Ticker

6/recent/ticker-posts

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Gatanan – gatananku

Wani malami ne yake zaune a wani gari wanda yake da rufin asiri, kuma kowa yana mamakin wannan rufin asirin nasa saboda shi dai ba ya yin aikin komi, kuma ba ya da wata sana’a sai karance-karancensa kawai. Abinci kuwa a gidan malam sai kowa ya ci ya bari. Babban abin mamakin mutanen wannan gari shi ne; malam ba ya saye, balle sayarwa, ba ya zuwa ko’ina balle ya biɗo abinci.

Wannan lamari na malam ya cigaba da ba kowa mamaki. Ashe malam wata addu’a ce yake yi sai abinci ya faɗo masa daga sama kowane iri yake so! Da zarar ya so tuwo sai ya ce “Tuwo tutui-tutui” sai ko tuwo ya yi ta saukowa har sai ya ishi kowa.

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Idan kuma ya sake buƙata sai ya yi haka, babu wata matsala da ta dami malam sai dai ya yi ta karatunsa. Ko da ya gaji da wannan sai wata rana ya je a rafin da ke bayan garin ya faɗa ya tsamo wani yaro ya zo da shi gida, amma kafin ya je gida da shi sai ya tambaye shi “mene ne sunaka” yaro ya ce “suna na girgiza mani” sai ya ce “ya ya kake da wannan sunan?” Sai yaro ya ce ai da mutum ya ambaci sunana sai kawai in riƙa girgza kaina hatsi na zuba! Nan take sai malam ya ce “girgiza mani” sai kuwa ya fara girgiza kansa dawa ta fara zuba! Sai da malam ya tsayar da shi.

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Sai malam ya tambaye shi cewa; “mice ce al’adarka idan ana son a ajiye ka?” Sai ya ce idan ana so a aje shi, sai an sami yashi mai kyawo, a sa shi a wuri mai kyawo, a riƙa jiƙe shi da ruwa mai kyawo sannan a sa ni ciki in zauna”, sai malam ya ɗauke shi ya kai shi gidansa, ya sami wani ɗaki mai kyawo ya sa shi, ya bi duk ƙa’idojinsa. Duk lokacin da ya so hatsi sai ya shiga ɗakin ya ce masa “Girgiza mani” sai shi kuma yaron ya yi ta girgiza kansa dawa tana zuba! Sai ya kwashe ya tara, abinci ya samu.

Ana nan-ana nan sai labarin wannan malami ya kai ga sarkin garin cewa ga hidimar da yake yi wa yaro, shi kuma yaro yana samar masa da abinci kowane iri yake so, sai sarki ya sa aka ɗauko masa shi, ya tambaye shi cewa wannan maganar da ya ji ko gaskiya ce? Malam ya ce “haka ne,” sai sarki ya ce “to a zo da yaron in gani da idona”, aka kawo yaron a ƙofar gidan sarki, malamin ya ce masa “Girgiza mani” sai kuwa sarki ya ga tsaba na zuba babu ƙaƙƙautawa[1]! Da ganin haka sai sarki ya kwace yaron ya ce a gidana ne ya fi dacewa, ya sa aka kori malam!

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Sarki ya sa aka gina ma yaro sabon ɗaki ya sa shi a ciki amma bai bi ƙa’idojin yaro ba kamar yadda malam ya yi. Da farko yaro ya fara girgiza ma sarki har ya huta da sayen dukan kayan abinci, amma da zafi ya dame shi wata rana sarki na buɗe ƙofa sai kawai yaro ya fito aguje! Sarki bai yi wata-wata ba sai ya biyo shi da gudu.

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Da zuwa rafi sai kawai yaron ya faɗa a ciki, sai kuwa sarki ya ce da wa aka haɗa ni ba da kai ba? Shi ma ya faɗa ruwa ya bi shi don ya kamo shi, bai daɗe da shiga ba sai ya lalabo yaro, amma kash! Ba wancan da ya gudo ba ne. Ko da ya fito da shi bai tsaya koina ba sai cikin ɗakinsa, ya yi, ya yi amma yaro ya ƙi yin komai! Sai ya sa fadawansa da su nemo masa malam duk inda yake. Fadawa suka bazama wajen neman malam har suka gano shi, suka zo da shi gaban sarki.                          

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Sarki ya ce wa malam ya gaya masa yadda ya yi a lokacin da ya sami yaron nan. Malam ya ce masa, lokacin da na tsamo shi cikin ruwa sai da na tambaye shi sunansa, sannan na tambaye shi al’adarsa. Da jin haka sai sarki ya gane kuskurensa na rashin binciken yaron, sai ya ce a saki malam, aka sake shi ya tafiyarsa.

Sarki ya tafi wajen yaronsa, ya ce “kai yaro mene ne sunanka?” sai yaro ya ce “sunana Ƙwaƙƙwala mani” Sarki ya ce “To yaya al’adarka take?” sai yaro ya ce “Ɗaki ake sa mu ni da wanda ya tsamo ni a kulle kar a buɗe sai mun ƙare da shi, komai aka ji yana faruwa” Sarki ya ƙara gyara zama, ya ce wa fadawansa “a rufe mu ni da yaro a cikin ɗaki, komai aka ji kar a buɗe sai mun buɗe da kanmu”.

Bayan an yi hakan sai sarki ya ce “Ƙwaƙƙwala mani” ai kuwa sai yaro ya sa kulki ya yi ta ƙwala ma sarki, sarki yana ta ihu amma yaro ba ya kula jibgar[2] sarki kawai yake yi! Tun fadawa suna jin ƙarar sarki har suka ji shiru!

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Sai da yaro ya ga sarki ya bar motsi sannan ya buɗe ƙofa ya ruga aguje ya faɗa ruwa a inda sarki ya tsamo shi.

Shi kuma malam da ya wuce sai ya koma rafi ya sake kamo yaronsa na farko, ya kuma koma gidansa na da, ya cigaba da yi masa kamar yadda ya saba. Sarki ya mutu saboda jibgar da yaron ya yi masa! Sai mutanen gari suka ce; wa za su ba sarautar garin ba malam ba?

Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

Malam ya zama sarkin garin ya kuma cigaba da kyautata ma jama’ar garin kamar yadda yake yi a da, kowa ya yi murna, har wasu talakawa da fadawa sukan ce sun haɗu da lailatul ƙadari, don ya hi tsohon sarki!

Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

Tambayoyi

1.                  Mene ne sunan yaron da malam ya tsinto? Kuma mece ce al’adarsa?

2.                  Waɗanne dalilai kuke ganin suka sa yaro ya gudu daga gidan sarki?

3.                  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?
[1]  Saurarawa/dakatawa.

[2]  Duka da wani babban abin bugu.

Post a Comment

0 Comments