Ticker

6/recent/ticker-posts

Sa’idu Dokin Sukan Sabra

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Sa’idu Dokin Sukan Sabra

Sunan garin su  Sa’idu ‘Yag gona a cikin yankin Maradun ta jihar Zamfara.  Sa’idu shahararre ne wajen aikin gona, kuma Amali yana yi wa duk irinsa waƙa.

 

 G/Waƙa : Tahi noma,

: Sa’idu dokin sukan sabra,

  : Tahi gonakka,

: Raƙumi mai yini duƙe[1].

 

Jagora: Sai wata rana da Antu,

: Sai an jima Kaka,

     ‘Y/Amshi: Sai wata rana,

: Da ni da ku inji mai ƙorai, 

   

Jagora: Sai wata rana,

: Amina tahiya nikai yanzu.

‘Y/Amshi: Sai wata rana,

: Da ni da ku inji mai ƙorai.

 

Jagora: Sai Ku yi man godiya,

: Ga Maidamma mai tcage.

  ‘Y/Amshi: Sannu da hwama,

: Ga Tumba mai zucciyak kyauta,

  : Tahi noma,

: Sa’idu dokin sukan sabra,

  : Tahi gonakka,

: Raƙumi mai yini duƙe.  

 

     Jagora: Yarinya tag gane ni,

: Tac ce ina zaka?

  : In dai ‘yag gona zaka,

: Mamman ina saƙo,

  : In ka ishe malan,

: Sa’idu ka hwaɗi ina so nai,

  : In ya zaɓe ni,

: To biyo in jiya gobe,x2

  : Yarinya gafarak ki,

: Sam ba mu son hauka,

  : Ina kika samun,

: Sa’idu ko kin hi wa nonna[2],

   ‘Y/Amshi: Ina kika samun,

: Sa’idu ko kin hi wa nonna,

: Tahi noma,

: Sa’idu dokin sukan sabra,

  : Tahi gonakka,

: Raƙumi mai yini duƙe.

 

  Jagora: Da munka biyo,

: In dire da waƙan na Maigayya,

  : ‘Yanmata na ishe su,

: Gamji suna wasa,

  : Hau wani laushi sukai,

: Da murya suna taɓi,

  : In dai kin san  Sa’idu,

: Ke san mijin wari,

  : Na so auren  Sa’idu,

: Inda shina sona,x2

  : Wagga abutta da ni,

: Da ke bata yi kenan!

  : Ina kika auren  Sa’idu,

: Na ce ina so nai,

  : Sai ki yi man hanƙuri,

: Ki Komaa ga Maigayya,

‘Y/Amshi: Ki Komaa ga Maigayya,

 

     Jagora: Ke ki yi man hanƙuri,

‘Y/Amshi: Ki Koma ga Maigayya,

 

     Jagora: Haba ki yi man hanƙuri,

‘Y/Amshi: Ki Koma ga Maigayya,

 

     Jagora: In ya ce baya sonki,

: Ada yana sonki,x2

‘Y/Amshi: In kic ce baki yi da,

: Ada kina dandi[3],x2

: Tahi noma,

: Sa’idu dokin sukan sabra,

  : Tahi gonakka,

: Raƙumi mai yini duƙe.

 

     Jagora: Ikon Allah  Sa’idu,

: Kowa yana son ka,

  : Maza na murnar  Sa’idu,

: Mata suna so nai,

  : Manya na son  Sa’idu,

: ‘Yan yara na so nai,

  : Ni ma makaɗin  Sa’idu,

: Kowa yana so na,

  : Kowacce baya son mu,

: Allah yana ƙi nai,

‘Y/Amshi: Maisama sai ya yi mai,

: Azabad da ba ceto.

: Tahi noma,

: Sa’idu dokin sukan sabra,

  : Tahi gonakka,

: Raƙumi mai yini duƙe.

 

Jagora: Sai wata rana  Sa’idu,

: Zaure masha baƙi,

‘Y/Amshi: Sai wata rana da ni,

: Da ku inji mai ƙorai, 

 

Jagora: Sai wata rana da ni,

: Da Kwamma da Maigayya, 

‘Y/Amshi: Sai wata rana da ni,

: Da ku inji mai ƙorai,

: Tahi noma,

: Sa’idu dokin sukan sabra,

  : Tahi gonakka,

: Raƙumi mai yini duƙe.

 

     Jagora: Gwalon kura mutane,

: Akuya ka wa tsoro,

  : Sakko gona mutane,

: Yaro ka tsunke ma,

  : Sanyin raɓa a sashe,

: Sai ko da ban tausai.

 ‘Y/Amshi: Sai wata rana da ni,

: Da ku inji mai ƙorai,

: Tahi noma,

: Sa’idu dokin sukan sabra,

  : Tahi gonakka,

: Raƙumi mai yini duƙe



[1]  Noma

[2]  Nono na ƙirjin yarinya

[3]  Yawon bariki

Post a Comment

0 Comments