Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Alhaji Nahantsi
G/Waƙa:
Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Sai azzahar ka
tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
‘Y/Amshi:
Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Sai azzahar ka
tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Wamakko zani na ɗan kurma.
‘Y/Amshi: Domin in ishe ma zad daɗi,
: Sai
azzahar[1]
ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Alhaji Nahantsi
bakin kusu.
‘Y/Amshi:
Maza basu ja da kai ran noma.
Jagora: Wamakko zani na Ɗan
kurma.
‘Y/Amshi: Ga manyan ma’aikata zad daɗi.
Jagora: Wamakko zani na ɗan kurma.
‘Y/Amshi: Ga manyan ma’aikata zad daɗi,
: Sai
azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Ɗan
Garba maza.
‘Y/Amshi: Basu ja[2]
da kai ran noma.
Jagora: Ɗan
Garba maza.
‘Y/Amshi: Ba su ja da kai ran noma.
Jagora: Ɗan
yahaya aiki yakai gabaɗai gona.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Sai azzahar,
‘Y/Amshi: Ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Wamakko zani na Ɗan
kurma.
‘Y/Amshi: Ga manyan ma’aikata zad daɗi,
: Sai
azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: ‘Yau Wanakko zani
na ɗan kurma.
‘Y/Amshi: Ga manyan ma’aikata zad daɗi,
: Sai
azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Sarkin yaƙin
Nahantsi bakin kusu.
‘Y/Amshi: Maza ba su ja da kai ran noma.
Jagora: Sarkin yaƙin
Nahantsi bakin kusu.
‘Y/Amshi: Maza ba su ja da kai ran noma.
Jagora: Hussaini direba na
gode ma.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabaɗai kullun[3].
Jagora: Hussaini direba na gode ma.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gaba ɗai kullun.
: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Hussaini majema yai man ƙwazo.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabadai kullun.
Jagora: Hussaini majema yai man ƙwazo.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabadai kullun.
Jagora: Babban direba na gode mai.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gaba ɗai kullun.
Jagora: Almu direba na gode mai.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gaba ɗai kullun.
Jagora: Almu direba nag ode mai.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gaba ɗai kullun,
: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Ni nayi godiya gun Amadu.
‘Y/Amshi: Hairan ya kai gabaɗai kullun.
Jagora: Amadu Kwatta rannan ya kyauta
man.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabaɗai kullun,
: Sai
azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Sani sifawa na gode ma.
‘Y/Amshi:
Hairan yakai gabaɗai kullun.
Jagora: Sani Sifawa na gode ma.
‘Y/Amshi:
Hairan yakai gabaɗai kullun,
: Sai
azzahar[4]
ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Na Illela na yaba mai girma.
‘Y/Amshi:
Hairan yakai gabaɗai kullun.
Jagora: Muhammadu Illela na yaba ma kai
ma.
‘Y/Amshi:
Hairan yakai gabaɗai kullun.
Jagora: Malan Abubakar na gode.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabaɗai kullun.
Jagora: Malan Haruna na
gode mai.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabaɗai kullun.
Jagora: Shi Haruna Dauran ya kyauta
man.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabaɗai kullun.
Jagora: Mamman Dauran na gode mai.
‘Y/Amshi: Hairan yakai gabaɗai kullun.
Jagora: Yau Inugu zamu taron gona,
:
Niyya mukai ga Sakkwato birni.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Mu Inugu zamu
taron gona.
‘Y/Amshi: Niyya mukai ga Sakkwato birni,
: Sai
azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Yau Inugu za a
taron gona.
‘Y/Amshi: Niyya mukai ga Sakkwato birni.
Jagora: Yau Inugu za a taron gona.
‘Y/Amshi: Niyya mukai ga sakkwato birni,
: Sai
azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.x2
Jagora: Inyamurai suna
dibin,
: Da
manyan ma’aikata sun taso.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Inyamurai suna
dibin,
: Da
manyan ma’aikata sun taso.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.x2
Jagora: Inyamurai suna dibin,
: Da
manyan ma’aikata sun taso.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: In ko tare da noma
kai gudu,
:
Moro kada kaja mai girma.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Inko tare da noma
kai gudu,
:
Moro kada kaja mai girma.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: In ko tare da noma.
‘Y/Amshi: Kai gudu Moro kada kaja mai girma.
: Sai
azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Kai Abubakar masu ja da kai sun
yi ƙarya.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona.
Jagora: Kai Abubakar masu jah dakai ran
noma.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Ɗan
Garba maza basu jah da kai ran noma.
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
Jagora: Ɗan
Garba maza basu jah da kai ran noma,
‘Y/Amshi: Sai azzahar ka tassai gona,
:
Alhaji Nahantsi sarkin noma.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.