Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Noma Amadu Kwatta

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Sarkin Noma Amadu Kwatta

 

 G/Waƙa: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

 

Jagora: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

  ‘Y/Amshi: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

 

Jagora: Ga Bunguɗu local gamman[1] ,

: Ko can gidan ku dawa take shirge[2].

‘Y/Amshi: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

 

Jagora: Ga Bunguɗu local gwamman.

  ‘Y/Amshi: Ko cen gidan ku dawa take kimshe.

 

 Jagora: Ga Bunguɗu local gwamman.

 ‘Y/Amshi: Ko cen gidan ku dawa take kimshe,

: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

 

Jagora: Na Hauwa kana,

: Gamanuwa kai dai ka kare,

: Aikin dawa sosai.

  ‘Y/Amshi: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

 

 Jagora: Na Hauwa kana gama noma.

  ‘Y/Amshi: Kai ɗai ka noma aikin dawa take.

 Jagora: Na Hauwa kana gayyatowa.

  ‘Y/Amshi: Kai ɗai kana noma aikin dawa take.

Jagora: Gwarzo mu mukai shiryayye.

  ‘Y/Amshi: Shiɗai ka noma aikin dawa take.

 

 Jagora: Gwarzo mu mukai shiryayye. 

  ‘Y/Amshi: Shiɗai ka noma aikin dawa take.

 

 Jagora: Gwarzo Abubakar shiryayye.

  ‘Y/Amshi: Shiɗai ka noma aikin dawa take.

 

 Jagora: Na yi godiya gun Kaka.

  ‘Y/Amshi: Albarkacin ka hairan yaka zakka.

 

 Jagora: Na yi godiya gun kaka.

  ‘Y/Amshi: Albarkacin ka hairan yaka zakka.

 

 Jagora: Muttala Amadu na gode mai.

  ‘Y/Amshi: Albarkacin ka na amadu Kwatta,

: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

 

 Jagora: Na Hauwa ko da ɗai,

:Baka da wasa ranar ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Ba ka da wasa.

 

 Jagora: Na Hauwa ka da ɗai ba ka.

  ‘Y/Amshi: Ranar kwazo ba ka da wari[3].

 

 Jagora: Na Hauwa maganin masu Turuci.

  ‘Y/Amshi: Ranar ƙwazo ba ka da wari.

 

 Jagora: Muttala Amadu na gode mai.

  ‘Y/Amshi: Albarkacin ka Amadu Kwatta,

: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.

 

Jagora: Muttala Amadu na gode ma.

  ‘Y/Amshi: Albarkacin ka Amadu Kwatta,

: Sarkin noma Amadu Kwatta,

: Barden Salau mai gama gayya.[1]  Government wato ƙaramar hukuma.

[2]  Tattare yana nufin an tara da yawa.

[3]  Sa’a wanda yake daidai da shi.

Post a Comment

0 Comments