Ticker

6/recent/ticker-posts

Roƙo

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Roƙo

Roƙo shi ne neman taimako daga wani don samun biyan wata buƙata. Kusan ana samun wannan jigo a cikin kowace waƙa ta bara domin roƙo ne dalilin rera waƙar. Mabaraci na ambaton abin da yake roƙo a cikin waƙar da yake rerawa, wani lokaci ya ambaci abin da yake roƙo wani lokaci ya tsaya ga amfani da kalmar taimako ko sadaka. A cikin waƙoƙin bara na baka ne ake samun roƙo kamar yadda ake samun roƙo a sauran wasu waƙoƙi na baka waɗanda ba na bara ba. Bambancin roƙon da ake samu a cikin waƙoƙin baka na bara da waɗanda ba su ba shi ne, mabarata kusan roƙon da ke cikin waƙoƙinsu bai wuce na abinci ko ɗan abin biyan ƙaramar bukata ba. Sauran waƙoƙin baka kuwa irin na shata manyan abubuwa ake roƙo kamar mota da gida da kujerar haji da manyan kuɗi. Rubutattun waƙoƙin baran ba a samun roƙo cikinsu saboda ba domin bara aka shirya su ba amma dai su mabaratan kan ƙara da kansu don su sami sadakar da suke neman jama’a su ba su. Misali kamar haka:

 Jagora: A ba mu domin Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Wa za ya ba mu na Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Na zo don in samu,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Ku taimake mu ku ba mu,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 (Saboda Manzon Allah)

Ɗiyan waƙar da suka gabata duk roƙo ne da ke cikin waƙar ‘Saboda Manzon Allah’. Babu wani saƙo a ciki sai roƙon. Tun a layi na farko ne aka fara da roƙo sadaka, su kuma Amshin su amsa su amsa dalilin da ya sa za a ba su sadakar ko taimako.

Haka kuma wani misali a waƙar ‘Atumbulo na cewa:

“A tumbulo Inna a tumbulo,

 A tumbulo a kawo ma gajere,

 Gajere ba abin reni ne ba.

(A Tumbulo)

A wannan ‘yar gajerar waƙa da mabarata ke yi suna roƙon masu gida ne don su ba su sadaka ga alama sadakar fura, saboda kalmar na nuna ma’anar abin da ake son a bayar ruwa-ruwa ne kuma da yawa ake son a ɗebo shi, irin fura wadda ita ce abinci mai ruwa da aka san Bahaushe da shi. Haka kuma ya na nuna wa matan da yake yi wa bara cewa shi fa ba banza ba ne abin renawa, don haka a ba shi sadakar da yake nema. Wannan na ƙara fito da falsafar da ke nuna Almajiri mutum ne mai daraja, kuma baran da yake kada ya hana a dube shi da darajar.

Post a Comment

0 Comments