Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Kai Kara Ta Wajen Iyayenta Wai Ba Na Ciyar Da Ita, Kuma Wallahi Karya Take

TAMBAYA (97)

Assalamualaikum mallam. Ina kwana, dafatan katashi lfy mallam, inna niman fatawa cikin wannan al'amari.

Matana ne ta tafi gidansu ta yi wa ma'aifiyanta karya wai bana ciyar da ita, ah hallin ba haka bane wallahi wallahi wallahi mallam babu randa ba ayin abinci agidana saidai randa idan taqiyi, mallam tsakani da Allah abinda yashiga tsakanin mu shine kamar haka

1) na hanata yin sana'ar ta na kwaliya sabida bata zama agida kuma bata yimin abinci, intayima ba akan lokaciba wani sa'in idan aikin agida zatayi sai nadawo gida sai na tsinci yan mata wani 1 wani 2 wani 3 duk dai inda yaka kuma da zanuwa aqirijin su Kuma baligai

2) saikuma saniya da muka hada kudi zamu yanka da Sallah sai yanaso yakasa sai muka yanka ana Sallah sauran sati 1 nakawo mata nace da ita tasoya naman nam ta'ajiye dashi zamuyi hidiman Sallah amman se ta rabar da naman duka ga yan mata masu zuwa gujin ta aiki. Kurum ranar Sallah da tatafi masallacin idi bata dawo gidana ba yanzu haka tana gurin ma'aifiyanta domin ma'aifinta ya mutu. Mallam atemaka min da mataki daya dace na dauka bissalam nagode

Mallam wallahi wallahi wallahi wannan shine Dining dinmu dakuma kitchen dinmu ah haka wai bana ciyar wa

AMSA

Waalaikumussalam, warahmatullahi, Wabarakatuh

Lahaula wala quwwata illa billah

To dan uwa, indai har yanda ka fada dinnan haka maganar take to abinda ta aikata bai dace ba

Dangane da sana'ar da take yi, indai har zata dinga fifita neman kudi ta hanyar yin kwalliya akan yi maka biyayya wajen aiwatar da ayyukan gida kamar irinsu girki da sauransu to wannan ta jahilci yanda ake rayuwar zamantakewar auratayya a bisa koyarwar shari'ah

Duk abinda yake kawo irin wadannan matsalolin shine: rashin halartar makarantar yanda ake rayuwar aure a shari'ance a musamman a lokacin da aka sakawa mace rana. Daga sanda aka ce an kusa bikin mace to kamata yayi ta shiga makarantar koyar da zamantakewar aure don ta samu ilimin da zata zauna da mijinta lafiya kamar yanda matan Annabi Sallallahu alaihi wasallam suka zauna dashi

Kana da qwaqqwarar hujjar da zaka hanata sana'ar nan saboda ko iya kallon mace baliga mai daurin kirji bai halatta ba, tunda kafadunta suma al'aura ne. Kuma majority idan mata sun hadu a gidan kwalliya ko kunshi ba hirar lahira ake yi ba ko kuma abinda ke faruwa a cikin kabari, saidai abinda aka fi yi shine; tsegumi, gulma da munafurci kuma idan itama matar mara wayo ce sai ta dinga fallasa asirin mijinta a gaban wadanda takewa kwalliyan wanda cin naman mutum kuma haramun da nassi a cikin Qur'ani da Allah Azzawajallah yace

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ )

الحجرات (12) Al-Hujuraat

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.

Haka kuma idan sana'ar kwalliya din da take yi ya shafi har irinsu make up to da kuma saka man bleaching to wannan haramun ne saboda canza halittar Allah ne, kuma daman Iblis ya dauki alqawarin sai ya sa mutane sun canza halittar da Allah yayi musu, kamar yanda Allah Subhanahu wata'ala ya labarta mana a cikin Qur'ani;

( وَلَأُضِلَّنَّهُمْ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمْ وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُبَتِّكُنَّ آذَانَ الْأَنْعَامِ وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلْقَ اللَّهِ ۚ وَمَن يَتَّخِذِ الشَّيْطَانَ وَلِيًّا مِّن دُونِ اللَّهِ فَقَدْ خَسِرَ خُسْرَانًا مُّبِينًا )

النساء (119) An-Nisaa

"Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.

Kuma masana kiwon lafiya sunce "Yin kwalliyar bleaching yana kawo cutar Glaucoma (Hawan jinin ido)". Wannan qalubale ne ga masu canza halittar Allah. Dadin dadawa kuma bai halatta a kira ta kwalliya wani wajen ba, ba tare da ta nemi izininka ba

Duk wadannan hujjoji ne akan abinda ya shafi sana'ar da take fifitawa akan Ibadah wato zaman aure

Dangane da batun watandar saniya da kukayi tare, shima bai kamata ta rabar da naman gaba daya ga customers din ta ba, ko da ace tayi hakanne don ihsani to amman shaidan zai iya rinjayarta ta basu don ta kara jan su a jiki saboda sana'ar nan da take yi, abinda yafi dacewa shine ta rabawa makusantan ta musamman la'akari da cewar su marayu ne kamar yanda kace mahaifinta ya rasu, ka ga sune suka fi cancantar naman sallar bawai masu zuwa kwalliya ba

Wasu matan basu da godiyar Allah, yanzu ace wannan shine kitchen da kuma dining table din gidanka (Tabarakallah, kamar yanda na ga ni a video din da ka turo) amman ace bazata yi maka girki yanda kake so ba, alhalin wasu matan basu samu rabin-rabin irin wannan ba, kuma ga halin da ake ciki na tsadar rayuwa

Wannan kadan kenan daga cikin halayen wasu matan. Kuma shiyasa ma wasu mazajen suke saka sharadi kafin su auri mace akan cewar ba zata yi aiki ba, wasu mazan ma suna dauke nauyin biyan matan sana'ar da suke yi, duk wata

Dangane da matakin da zaka dauka, shawarar da zan baka anan itace; ka qyaleta ta ci gaba da zama a gidan nasu, tunda ai macen da aka saketa ita ake biko kuma kai baka sake ta ba, idan ta gaji da zaman gidansu dole wataran zata kiraka a waya. Kamar yanda wata baiwar Allah itama ta je gida, lokacin da suka samu matsala da mijinta karshe sai ga ta tana yi masa flashing a waya saboda ta gaji da zaman gidannasu. Sai ga ta ba shiri ta koma tana bawa mijin haquri

Kaima kada abin ya daga maka hankali. Kuma kada shaidan yayi nasara akanka kace zaka saketa, saidai ko da ta dawo to ka saka mata sharudda. Idan kuma waliyyanta sun kira ka sai ka je kayi musu bayani. Amman idan ba wanda ya kira ka, kawai ka ci gaba da zuba ido ka ga iya gudun ruwanta tunda ai igiyar aure a hannunka take ba a hannunta ba

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments