Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Garba Bai san wuyag gargare ba
Garba Bai san wuyag gargare ba mutumen garin Kalgo ne ta
cikin yankin Sabonbirni. Yana noma ƙwarai da
gaske kuma ya sami rufin asirinsa ta hanyar noma, Amali ya yi masa waƙar noma ne domin irin faɗi-tashinsa
a harkar noma.
G/Waƙa : Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa[1],
: Namijin da noma ka wa haske.
Jagora : Allah ka
bar man masoyana.
‘Y/Amshi: Ya Allah ka bar muna mijin
: daga,
: Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske,
Jagora: Sannu da lubta[2]
kalme ga yashi,
‘Y/Amshi: Sannu
da assako[3] ɓurgujen
laka.
: Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske,
Jagora : Sannu da
jehwa kalme ga turɗa[4]
‘Y/Amshi: Sannu da assako ɓurgujen laka
Jagora : Na gode
Allah da Annabi,
: Na gode girman
manoma,
: In na yi taggo
da riga,
: Albarkacin masu
kafce,
: In ka ga ƙube ga kaina,
: Albarkacin
masu huɗa,
: In na yi zoben
azuhwa,
: Albarkacin
masu ƙwazo,
: In na yi mata
na wari,
: Albarkacin
masu kaibe
: Na gode Allah
da Annabi,
: Na gode girman
manoma,
‘Y/Amshi: Ba mu rena girman manoma ba,
: Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske.
Jagora :
Kui aniya ku saba da kafce,
: Kun san biɗa ba ta ƙin ku,
: In ka ga yaro
da wandon yadi,
: Da taggo[5] da
riga,
: Hak kag ga ƙube ga
kainai,
: Ka tabbata ya
yi kafce,
: Ka san ba ya
samun su kyauta.
‘Y/Amshi: Allah
baya yin wane kan banza.
: Bai damu yin
gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske.
Jagora : Kui aniya
ku saba da ƙwazo,
: Kun san biɗa bata ƙin ku,
: In ka ga yaro
da mata tcadadda,
: Tana runguma
tai,
: Hannunta na
lalaba tai,
: Ya yi baƙi ƙirin da baƙin lalle.
: Abu dai kamaz zai karewa,
: Allan ko baran bai karewa,
: Nonnonta na inguza tai,
: Ka tabbatar ya yi gabce,
: Ka san ba ta iske shi kyauta,
‘Y/Amshi: Sai an sha wuya za a shan daɗi.
: Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske.
Jagora : Sai an
sha wuya za a shan daɗi,
: Ka san,
‘Y/Amshi: Sai
an sha wuya za a shan daɗi.
: Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske.
Jagora: Ni niz zo gida ni ishe shi,
: Nik ko taho lahiya lau,
: Nik ko iso lahiya lau,
: Nig ganai lahiya lau,
: Shi yag ganan lahiya lau,
: Yab bani taggo da riga,
: Gami da ƙube da
wando,
: Gami da dokin hawowa,
:
Gami da kuɗɗi tamanin,
:
Ni godiya ɗai nikai
mai,
:
Kuma shi godiya
ɗai shi kai,
:
Kuma had da
hwata[6]
shinai man,
:
Wada kat
taho lahiya lau,
:
Ka zo gida
lahiya lau,
:
Don
albarkacin mai iyawa,
:
Sarkin nan
da yab busa sheɗa[7],
:
Don
albarkacin Annabi nai,
: Don darajjar Abu mai riƙonmu,
:
Garba
naukku sarkin Musulmi,
‘Y/Amshi: ‘Yan amin ku amsa muna hwata.
: Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can za mu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske.
Jagora:
Bankwana
yana bani tausai,
:
Da sunka zo
rakkiya ta,
: Nid dibi jam’in mutane,
: Za ni rabo da huskam
masoyana,
: Sai zucciya taj jiye man,
: Ka san ba ƙashi ag
gare ta ba,
: Sai niɗ ɗora ƙyallin hawaye,
: Sai wataran da ku masu so na,
: Ko mu game da ku masu so na,
: Ko ko dai ya zan ba gamewa,
: Saboda ban san da rai ba,
: Hakanga na ba
ni tsoro,
‘Y/Amshi: Bai san wuyag gargare ba,
: Ga Garba can zamu jiɗa,
: Namijin da noma ka wa haske.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.