Ticker

6/recent/ticker-posts

Hatsarin Riya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Don Allaah, ina da tambaya: Wai mecece riya? Wane abu ne idan mutum ya yi shi ya zama riya? Don Allaah, ina neman ƙarin bayani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Kalmar riya asalinta balarabiya ce, watau daga harshen Larabci ne Hausawa suka samo ta, kuma ma’anarta a wurin malaman Aƙida da Tauhidi ita ce: Yin wani aikin ibada na-Allaah, kamar Kalmar Shahada ko Sallah ko Zakkah ko Azumi ko Hajji ko Sadaka ko Tilawa ko Zikiri ko Kyautatawa ga iyaye da marayu da talakawa da maƙwabta da sauransu, amma ba don Allaah ba, sai domin kawai mutane su gani su yabe shi! Wannan mummunan zunubi ne daga cikin manyan Kabairai da aka ba shi matsayin Shirka Ƙarama, in ji malamai.

A ƙarshen Suratul Kahf Allaah Taaala ya ce:

فَمَنْ كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا

Duk wanda yake ƙaunar haɗuwa da Ubangijinsa to sai ya aikata ayyuka na-gari, kuma kar ya haɗa kowa a cikin ibadar Ubangijinsa.

Sannan Al-Imaam Al-Haakim ya riwaito Hadisin da Al-Haafiz Az-Zahabiy ya dace da shi wurin sahhaha shi a bisa Sharaɗin Al-Bukhaariy da Muslim daga Sahabi Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa:

Wani mutum ya faɗa wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa: Ni, ina tsayawa a wani irin matsayin da ina neman Fuskar Allaah, a lokaci guda kuma ina neman mutane su ga irin wannan matsayin. Amma sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai ba shi wata amsa ba sai da wannan ayar ta sauka.

Abin da ya wajaba dai ga mumini shi ne: Duk lokacin da ya tashi yin wani aiki sai ya tsarkake niyyah tun daga zuciyarsa saboda Allaah shi kaɗai kawai. Haka Ubangiji Ta’aala ya yi umurni:

وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ

Kuma ba a umurce su da komai ba sai dai su bauta wa Allaah, suna masu tsarkake addinin gare shi.

Aiki kuwa ba ya zama na-gari (Amalun Saalih) in ji Malamai, sai ya cika waɗansu muhimman sharuɗɗa guda biyu:

1. Ya zama an tsarkake zuciya a wurin yin sa, watau a yi shi ne tsantsa saboda Allaah shi kaɗai. Wannan shi ne: Ikhlaas, wanda yake kawar da shirka.

2. Ya zama an bi koyarwa da karantarwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a wurin yin aikin sau-da-ƙafa. Wannan ne kuma shi ke kawar da bidia.

3. Wannan irin ɗabi’a ta yin riya a cikin ayyukan ibada siffar munafuƙai ne waɗanda ba su yi imani na-gaskiya da Allaah da Ranar Lahira ba, kamar yadda Allaah ya yi bayaninsu a cikin Suratul Maa’uun. Sannan kuma a cikin Suratun Nisaa’i ya siffata su da cewa:

وَإِذَا قَامُوا إِلَى الصَّلَاةِ قَامُوا كُسَالَى يُرَاءُونَ النَّاسَ وَلَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ إِلَّا قَلِيلاً

Kuma idan suka tashi zuwa ga sallah sai su tashi cikin kasala, suna yin riya ga mutane, kuma ba sa tuna Allaah sai ɗan kaɗan.

A ƙarshe dai a wurin ƙarin bayani da fayyace komai da komai da kuma bayar da hukunci, sai malamai suka karkasa ayyukan da riya take shiga cikinsu gida-gida, kamar haka:

1. Idan ya zama abin da ya zaburar da mutum ga yin aikin tun farko don ya nuna wa mutane ne, ba don neman Fuskar Allaah Maɗaukakin Sarki ba, to wannan aikin ya zama shirka kai-tsaye kuma aikin ɓatacce ne.

2. Idan kuma da farko mutum ya mike domin yin ibadar saboda Allaah ne amma kuma daga baya sai riya ta shige shi, to idan ibadar farkonta ba a haɗe ya ke da ƙarshenta ba, to sashen farko na ibadar Sahihiya ce, sashen ƙarshe kuma da riyar ta shige shi ne ya lalace.

3. Idan kuwa farkon ibadar da ma a haɗe ya ke da ƙarshenta, to idan mutumin ya natsu da riyar kuma bai yi tsayin daka wurin kore ta daga zuciyarsa da gwargwadon ikonsa ba, to dukkan aikin ya ɓaci!

4. Idan kuwa zuciyarsa ƙyamar riyar ta ke, ba ta natsu da ita ba, har ma ƙoƙarin kore ta daga zuciyarsa ya ke, to a nan ba za a ce aikinsa ya ɓaci ba in Shã Allãh.

5. Haka kuma idan tunanin riyar ya faɗo masa ne a bayan ya kammala aikin ibadar, a nan ma dai malamai sun tabbatar cewa aikinsa yana nan daram, bai ɓaci ba.

Haka babban malami As-Shaikh Muhammad Bn Saalih Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) ya fayyace waɗannan abubuwa tare da misalai a cikin littafinsa: Al-Ƙaulul Mufeed. Allaah ya saka masa da alkhairi.

Ban da wannan, akwai kuma wani aikin da malaman Tauhidi suka nuna cewa in bai yi daidai da riyar ba, to kuwa ba za ta fi shi muni ba, shi ne:

Mutum ya tashi ya yi aikin ibada da tsarki zuciya saboda Allaah kuma a bisa koyarwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), sai dai kuma a cikin zuciyarsa ya yi wannan ne ba da manufar yin bauta ga Allaah Ta’aala wadda yake fatar samun lada a wurinsa ba, sai dai kawai domin Allaah Mabuwayin Sarki ya ba shi wata buƙatarsa a cikin rayuwar duniya!

Allaah ya kiyaye, ya taimake mu, kuma ya sa mu fi ƙarfin zuciyarmu da shaiɗanunmu.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments