Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Fatan Alheri
Fatan
alheri shi ne yi wa mutum kalamai masu ƙunshe
da addu’ar samun biyan bukatocinsa da yake fatar samu tare da haɗawa da wasu muradan rayuwa da
mutum ke son ya gani da saduwa da abubuwa masu kyawo da kowa ke son samu. Akwai
irin wannan jigo a cikin waƙoƙin da mabarata ke rerawa a lokacin da suke yin bara. Suna
yin haka ne domin daɗaɗa zuciyar waɗanda suke yi wa bara haka ya sa su ji daɗin ba su sadaka. Rubutattun waƙoƙin da ba don
baran aka shirya su ba, sai dai don wata manufa ta daban ba a samun irin wannan
a cikinsu. Duk da haka, mabarata kan ƙara
fatan alherin a cikinsu idan suna bara da su. Misali:
Iya
kalin-kalin-kalin,
Iya kalin na
malamai,
Iya komi kike biɗa,
Iya Allah na ba ki
shi,
Ki sami farin ɗa,
Abu mahaddaci,
Ya haddaci sittin,
Ya san sunnoni,
Ya sami hankuri,
Hankuri na duniya,
Wanda kowa yake biɗa.
(Iya Kalin-kalin)
Wannan wata waƙar bara ce da
almajirai ke amfani da ita wajen bara. A cikin waƙar mabaracin na nuna fatar alheari ga matar da yake yi wa bara. Babban
fatar alheri ga matar aure bai wuce ta sami haihuwa ba, kuma ƙari ga haka abin da za ta haifa ya zama ɗa namiji. Kowa ya san yadda mutane
ke kallon ɗa
namiji da daraja ba sai al’ummar Hausawa ba, domin an ɗauka shi ne magajin gida saɓanin mace da za ta yi aure ta koma wani gida. Haka kuma, ɗan da yake fatar matar ta haifa ya
kasance mai kyawon hali kuma masanin Ƙur’ani
ne, ilmin da kowane Musulmi ke kwaɗayin samu. Duk wannan zai samu ne bayan ta sami duk wani abu da take nema
daga wurin Allah. Haka kuma cewa ‘Allah zai ba ki shi’ kamar wani tabbaci ne.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.