ta inda yake shan wannan shagalin da har yake irin wannan kashi mai daɗin ɗanɗano. Dila bai tsaya wata gardama ba saboda sanin halin kura sai ya shiga gaba kura ta bi shi, bai tsaya ba sai gidan Fulani inda yake shan ƙwai.

            Dila yana ganin ƙwai sai ya ce: 

“Na ga kwarkwatatta wurin ɗibar kwamma”

          Sai kura ta ce:

“Kwashangyalat, aje shi nan, ni na aje shi

Dole sai dila ya bar ma kura ƙwan ta shanye! Ana haka duk lokacin da dila ya ga ƙwai sai kura ta ce nata ne, dole dila ya bar mata ta shanye. Dila dai bai sha ƙwai ko guda ba. Ana cikin haka sai dila ya hangi ƙwai a cikin kogon itace, sai ya ce:

“Na ga kwarkwatatta wurin ɗibar kwamma”

Sai kura ta ce:

“Kwashangyalat, aje shi nan”

Sai kuwa kura ta ce ai dama ita ta ce a aje mata shi a nan, rayuwar dila ta ɓaci sosai, kura ta hana shi ya yi kalaci!

Kura ta duba cikin kogo ta ga ƙwai, ta kara kanta amma kash! Kan kura ya ƙi shiga kogon! Sai ta roƙi dila ta ce malamin daji a yi man addu’a don kaina ya shiga cikin kogon nan. Sai ya ce to, ya yi mata burga, ya samo wani ganye mai yauƙi, ya shafa wa bakin kogon, sannan ya ce kura ta gwada a gani, aza kan kura ke da wuya sai dila ya dawo bayanta ya daddage ya tura ta har kan ya shige, daga nan sai ya ɗebo yashi ya goge yauƙin nan da ya sa, sannan ya koma baya ya ɗauko gangarsa ya fara kiɗin farauta! Sai kuwa ya sake murya ya ce “kai jama’a ku yo gaba ga dila cikin ƙaya!” Ya kuma sake murya yana cewa kai dilan mi ga kura kogo! Ai kuwa sai dila ya sami faskare lafiyayye ya fara jibgar kura, kura ta yi duk irin yunƙurin da take yi ta fito kanta ya ƙi fita, shi kuwa dila sai kiɗi yake yi yana jibgar kura tana zawo.

TATSUNIYAR DILA DA KURA

Sai can kura ta fizga kanta da ƙarfi ta fito da shi duk fatar kanta ta kware, ai kuwa bata tsaya wata-wata ba sai ta arce a guje ta nufi gidanta. Shi kuma dila ya bi ta ‘yar kurɗe ya riga ta gidan, ko da ta zo sai dila ya ce yau mun sha kashi! Kura ta ce ai naji lokacin da ake cewa mi muke yi da dila a cikin ƙaya ga kura kogo? Ita ba ta san dila ne ya doke ta ba. Sai dila ya ce sai an jima, ya tafi ya bar kura tana jinyar dukan da ta sha, da kuma kwarewar da kanta ya yi.

Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

Tambayoyi

1.                  Ko kun yarda cewa shagali na sa a yi kashi mai daɗi?

2.                  Wane sakamako kura ta samu a kan zaluncin da ta yi wa dila?

3.                  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?

Post a Comment

0 Comments