Ticker

6/recent/ticker-posts

Buda

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Buda

A Tangyalla Arɗo Buda yake ta ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara. Buda manomin hatsi ne, kuma yana yin noma sosai, kuma yana da rufin asiri, don haka Amali ya yi masa waƙa.

 

G/Waƙa : Na taho in kai mai dandama garka tai,

  : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

 

Jagora  : Bakwai da Jimmai kun yi dacen aure,

‘Y/Amshi: Faɗa ma Buda shi ma ya yi dacen mata, 

  : Na taho in kai mai dandama garka tai,

  : Buda ko san noma baya hi nai sauri.

 

Jagora  : Na ga yunwa ta lunke ga matar raggo,

‘Y/Amshi: Na ji an ce hat ta saci garin kwaki.

 

Jagora  : Na ga yunwa ta tuzga da matar raggo,

‘Y/Amshi: Na ji an ce hat ta saci garin kwaki.,

: Na taho in kai mai dandama[1] garka tai,

  : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

 

Jagora  : Ɗan Kogi na gode,

‘Y/Amshi: Don ko kari[2] yay yo man.

: Na taho in kai mai dandama garka tai,

  : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

 

     Jagora  : Ɗan Kogi lalle mun gode da kyautar

: Girma.

‘Y/Amshi: Da kyautar girma[3].

: Na taho in kai mai dandama garka tai,

  : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

 

 Jagora: Sai godiya Makau don ko kari,

: Yay yo man,

    ‘Y/Amshi: Don ko kari yay yo man..

 

    Jagora: Sai godiya Mudi,

    ‘Y/Amshi: Don ko kari yay yo man ,

 

    Jagora: Ni Shehu na gode,

    ‘Y/Amshi: Don ko kari yay yo man.

 

    Jagora: Ni Jaɓɓi na gode,

    ‘Y/Amshi: Don ko kari yay yo man.

 

    Jagora: Ko Ɗangaladima,

    ‘Y/Amshi: Shi ma kari yay yo man,

: Na taho in kai mai dandama garka tai,

: Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

 

    Jagora: Bakwai da Jimmai kun yi dacen aure,

     ‘Y/Amshi: A ce ma Buda shi ma ya yi dacen mata, 

 

    Jagora: Na ga yunwa ta tuzga[4] da matar raggo,

     ‘Y/Amshi: Na ji an ce hat ta saci garin kwaki.,

 

3.0.15 Hussaini Zarton Noma

Husaini zarton hwashin kuyye mutumen garin Gidan hanya ne, kusa take da Gidan Rijiya a ƙaramar hukumar Shinkafi.

 

 G/Waƙa : Dare da rana yana gona,

  : Hussani zarton hwashin kuyye.

 

   Jagora: Har yau ban zo Gidan Hanya ba ,

    ‘Y/Amshi: Don jikan Kohwa can za ni in kwana, 

 

   Jagora: Har yar yau ban zo gidan Hanya ba, 

    ‘Y/Amshi: Don jikan Kohwa can za ni in kwana, 

 

   Jagora: Dare da rana yana gona,

  : Hussani zarton hwashin kuyye.

    ‘Y/Amshi: Dare da rana yana gona,

  : Hussani zarton hwashin kuyye.

 

   Jagora: Hai yau ban zo Gidan Hanya ba.x2

    ‘Y/Amshi: Don jikan Ƙohwa can  Za ni in kwana.

 

   Jagora: Hai yau ban zo Gidan Hanya ba,

    ‘Y/Amshi: Don jikan Ƙohwa can  za ni in kwana.

: Dare da rana yana gona,

  : Hussaini zarton hwashin kuyye.[1]  Kiɗin noma.

[2]  Bam akaɗI kyauta a lokacin da yake kiɗinsa.

[3]  Babbar kyauta wadda manyan mutane ke yi.

[4]  Kamawa/Rutsawa.

Post a Comment

0 Comments