Ticker

6/recent/ticker-posts

Saki A Rubuce Da Saki A Zuciya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam. Mace ce mijinta ya rubuta mata saki biyu a takarda, sannan kuma kwanakin baya ya ce ya ƙudurta saki a cikin zuciyarsa amma bai faɗa mata ba. Da aka tambaye shi, sai ya ce wai da wancan na rubutu da wannan da ya ƙudurta guda biyu kenan. To, wai yaya abin ya ke?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Da farko dai Malamai sun yarda cewa: Wanda ya rubuta wa matarsa saki, to sakin ya tabbata matuƙar dai ya yi niyyar hakan. Haka aka riwaito daga Al-Hasanul Basariy, da Shaabiy, da Ƙataadah, da Abu-Haneefah, da Maalik, da Shaafiiy, da Laith Bn Saad da sauransu (Rahimahumul Laah).

Amma wanda ya yi saki a zuciyarsa ba tare da yin furuci da baki ba, sakinsa bai auku ba. Haka Abdurrazzaaƙ As-Sanaaniy ya riwaito da isnadi sahihi daga Al-Imaam Ƙataadah. Dalilin wannan kuwa shi ne maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)

Tabbas! Allaah ya yafe wa al’ummata abin da suka yi tunani a cikin zuciyarsu matuƙar dai ba su yi magana ko aiki da shi ba.

Daga nan muke iya fahimtar cewa:

1. Sakin da wannan mijin ya yi wa matarsa ta rubutu ya tabbata tun da dai shi da kansa ya tabbatar da shi.

2. Sakin da ya yi a zuciyarsa ma ya tabbata saboda bayaninsa ya bayyanar da abin da ya ƙudurta a zuciyar.

3. Game da sakin da ya yi a rubuce kuwa: Shin ko mutum yana iya sakin matarsa fiye da sau ɗaya a lokaci guda kuma a zartar masa? Malamai sun sha bamban a kan wannan. Sahihiyar maganar da hujjojinta suka fi bayyana a wurinmu ita ce: Saki ɗaya ne kawai miji ke iya yi a lokaci guda, ba zai iya ƙarawa ba sai bayan ya komo da ita, kamar yadda As-Shaikh Ahmad Shaakir (Rahimahul Laah) ya tattauna a cikin Nizaamut Talaaƙ Fil Islaam.

A taƙaice dai, wannan miji ya saki matarsa saki biyu kenan: Na rubutu da na zuciya wanda ya bayyanar daga baya. Sai ya yi taka-tsantsan, kar ya kuskura ya ƙara saki ɗaya kuma, domin idan ya yi, to ba shi da ikon dawo da ita har sai ta auri wani mijin da ba shi ba, kamar yadda aya ta nuna.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aƘZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments