Ticker

6/recent/ticker-posts

Barkwanci

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

 Barkwanci

“Barkwanci zantuttuka ne na raha da wasu mutane waɗanda Allah ya hore wa iya raha da magana da bandariya ke wa jama’a”. Ɗangambo, (1984:50).

A bisa bayanin da ya gabata ana iya cewa barkwanci na nufin kawo wasu zantuttuka saɓanin yadda aka san su a cikin labari ta yadda mai ji ko gani ya yi mamaki har wani lokaci ya ƙyalƙyace da dariya. Mabarata kan yi amfani da irin wannan a cikin waƙarsu idan suna bara. Misali:

 Kura ta ga Ɗan bara ɗan almajiri,

 Bari in bika ɗan bara in shawo gari,

 Tahiyata da taki ba ta zama ɗai da ɗai,

 Ni roƙo nikai ga mata ‘yan arziki,

 Ke ƙwace ki kai ga mata ba su ba ki ba,

 (Daudun bara)

 

A cikin wannan waƙa akwai barkwanci, domin a cikin firar da ta gudana tsakanin daudun bara da kura maganganu ne na barkwance masu nuna ƙyama ga wasu halaye na kura waɗan da suka hana daudu yarda da ya abuce ta.

A wata waƙar ta “Ɗan na birgi-birgi” ana cewa:

 Jagora: Ɗan na burge – burge,

 Amshi: Burge

 Jagora: Ga Inna ta yi baƙi,

 Amshi: Burge,

 Jagora: Baƙin da ba su ƙoshi,

 Amshi: Burge,

 (Burge)

A ɗa na shida da na bakwai akwai barkwanci, wato kalamai masu rikitar da tunanin mai sauraro masu nuna ga wani da abinci kaɗan ba ya isarsa har yana iya cinye ƙaiƙayin dame talatin kafin wataƙila ya ƙoshi. Ko dabba da aka sani da ci ba ta iya cinye abin da shi yake ci kuma babu tabbacin ya ƙoshi don ya ci shi.

Post a Comment

0 Comments