𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh. malam
ina maku fatan alkhairi akan irin gudun mowarku a garemu, malam don Allah
wadanne sharuɗa ne
akeso hijabi ya cika sannan mace musulma ta sanya shi a matsayin hijabinta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.
Na'am lallai
'yar uwa kinyi tambaya mai fa'idah wacce yakamata ace kakaf ɗin iyayen mu sunyi wannan nazarin akan
wane irin tufafi ya kamata su dika sanya wa a matsayin su na musulmai (matan
aure da 'yan mata).
Hijabin mace musulma yana da sharuɗa guda 6-8 wanda malamai suka ce duk wani
hijabi da mace zatasa matukar bai cika waɗannan sharudda ba to gaskiya baza'ace masa hijabi
ba sai dai a nemo wani suna a saka mashi amma wannan ba Hijabin da Allah yayi
umarni cewa a sanya bane, to yaya matan mu a yau suke!!!?
1. Hijabin mace ya kasance babba ne wanda zai
lulluɓe mata
jiki kamar yanda ayar Al-Ƙur'ani
tayi mana nuni da haka acikin Suratun-Nur aya ta 31:
... ۖ وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ ۖ ...
kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu.
wanda idan ta sanya shi zai kasance baya nuna
komai sai fuskar ta da tafin hannun ta amma dai ta tabbatar babu kwalliya
ajikin fuskar ta!
2. Hijabin
ya kasance babu wani zane na kwalliya da zaija hankalin mutane har su kalleta,
kawai ya kasance idan ta sanya farin Hijabi to kawai fari ne babu wani abu na
kwalliya akansa, kamar yanda ayar Al-Ƙur'ani mai girma ta nuna mana acikin Suratul
Ahzaab aya ta 33:
...وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَىٰ ۖ ...
kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar
gãye-gãye ta jãhiliyyar farko.
3. Kada Hijabin ya kasance ɗangyalalle ko kuma anyi masa wani kalar ɗinki ko kuma ya kasance shara-shara ko
kuma ya ɗame jiki,
domin wannan yana kai mace wuta kamar yanda Imamu Addabaraniy ya ruwaito
sahiihin hadisi akan haka.
4. Ya
kasance ajikin wannan Hijabin babu turare domin Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi yace mai wannan mugunyar hali na sanya ma kayanta turare
ta fita waje wajen da maza suke domin suji kamshi hukuncin ta kamar mazinaciya
ce, Kamar yanda Imam Ahmad da Baihaƙiy da Imam Tirmidhiy da wasun su suka ruwaito
ingataccen hadisi.
5. Kada wannan Hijabin ko kayanta yayi kama da
kayan maza kamar sanya wando da hula da sauran su, Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi yace, Allah ta'ala ya tsine ma dukkan namiji da yake
kamacece niya da mata, kuma ya tsine wa dukkan mace wacce take kamacece niya da
namiji" kamar yanda Abu-Dawud da waninsa suka ruwaito.
6. Kada tufafin yayi kama da kayan kafirai arna,
ko kuma wata kamacece niya tsakanin su, domin Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi yace Duk wanda yayi kamaceceniya da waɗansu mutane to shima ya koma cikin su.
Ƴar'uwa ta waɗannan Suna daga cikin sharudda da Shari'ar
musulunci tayi maki tanadi domin kiyaye mutuncin ki, shin ƴar'uwa ta haka Hijabin
ki yake!!!? Zaman lafiya shi ne idan kayi ilimi wato kasan abu to kayi aiki dashi,
Allah ta'ala ya shiryar damu, Allah yasa mudace.
Duba Jal' baabul-Mar'atil-Muslimah na Albany, ko
kuma Littãfin Fiƙhul-Muyassir
na Sa'ad Yusuf shafi na 310-311
WALLAHU A'ALAM
Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.