Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Maigidan Nasara (Ta biyu)
Noma Autan Yaya shi ne sunan Maigidan Nasara, taubashin
Amali ne (abokin wasansa), mutumen garin
Kuzi ne na mazaɓar Faru da ke cikin ƙaramar hukumar
Maradun a jihar Zamfara. Shi ma manomi ne wanda yake noma amfanin gona, hakan
ya sa Amali ya yi masa waƙa. Na sami
wannan waƙar ne bayan na taɓa samun
wata wadda na kawo a sama, sai na ga akwai wasu ‘yan bambance-bambance, bayan
na yi shawara da malamina sai muka ga cewa a sa su duka su biyun.
G/Waƙa : Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: A
jinjina a aje,
: Ba shi Komi da hwata, x2
: Tunkuɗay yaro,
: Ba ta Komi da dutci,
: Noma jan zaki ,
‘Y/Amshi:
Mai wa yaro kujera[1].
: Ka yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Mijin
Rahammu,
: Na ‘Ya’inna,
: Baban Habibu,
: Ina gida wani bi,
: Hankalina ka tashi,
: Ga ni can wani bi,
: Zuciyata ta yo nan,
: In biyo hanya,
: In taho inda Mamman,
‘Y/Amshi:
Ko da nig ga ka sai,
: Hankalina ya kwanta.
: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Duk inda nig gaka sai,
: Hankalina ya kwanta,
‘Y/Amshi: Sai hankalina ya kwanta,
: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Yanzu kau Mamman,
: Sai ka hausan[2] ga
doki,
: Wanda za ni gwada,
: Wa gida can ga dangi,
: In yi mai turke,
: Masu sona su diba,
: Ga shi dai nau ne,
: Ba biri babu mashi,
‘Y/Amshi: Ko na hwan huɗu ne,
: Noma na so ka ba ni,
: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat tara
damma.
Jagora: Kuma in akwai halin,
: Ba matcewa ga dokin,
: Ko jiranka nikai,
: Hak ka dibo Talata,
‘Y/Amshi: Kasuwam Mahwara,
: Mai dawaki da shawa.
: Ka yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora:
Noma wana ne,
: Don mu ɗauko ta tushe,
: Ɗan’uwana ne,
: Wanda yak kai jimilla,
: Lissafin da nikai,
: Tamu kaka Halima,
: Mai biɗaj jikan,
: Gona Buda ya bini,
‘Y/Amshi:
Jikan gona Buda ya bini.
: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Wanga kau wajjen,
: Noma jikan Salau ne,
: Irin gidan Abdu,
: Jan kada dama gurbi,
: Taƙamar da
nikai,
: Taka ce Ɗan Tahida.
‘Y/Amshi:
Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Duniya da yawa,
: Ba ni roƙun Bahili,
: Ina ganin zaure,
: Ba ni kwana ga hanya,
: Na gano shigihwa[3],
: Ba ni kwana ga bukka,
: Na gano ɗaki,
: Ba ni kwana ga zaure.
‘Y/Amshi: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Yawan hwarauta mai,
: Tsunke gyado ga daji,
: Shi da ba rame,
: Ba wurin molaƙewa,
: Sai ya dunga gudu,
: Har a cimmai a kame,
: Yana iyakay yi,
: Nai a ci mai mutunci.
‘Y/Amshi: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Mai kwaɗan nama,
: Ce ya dawo ga tuji,
: Don ganin suturar,
: Mujiya kay ya ja ka,
: Ina ganin gashin,
: Mujiya manya-manya,
: Ko da nit tona,
: Mujiya ‘yak kaɗan ce.
‘Y/Amshi:
Mujiya ‘yak kaɗan ce,
Jagora: Amali na gane,
: Mujiya yak kaɗan ce,
‘Y/Amshi:
Mujiya yak kaɗan ce,
: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora:
Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
‘Y/Amshi: Ya yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.