Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Salon Jinsintarwa a Waƙoƙin Amali
Jinsintarwa dabara ce inda akan yi kwatancen ta fuskar jinsi wato a ɗauki halayyar wani jinsi a ba wani jinsin daban. Ɗangambo, (2007:45).
Jinsi shi ne iri, wato irin wani abu kamar halitta wanda ya bambanta shi da sauran irinsa. Misali jinsin mutum ko jinsin dabba da dai sauransu. A jinsantarwa ana ɗaukar halayya ko ɗabi’ar wani jinsi a saka wa wani jinsi da ba a san shi da irin wannan halayya ko ɗabi’a ba. Ana irin wannan ne domin ɗaukakawa ko ƙasƙantawa gwargwadon manufar salon mawaƙi. Akwai jinsi iri-iri da ya haɗa da na mutum ko dabba ko ƙwari ko tsirrai da sauransu. Masu nazarin adabi suna amfani da salo iri uku na jinsantarwa: mutuntarwa da dabbantarwa da abuntarwa.
Yanzu za mu ɗauke su ɗaya bayan ɗaya mu zaƙulo misalansu daga cikin ɗiyanwaƙoƙin Amali Sububu don daɓenmu ya ji makuba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.